Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Ma'aikaci tsoho
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ma'aikaci tsoho

 

Yammaci yayi, tareda Imam Rida (a.s) mun tafi gidansa, wsu adadin mutane sun shagaltu da yin aikin gini, bangwaye sun lalace, sannan ga wasu mutane uku a cikin filin gida suna kwaava qasa mutum guda yana xora tubali kan tubali, wasu adadi kuma suna fito da qasa , Imam (a.s) ya wuce ya gaishe da kowannensu kai kace yasan dukkanin ma'aikatan, kwatsan sai idonsa ya faxa kan wani ma'aiakaci tsoho ramamme, yace ban tava ganin wannan ba sai ya xan tsaya ya kalle shi sosai, sai ya tambayai hadiminsa mai kula ayyuka yace: wannan ma'aikacin wane ne shi?

Wannan hadimi nasa ya bada amsa da cewa: ma'aikaci ne da ya zo ba da taimako, sai Imam yace: shin kan ayyana ladan aikinsa? Sai ya bada amsa : A a bab yawa duk abinda muka bashi zai karva.

Jin wannan magana ta matuqar vatawa Imam rai lamarin da ya kai ga Imam ya kausasa lafazi kan wannan hadimi nasa.

Sai na xan matsa gaba domin in xan tausasa shi, sai na ce: gafarta malam raina fansarka! Kada ka vata ranka da yawa.

Imam Rida (a.s) ya waiwaye shi ya ce: ya kai Sulaiman lokaci da daman gaske na gaya maka cewa duk sanda zaka kawo wani aiki to kafin ka kawo shi ka ayyana ladansa sannan ka bshi adadi wannan kuxin, zasu yi farin ciki, idan kuwa aka xan qara wasu `yan kuxaxe kan ladan , to wannan lokaci zai samu gamsuwa ya tafi yana mai godiya.

A wannan rana na ga Imam Rida (a.s) ya kira wannan ma'aikaci tsoho, bayan ya tattauana da shi  sai ya bashi ladan aiki mai yawa, wannan ma'aikaci yayi matuqar farinciki ya kuma yi masa addu'a    

 

Tura tambaya