lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

DAN KASUWA DA MAI KETARA

 

Malikul Ashtar ya kasance dogon mutum mai tsayi yana sanya da doguwar riga da rawani, idan ka ganshi zaka alamomin gwagwarmaya da yaki duk sun bayyana a fuskarsa, sadaukantaka da jarumtaka duk san bayyana a fuskarasa.

Wata rana yana tafiya a cikin kasuwar garin Kufa sai wani ga wani mutum yana kuskus cikin zuciyarsa yana yi masa kallon raini da wulakanci da izgili sakakamon shigar da ya ganshi ciki, sai ya jefe shi da kwayar gyada, shi ko Malikul Ashtar ko bai ko waiwaye shi sai ya cika gaba da ketara kasuwa hai sai da aka daina hango shi, lokacin da wani ya tambayi wannan da kasuwa da yayi jifa yace masa tir da kai shin kasan wanda jefa kuwa?

 sai yace: a a ban san shi ba, kadai na yi hukunci kansa da cewa masu ketarawa ne ta cikin kasuwan misalin sauran dubunan masu ketarawa.

Sai yace masa: wannan da ka jefa shine Malikul Ashtar Naka’i  Sahabin Sarkin Muminai Ali (as) kuma kwamandan rundunarsa, sai yace kai kai yanzu wannan shine Malik din da kafadun Zaki ke karkadawa idan suka hadu saboda tsoransa, haka makiyin yana girgiza daga jin sunansa?!

Sai yace masa: eh shine, da jin haka sai yayi wuf ya tashi a guje yana bin sawu don nemansa domin ya bashi hakuri bisa abinda yayi gaggawar aikatawa kansa, sai dai kuma cewa tuni Malik ya riga ya shiga daya daga cikin masallatai, yayin da wannan mutumi ya iso sai ya samu Malik a tsaye yana sallah, yayin da ya idar da sallar sai wannan mutumi ya fadin kan kafafun Malik yana sumbatar kafafun, sai Malik yace: meye haka?!  Yace ina neman afuwarka bisa abinda na aikata , ni ne wanda na yi maka izgilanci nayi maka tsageranci, sai yace masa babu matsala, wallahi ban shiga wannan masallacin ba face don ina maka gafara.

Tura tambaya