lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wasu takaitattun bincike da zasu amfanar da mumini da mumina.

 

So shi ne karkatuwar zuciya, saboda haka masaukin son duniya shi ne kwaryar zuciyarka, me zamu aikata mu kubuta mu fitar da son duniya daga zukatanmu?

Hanyoyin duk da kasantuwarsu suna da yawan gaske sai dai cewa mafi muhimmancinsu sune:

1-ka tuna cewa ita mai gushewa ce ba ta da tabbas din dawwamuwa da wanzuwa ga kowa.

2-kayi tunani kan wulakantarta da kuma cewa dadainta kankani ne.

3-ka kalleta da idon basira da fadaka ga wanda ya gabaceka cikin duniya da abin da ya faru da shi daga faduwarta da hawanta.

4- ita fa duniya yaudara take bata taba cika alkawari ga wani mutum ba, babu mai aminta da ita sai anda ya jahilceta ya jahilci ha’incinta da makircinta da yaudararta.

5- babu hutu cikin duniya, baki dayan mutane cikin wahala da gajiya suke matukar dai sun ratayu da soyayyarta sun kuma kaunace ta, basu guje ta ba.

6-ka dubi gogayyar da wasu sukai, da abin da ya gudana kansu daga jarrabawowinta da fitintinun cikinta da bala’in da yake cikinta.

7- ka karanta ayoyi da riwayoyi da kalmomin ma’abota hikima da malamai kan zarginta da wulakantarta da kasantuwar dadinta kankani ne.

8- yau ina sarakuna da yayan sarauta, yau ina fadoji yau ina dukiya da jin dadin ma’abotanta, dukkaninsu sun zama labara, me yasa zan so duniya alhalin ga yadda karshen lamarin yake kasancewa?

9-annabawa da wasiyyai da salihan bayi da arifai sunyi zuhudu cikinta, ta kaka zan so ta, lallai da ta kasance ta cancanci soyayya da waliyyai da annbawa da manzanni tun daga adamu har zuwa cikamakinsu tsira da amincin Allah ya kara tabbata gare su sun nuna mata soyayya, bari dai sai ma zarginta da suka sukai suka kuma kyamace ta lokacin da ta kasantu mai cutar da lahirarsu.

10- mafificin abu cikin kubuta daga son duniya shi ne ka cika zuciyarka da soyayyar wanda shi ne mafi girma da cika daga dukkanin so da karkatar zuciya, ku saurara wannan ba kowa bane face Allah matsarkaki da kuma soyayyar manzonsa da soyayyar tsatsonsa ahlin gidansa tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata gare su, lallai zuciya biyu basu haduwa cikin mutum guda, zuciyar da take son Allah da zuciyar da take son duniya.

3-lallai munanan halaye kamar misalign kangarwar tayar mota ce da take da huda, matukar dai matuki direba bai sauya ta da lafiyayyar kangarwar taya ba ko kuma ya gyara ta ba, lallai motar lalace take ba zata iya motsawa ba ta tafi, idan ma ta motsa lallai ba zata kai ka inda kake son takai ka ba, dole a canja ko kuma a gyara munanan halaye da kyawawa

4-daya daga cikin arifai yana cewa daya daga cikin almajiransa: ku yaudari duniya.. sai sukace: ta kaka hakan zai yiwu? Sai ya ce: ku ci gurasarta ku ji dadi da dadinta kuyi aiki don lahirarku.

ـ قال أمير المؤمنين علي عليه السلام: أسعد الناس من ترك لذّة فانية، للذّة باقية.

5- sarkin muminai Ali (as) yana cewa: mafi farin cikin mutane shi ne wanda yay i watsi da dadi mai bushewa don dadi mai wanzuwa.

ـ عن الحسين بن مصعب قال: سمعت أبا عبد الله الإمام الصادق عليه السلام يقول: ثلاثة لا  عذر لأحد فيها ـ أي من الواجب الذي لا يُعذر في تركه بمعاذير وأعذار:

Daga Husaini ibn mus’abu ya ce: naji Abu Abdullah imam Sadik (as) yana cewa: abubuwa uku mutum bai da uzuri cikinsu –ai daga wajiban da ba a yin uzuri cikin barinsu da kawa uzurai da bada uzuri sune:

1 ـ أداء الأمانة إلى البّر والفاجر.

Wajabcin sauke amana zuwa mutum kirki da fajiri.

2 ـ والوفاء بالعهد إلى البّر والفاجر.

Cika alkawari zuwa ga mutum kirki da fajiri.

3 ـ وبرّ الوالدين برّين كانا أو فاجرين.

Biyayyar iyaye babu banbanci cikin kasantuwarsu daga mutanen kirki ko fajirai.

فطوبى لمن كان باراً بوالديه في حياتهما وبعد مماتهما.

Farin ciki ga mai biyayya ga iyaye lokacin da suke raye da bayan mutuwarsu.

7-lallai ladabi shi ne kyawuntar zahirin ayyuka da furuci lallai kuma yana daga mabubbugar kyawawan halaye wadanda sune: kyawuntar badini da malaka mai falala da siffofi ababen yabawa da darajoji da karramammun halaye, da kauracewa munana halaye da miyagun ayyuka,

Ladabi bai kasantu ba daga tsarkakewa da shaidar makarantun zamani ko shaidar hauzozin ilimi, bari dais hi ladabi na nufin aminci da amintuwa da sadaukarwa cika alkawari da nuna soyayya da kauna da jin kai ga matarka, da kyauta da nuna soyayya ga yayanka, da tsarkakakkiyar kyauta da hidima ga iyayenka  ta hanyar kaskantar da kanka gabansu da tawali’u, da kuma yin tsarkakakkiyar bauta da biyayya ta gaskiya ga ubangijinka, ka kuma kasance mai bawa addini kariya da kasarka da mutuncin mutane da jininka. Ka kuma zamanto cikin hidimtawa mutane da amfanar da mutanenka da ni’imtar da jama’ar imani da mutumtaka da kyawawan halayenka masu daraja da falalarka da kyautarka da sadaukarwarka.

8- hakika Allah ya umarci Ibrahim badadinsa cikin mukamin ibtila’i da jarrabawa tare da girmansa da tsufansa  da cewa ya yanka dansa sai Ibrahim ya mike da niyyar zartarwa da biyayya ga umarnin ubangijinsa, ya kayar da shi a gefan goshinsa ya goga wukar kan jijiyoyin wuyan dansa sai dai cewa ita wuka batai aikinta ba wannan wuka tayi magana da harshe mai fasaha tana mai cewa: masoyin Allah yana umarta ta mai girma kuma na hana ni, sai Allah ya yiwa Ibrahim magana ya ce masa lallai ka gasgata mafarkinka ya Ibrahim.

Sai ya tambayi ubangijinsa ta kaka bazan yanka dana ba don in samu mafi girman ladan ibtila’inka?!

Sai Allah ya nuna masa kasar karbala mai tsarki, sai waki’ar karbala tayi tajalli cikin zuciyarsa, da yadda za a yanka dansa imam Husani amincin Allah ya kara tabbata gare shi kan saharar karbala an yayyanke masa jijiyoyi an tattake masa kirji kansa kuma na tsire a saman mashi, sai Ibrahim ya fashe da kuka da fiye da radadin da ya sha kan yanka dansa isma’il amincin Allah ya kara tabbata gare shi.

Ya zo cikin wani hadisi: da Ibrahim ya yanka dansa isma’il da ba zai ji radadin da yaji kan kisan dansa Husaini, sai Allah matsarkaki ya nufe shi da wannan bala’i mai girma da wannan musiba mai girma wacce ta sanya sammai da kassai kuka kai hatta matan aljanna sai da sukai kuka, don ya samu matsayi mai girma da rahama mai girma. Wacce ita ce mukamin imamanci da kuma kasantuwa shi wanda biyayyarsa take wajibi  

 (إني جاعلك للناس إماماً)

Lallai ni mai sanya ka imami ne ga mutane.

Hakan ya kasance ta hanyar musibar imam Husaini da yin kuka kansa. Ta yiwu ba zai cimma wannan mukami da matsayi na imamanci ba ta hanyar yanka dansa Isma’il amincin Allah ya kara tabbata gare shi. Farin ciki ga masu kuka da masu ta’aziyya kan shugaban shahidai, musammam ma cikin watannin muharram da safar, cikin faron muharram cikin kowacce shekara, mai ta’aziyya da nuna soyayya da kauna da raya sha’a’irul husainiyya bai san irin lada mai girma da yake da shi a cikin aljanna cikin korama cikin matsunin gaskiya wajen sarki mai kudura daga abin da idaniya bata taba gani ba kunne bait aba ji ba zuciya bata taba darsawa ba, wancan babu kokwanto cikinsa shiriya ne ga masu tsoran Allah wadanda suke imani da gaibu da kuma abin da Allah ya rubuta kan al’arshinsa da launin ma’arifa:

 (إنّ الحسين مصباح هدىً وسفينة نجاة)...

Lallai Husaini fitilar shiriya ne kuma jirgin tsira ne.

Tura tambaya