lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Ummul Masa’ib Haura’u Zainab diyar sarkin muminai Ali bn Abu dalib (as)

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Sirri da sirrikan Haura’u Zainab amincin Allah ya kara tabbata a gareta- tareda Alkalamin Sayyid Adil-Alawi

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kayata mutum da ilimi ya sanar da shi matattaran kalamai, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittun Allah adon dukkanin kasantattu Alfahari duniya Muhammad da iyalansa tsarkaka haske mafi alheri adon rabautattu.

Allah ta’ala yana cikin mabayyaninj littafinsa yace:           

 (وَمِنْ كُلِّ شَيْءٍ خَلَقْنا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرونَ)

Kuma daga kowanne abu mun halicci nau’i biyu saranku ku tuna.

Albayyinatu cikin isdilahin fakihai tana nufin shaidu guda biyu adalai kan wani abu da ya afku cikin mukamin bada shaida, wannan ana kiransa da sunan (bayyinatu shar’iyya wa tashri’iyya) cikin kasantattu akwai bayyina takwiniya, cikin komai Allah ya halicci jinsu biyu domin su shaida kan dayantakarsa matsarkaki, cikin kowanne abu yana da aya da shaida kan cewa shi daya ne rak  tal abin nufi da bukata wanda bai Haifa ba kuma ba haifeshi ba kuma wani bai kasance tsaransa ba, kissar Ashura da garin Daffi kiss ace mai bakanta rai da kuna a zuciya, wannan kisa ta kasance daga jinsu biyu tsarkaka tsatson Aliyu  da Fatima (as) sune shugabanmu shugaban shahidai Imam Husain ibn Ali b Abu dalib (as) da Sayyada Zainab (as), ita Ashura gundarin muslunci ce, da aka haifeta a Karbala, babanta kuma shine shugaban shahidai (as) mai rainonta kuma itace Mujahida `yar juyin juya hali Zainab (as) bada ban ita da Ashura ta kasance marainiya da zata mutu tun cikin yarintarta, sai dai cewa kuma Sayyada Zainab tareda fafutikarta da gwagwarmayarta ta raini Ashura wannan yar jaririya da jinin daukar fansar Allah yake gudana cikin jijiyon jikinta, sai Ashurar Husaini ta girma karkashin rainon Zainab cikin hallarar dakinta mai albarka da jihadinta mara yankewa, ba don komai ba sia don ta kasance uwar dukkanin wani ynukurin `yanci tsakankanin al’umma tsawon zamanunnuka da dukkanin kasashe har zuwa tashin kiyama, itace tushen duk wani gwagwarmayar neman `yanci da yankurin muslunci har zuwa ranar alkawari.

Babu wani mutum da ya isa ya san mukamin uwar Ashura da matsayinta a duniya da lahira in banda Allah matsarkaki da Annbawa da wasiyyai amincin Allah ya kara tabbata a gares. Lallai ma’arifa da ilimi da sanin wani abu lazimnisa shine kewayuwa da shi, bai yiwuwa ga mutane su kewayu da Ashura da gundarinta da falsafarta, ba zaku ma taba kewaya da mahaifiyarta ba da mahaifinta, ita Zainab Kubra cikin daurorin rayuwarta da tarihinta tana baka labarin asalantar samaniya  da bishiyar annabta da hashimiyya da tarjamar kur’ani, asalinta tabbatacce ne cikin samaniya, cikin adon mahaifinta sarkin muminai zakin Allah mai galaba Ali bn Abu dalib (as) lallai shi bai yi alfahari da littafinsa mai girma ba (Nahjul balaga) wanda shi littafi ne na rayuwa da farin ciki bai yiwuwa ga mutum ya san abinda yake tattare cikinsa daga girmama da daukak, sai dai cewa shi yana alfahari da kuma yin ado da diyarsa Zainab, bada ban ina tsoro kan kwakwalen mutane ba da cikin baitin begenta da yabonta da saninta mun fadi abinda zai gigita kwakwale da rikita ma’abota zurfin tunan, kadan daga bayina masu godiya da zurfin tunani, mutane kadan ne masu godiya cikin bayina da zurfin tunani da hakuri, Zainab bata gushe ba Zainabun annabta da da imamanci da wilaya mafi girma fursunan son rai, a jiya ta kasance fursunan azzalumai daga Banu Umayya dagutaida mabiyans, yau kuma gata fursunan raunanan kwakwale, har taki ga sun ace mata mace ce gamagari kamr kowacce mace?!!

Kadai dai ita ma’arifa tana cika da Imani da Allah da kaunar girmamarsa da kyawunsa mai tajalli cikin kasantattu da bauta da sallamawa da mika wuya ga lamarinsa, abinda yau muka sani dangane da Zainabun muslunci ba komai bane face inuwa daga tsarkakarta da girmamarta, bayyane yake a fili sarari cewa inuwa bata iya bada cikakkiyar ma’arifa abu da hakikarsa, amma Zainabun muslunci ikonta na nufin hukumar kyawawan dabi’u da sadaukarwa da fans, tarbiyarta na nufin soyayya da kaunar Allah da narkewa  cikin zatinsa girmansa ya girmama, sakafarta na nufin kubutuwar halitta da ikonta cikin dukkanin fagagen rayuwa tun daga matakun daidaiku da jama'a, soyayya da kaunar ubangiji da suka bayyana cikin Ashura kadai jijiyoyinta Zainab reshenta a samaniya tana bada kayan marmarinta cikin kowanne lokaci da izinin ubangijinta `yayanta isma ganyenta iklasi tushen jijiyoyinta tsaki, hasken girmama, ita kauna kadai dai tana bubbuga daga zuciya, sannan ita zuciya haramin Allah ce. Sannan fitira tana kira da cewa lallai ya kamata cewa ma'abocin zuciya da soyayya ya san cewa ita zuciya kadarar Allah c, sai dai cewa Iblis yana sadadawa yayi sata cikin haramin Allah ma'ana zuciyar mumini ya zauna cikinta yayi kwai da kyankyasa ya mai sheta shekarsa shi da `yayansa da rundunarsa, sai ka samu zuciyata na kazantuwa da aikata sabo ta fita daga kasantuwarta haramin Allah masaukar rahama da iliminsa matsarkaki, anan zaka ga cewa zuciya ta mutu ta kasance kamar dutse ko kuma mafi bushewa daga dutse cikin kekashewa, zaka samesu kamar dabbobi bari dai sun fo dabbobi batan hanya.

Karbalar Husaini tareda Zainab (as) kadai dai ta kasance mahallin shahadar masoya kamar yanda sarkin muminai Ali (as) ya fadi lokacin da gifta ta

: «ها هنا مصارع العشّاق»

Nan ne makabartar masoya.

wannan wani dan karamin rubutun masoya zautattu ne cikin soyayyar Allah da kyawunsa, Zainab jarumar Karbala malamar soyayya cikin zatin Allah ta daga gawar dan'uwanta sama jike da jini kansa a yanke cikin nutsuwa tana fadin:

 «اللهمّ تقبّل هذا القربان من آل محمّد».

Ya Allah ka karbi wannan ibadar neman kusancinka daga iyalan Muhammad.

Daga cikin lakubbanta: SIddika, Ismatul Sugra, waliyatullahi….

Tura tambaya