lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Sirri daga sirrikan imam sadik (as)


(Sirri daga sirrikan imam sadik (as)

سرٌ من أسرار الإمام الصادق(ع) - بقلم السید عادل العلوي

Siiri daga cikin sirrikan imam sadik (as) tareda alkalamin sayyid adil alawi

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Babu shakka babu kokwanto kan cewa maganar kan ilimi da darajoji da faloli ahlul-baiti (as) daga cikisu majabancinmu imam sadik (as) da bayanin manya-manyansu cikinsu da masanansu, da abin da suka aikata daga daurori ma’abota haske da matakai da suka dauka na Allah cikin fagagen muslunci da dukkanin matsugunansu, lallai hakika mukami ne mai girma da babu mutum da zai iya kaiwa gareshi tareda duk matsayin da ya kai gareshi cikin ilimi da ma’arifa, babu wani marubuci da zai iya sauka kansa, ko wani masanin tarihi ko adabi tareda baiwa da yake da ita daga kwarewa cikin tsara karfaffen usulubi da bayani kayatacce da dadadan jumloli.

Lallai bijira ga tarjamar daya daga cikin haskakkun sunaye daga wannan gida tsarkakakke kamar misalin tarjamar shugabanmu imami mai furuci  jafar assadik (as) da bayaninsa da kuma abin da ya shagaltar da shi daga matsugunan tarihi, kadai wata maj’mu’a da mausu’a mai girma ka iya tattaro shi da wata jumla ma’anoni madaukakiya mai hadafi cikin wannan tafarki, bai tsira daga kasanrtuwarta bincike da darasi cikin rayuwar ahlul-baiti da bahasi kan darajojinsu da falolinsu masu girma, bari dai zai kasance wani bahasi na akida da tarihi da akhlak a jumlace da dalla-dalla filla-filla.

Ahlul-baiti da sadik musaddak sun wanzu tsawon tarihin al’ummu tsarkakku cikin zukatan al’ummu, suna masu daukaka kan dukkanin tatsuniyoyi da shubuhohi da kage da karairayi, gidajen imamai sun wayi gari makarantu ayoyi magirmama musammam ma imam sadik (as) ma’abota daurori masu babbar jami’a da masu bukata da daliban ilimi da ma’arifa ke nufarta, cike take da kumfar motsi da nishadi na ilimi da sakafa bisa mabanbantar dabakoki domin yada addini na asali, da tarbiyar al’umma karfaffa da zata fuskanci wahalhalu da ke bijirarwa mutane cikin kan hanyarsu mai tsayi.

    Ustazu muhammadu sadik nasha’at almisri wanda malami ne a kulliyatu adab a jami’ar alkahira lokacin da yake siffanta gidan imam sadik (as) yana cewa: ya kasance jami’a mai girma da ta cika da masana hikima da malamai, ya kasance yana amsa tambayoyinsu yana warware matsalolinsu  ba tareda waiwayar addinansu da mazhabobinsu  kungiyoyinsu da manufofinsu ba, hakika an tattara darasussukan sahabbansa na kusa-kusa cikin littafai dari hudu, wanda ana kiran wadannan littafai arba’a mi’atu usul (asalai dari hudu)

Idan ya zamanto imam jafar ibn muhammadu assadik (as) shi imami ne to me yasa ba za su yi koyi da shi ba ba za su bishi ba, me ya same sune yaya suke hukunci, shin akwai wani abu bayan shiriya in banda bata ?!!     

 

                      فلا تعدل بأهل البيت خلقاً                   فأهل البيت هم أهل السيادة

                      فبغضهم من الإنسان خسر                    حقـيقـي وحـبّـهـم عـبـادة

Ka da kai gangancin daidaita kowa da ahlul-baiti daga baki dayan halittu

Lallai su ahlul baiti sune ahalin shugabanci

Kiyayyarsu daga kowanne mutum hsara ce ta hakika sannan soyayyarsu ibada ce.

Hakika zurfafa tunani da kiyaye maudu’anci cikin suluki, da asali cikin sakafa da daidaita cikin bayyanarwa da ginawa dukkkaninsu sun sanya  ahlul-baiti suna mallakar yankakken dalili biye zuwa ga dalili mai huda kan imamanci na gaskiya da marja’iyya ta ilimi ta addini ga mutumtaka rudadda batatta, sannan kwarewa cikin gudanarwa da tarbiyya wanda karkashinta suka samu damar sauka kan matsugunin shar’antawar muslunci  da kimomi na akhlak zuwa ga dabbakawa, da tattaro dukkanin matsaloli da suke bijira da warkar da su warkarwar muslunci datacce duk da sabanin yanayi da zamani da bigire da wurare daban daban, wani marubuci `dan yammacin turai mai suna duwaiti cikin littafinsa mai suna (akidatush shi’a) yana cewa : hakika wasu adadi daga almajiran imam sadik(as) sun bada gudummawa gudummawa mai girma cikin cigaban ilimin fikihu da ilimin kalam wanda biyu daga cikinsu wato abu hanifa da maliku ibn anas  daga baya suka zamanto ma’abota mazhabobin fikihu, wasilu in a`da shugaban mu’utazilawa da jabir ibn hayyanu sanannen masanin ilimin kimiyya dukkansu daga almajiran imam sadik (as) suke.

Ibn hajar yana cewa : jafar ibn muhammadu assadik (as) mutane sun nakalci ilimai daga gareshi abin da ayarin mahaya sukai tafi da shi, sunansa ya yadu ya daukaka cikin dukkanin garuruwa, manya-manyan a’imma sun rawaita daga gareshi kamar misalin yahaya in sa’id da abi jarihu da malik da sufyanu sauri da sufyanu da shu ;ubatu da ayyubar sujustani. Da wadanda suka gabace shi malam jahiz da ya shahara da tsananin ta’assubanci kan  son usmanu da son zuciya kansa ya rubuta wannan jumloli cikin wannan siyaki da tsari : jafar ibn muhammadu wanda iliminsa da fahimtarsa suka cika duniya, ance abu hanifa da yana daga almajiransa haka ma sufyanu sauri, ya isheka da su biyun a wannan babi, tabbas shi imami ne sadauki , imamin musulmai jafar ibn muhammadu assadik amintacce (as)

Abin da mukai imani da shi muka kudurce cikin imamin mu shi ne lalli shi sirri ne daga sirrikan Allah masu girma lallai shi kammalallen mutum ne kuma hujjar Allah ne kan halittunsa baki daya da albarkacinsa al’uuma ta azurtu da samuwarsa kasa da sama suka tabbatu, lallai Allah yana tajalli cikinsa da sunansa mafi girma (allahu) da kalmarsa cikakka da ayarsa mai girma, amincin Allah ya tabbata gareshi da iyayensa tsarkaka da `ya`yansa  ma’asumai  har abadan abidin har zuwa tashin kiyama

karshen maganarmu da kiranmu muna godiya ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su tabbata ga muhammadu da iyalansa      

 

Tura tambaya