lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MALAMAI KAN TAFARKIN HUSAINI

 

An haifi Ayatullahi Shaik Muhammad Husaini Sibawaihi Ha’iri a shekarar 1306 hijiriya a birnin Karbala mai tsarki, mahaifinsa Ayatullahi Shaik Muhammad Ali Sibawaihi ya kasance daga fitattun malamai Mraji’an addini a Karbala, Ayatullahi Muhammad Sibawaihi yayi dalibta a Karbala a hannun manyan malamai  masu daraja da falala misalin Samahatu Ayatullahi Shaik Jafar Rashti da Ayatullahi Muhammad Rida Isfahani da Ayatullahi Aga Shaik Ali Sawuji da Ayatullahi Dabasi Ha’iri da Ayatullahi Shaik Yusuf Kurasani da Ayatullahi Shaik Muhammad Ali Sibawaihi.

A birnin Najaf Ashraf kuwa yayi dalibta da gun Ayatullahi Shaik Mujtaba Lankarani da Ayatullahi Assayid Ashkuwari da Ayatullahi Shaik Sdaraya Badukabe da Ayatullahi Haj Assayid Muhammad Bakir Mahallati, bugu da kari yayi dalibta a matakin bahasul Karij hannun Maraji’ai masu daraja misalin Ayatullahi Assayid Abu Kasim Kuyi da Imam Komaini da Assayid Hassan Bujunawardi da Mirza Bakir Zanjani da Haj Mirza Hassan Yazdi.

Tura tambaya