lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kibiya ta biyar

Wahabiyya babbar fitina:

Girman kai tare da karfinsa da Sojojinsa gabas da yamma baya bakin komai face wata fuska da fuskokion Shaidan jefaffe, hakika ma'abota girman kai sune masoyan Shaidanu, kuma lallai Shaidaniu suna wahayi zuwa Masoyansu, daga cikin wahayinsu akwai shrye-shirye da makircin girman kai na shaidanci, shi ne rarrabawa kawukan mutan, da tsagasu da datse dantsensu da jefa gaba da kiyayya da rarrabuwa tsakankaninsu.

 (إنَّما الشَّيْطانُ يُلْقي بَيْنَكُمُ العَداوَةَ وَالبَغْضاءَ)[2] .

 Kadai Shaidan yana jefa gaba da kiyayya tsakankaninku.

Sai siyasar mugunta da kiyayya ta bayyana garesu suka bi uslubin Shaidanci (raba kawuknsu sai ka shugabance su) domin tabbatar da shugabancinsu da hukumarsu da ikonsu kan mutane sai suka rarraba kawukan mutane sunyi amfani da duk hanya da suka samu dama wajen rarraba kawuka, wani lokaci suna amfani da sunan mutanenmu cikin rabai kai a wani karon kuma da sunan kungiya, wani lokacin da sunan mazhaba ko al'adu, haka da duk abin da zamani da wurin da suka ya hukunta amfani da shi daga dabara da makirci.

Makircin girman kai shi ne dasa irin munafunci da sabani tsakanin mutane, domin samun damar hakar arzikinsu da shan jinanensu, sannan domin warware matsalolinsu ya zama tilas su koma zuwa ga Girman kai `yan mulkin mallaka su shugabance su su kara samun iko da mallaka kansu, sun wanke kawukansu daga laifu da wannan dabara, ina sai abind aba haka yake sun karawa tabo ruwa, abin ban mamaki daga Jamhur din mutane shi ne har yanzu baus gushe cikin bacci gafala duk da cewa wasu `ayn kadan daga wayayyun cikinsu sun dan fara farkawa kadan sai dai cewa wannan farkawa da suka yi bai kai mataki da mustawar da ake bukata ba sai gashi cikin gaggawa wannan wuta da take kone takardun makircin Yan mulkin mallaka girman kai ta mutu ba ta ci gaba da babbake su ba tare da kaskantarsu.

Daga cikin makircinsu wanda suke ta kada ganga kansa lokaci bayan lokaci shi ne rarrabawa kawukan musulmi `yan sunna da `yan shi'a, wannan ganga ba ta bakin komai face kirkirarriyar karajin girman kai.

Daga cikin sababbin shirye-shiryensu da makircin Girman kan Birtaniya shi ne kirkirar sababbin Kungiyoyo da mazhabobi domin rarraba tsakanin `yan sunna su saka kirkiri sabuwar amzhaba da sunan `yantuwa da da'awar kawo gyara cikin mafi muhimmancin garuruwan musulmai wato Hijaz da Makka masaukar wahayi da sakon muslunci Muhammadiya, domin musulmai su fitinu su kuma rusa akidunsu sai suka kirkiri (Mazhabar Wahabiyya) kamar yanda suka kirkirawar musulmi `yan shi'a sabuwar mazhaba da take da alaka a nau'ance da akidunsu na gaskiya, sabida girman kai ya san daga ina ake cinye karfata, yana aiki da duk wata kungiya kan akidunsu da sunan addini ne zai rusa musu rukunan addini da matattakalarsa, sai ya kirkirawar shi'a Mazhabar Babiya dana kuma ta jirkice ta zama Baha'iyya, abin ban mamaki daga wadannan kirkirarrun Mazhabobi guda biyu ina nufin Wahabiyya da Baha'iyya shi ne girman kai ya samar da su a zamani guda cikin garuruwan musulmai shi'a da sunna daya cikin Hijaz daya kuma cikin Iran domin samun iko kan kasashen musulmi da bayin Allah da kuma ruguje addinin muslunci.

Sannan wadannan kagaggun mazhabobi biyu (Wahabiyya da Baha'iyya) babban hadafi cikin samar da su shi ne rarraba kan al'ummar musulmai da raunana su da rusa su, daga baya sai ya dawo ya samu damar farlanta cikakken ikonsa kansu, lallai siyasar shaidanci (raba kai ka shugabance su) abin ban takaici ta samu nasara cikin wannan shiryayyen makirci, har yanzu wasu ba'arin musulmi basu gushe ba cikin nauyayyan bacci, sai dai cewa juyin juya halin muslunci a cikin Iran ya katse hannayen girman kai ya girgizar karagun mulkin Dawagitai, ya hallaka mulkin Sarki Shahinsha halakakke la'ananne wand aya kasance yana taimakawa Baha'iyanci, Firaminstan hukumarsa wanda ya kasance kan wannan mukami shekaru goma sha uku wato Abbas Huwaida `dan Baha'iyya wanda aka zartarwa da hukuncin kisa bayan nasarar juyin juya halin muslunci, sai ya zamana babu abin da ya rage daga kufaifayin Baha'iyanci sai sauran sunanta da bakin tarihinta kamar dai yanda gwamnatin Gurzuzanci ta rushe ta zama tarihi a tarayyar Sobiyat.

Hakama muna nan muna jiran rushewar Wahabiyanci da bushewarsu daga kasashen musulmai domin cukwin `yan sunna ya tsarkaka al'ummar musulmai su tsarkaka daga kazantar Wahabiyanci, lallai hakan ba wani abune da ya gagari Allah ba, shin Asubahi bata kusa, lallai ita karya tana da lokaci kayyadadde ita ko gaskiya Daula ce madawwamiya, dole a karya dabaibayi dare yaye haske ya bayyana, da samun tabbatar nasara daga Allah.

Na'am: kungiyar Wahabiyyanci a Tarkibance a addinance da duniyance ta samu daga kazantaccen hadin kai daga Kabilu biyu, sune: Kabilar Alu Sa'ud da Kabilar Alu Shaik dangin Muhammad bn Abdul-Wahab ma'abocin wannan kirkirarriyar mazhaba karkatatta, duk wanda ya samu tsinkaya kan tarihin wadannan Kabilu biyu a bayyane zai san cewa Wahabiyyya ba komai bane face fitinar girman kai musammam ma a karni na ashirin domin raba kawukan al'ummar musulmi.

Wasu mutane na kokarin danganta Muhammad bn Abdul-Wahab bn Sulaiman ya zuwa asali na larabawa, sai dai cewa masadir daban-daban kamar yanda ya zo cikin tarihin Alu Sa'ud wallafar Nasir Sa'id na karyata wannan da'awa yana kuma tabbatar da cewa ya samo asalin daga dangin Yahudawa wacce aki kira (Dau'imatu) a kasar Turkiyya sun kutso cikin muslunci don cimma hadafin raba kai da rusa gininsa, Sulaimani kakan Muhammad bn Abdul-Wahab sunansa na hakika shi ne (Shauleman) ya kuma kasance a Turkiyya cikin wani gari da ake kira da (Bursatu) ana kiransa da Shaulemanu Karkuzi ma'anar sunan a yaren Turkanci:Kankana, wannan Bayahude ya kasance sanannen `dan kasuwa d ayake sayar da Kankana a garin (Bursatu).

Shauleman ya fito daga wani gari daga garuruwan Sham da rakiyar matarsa sai ya zauna a daya daga garuruwan geffan babban garin Damaskus Siriya ya canja sunansa ya bayyanar da cewa ya muslunta domin samun damar kasuwanci da jabun musluncinsa maimakon kasuwancinsa da Kankana, sai dai cewa mutanen garin Damaskus sun gano hakikarsa sai suka fitar da shi suka koreshi daga garinsu bayan sun masa duka tsiya sai ya gudu kasar Misira, anan ma cikin sauri suka gane hakikaninsa suka koreshi, sai ya tafi kasar Hijaz cikin Madinatul Munawwara daga nan bai zauna ba ya cirata zuwa garin Makka Mukarrama domin yada mugunyar burinsa da sunan addini, sai dai kuma cewa mutanen Makka sun gano niyyarsa take suka fitar da shi, sai ya koma Madina suma dai suka koreshi  a kaskance, dukkanin haka ya faru cikin shekaru hudu, sai ya gudu garin Najad ya zauna a wani gari da ake kira (Al'ainiyyatu) nan ya zauna dindin ha abada, lallai ya samu wannan gari wani fili dandali da zai ci bajokolinsa da yaudara da halakar da mutane sakamakon raunin fahimta da ra'ayi, sai yayi da'awar cewa shi ne ya gangaro ne daga dangin Rabi'atu sanann ya kara da'awar cewa shi daga dangin Tamimi yake, anan garin ya haifi Abdul-Wahab wannan `da da ya haifa sai ya haifi `da ya sa masa sunan Muhammad wanda ya kasance kan hanyar kakanninsa Yahudawa.

Dukkanin wand aya bibiyi tarirhin rayuwar Muhammad bn Abdul-Wahab tun yarintarsa zuwa mutuwarsa bayan shekaru 96 zai tabbatar da cewa tabbas ya kasance kwayar cutar barna da fasadi, kuma yahudancin duniya ne ya tanade shi domin rusau da yada barna da fasadi.

 Muhammad bn Abdul-Wahab cikin samartakarsa ya rungumi neman ilimin addini hakika mahaifinsa da `dan'uwansa sun kasance daga sanannun Malaman addini, sai yayi karatu a hannun mahaifinsa da hannun Malaman Makka da Madina, wadannan Malamai na da yayi karatu a hannunsu duka sun yi hasashe da kirdadon fitinar da zata kasance daga gareshi har ta kai ga `dan'uwansa yayi talifi cikin raddi kan tunaninsa, Muhammad bn Abdul-Wahab ya kasance yana karanta fikhu kan mazhabar Ahmad bn Hanbal wanda akasarin Malaman mazhabobin muslunci suke la'akari da shi matsayin wanda bai nuna cikin ilimi ba kuma bai da gogewa sosai, ya kuma taso kan tunanin Bn Taimiyya da Almajirinsa Bn Kayyim Jauziyya ya zama yana magana da kalmomin da musulmi basa fahimtarsu kuma ya zama ya dinga inkarin akasarin abubuwa da musulmai sukayi ittifaki kan ingancinsu, sannan ya fara wurgo da ratsattsun tunanukansa da sunan tsantsan tauhidi, hakika Malamai sun karyata wadannan sababbin tunanunnuka kuma sun yi rubuce-rubuce cikin raddin kansu da kaucewarsu hanya.

Sai yayi tafiya daga garin Al'ainiyyatu zuwa Makka Almukarrama sannan daga nan ya tafi Madina, ya tsananta inkari kan neman taimako Allah ta'ala da riko da Annabi (S.A.W) a kabarinsa mai daraja, sanna ya koma garin Najad sannan Basara ya zauna cikinta tsawon lokaci sai dai cewa daga karshe mutanen garin sun koreshi , ya dinga yawo daga wannan gari zuwa wancan, bayan mutuwar mahaifinsa sai ya mike da tsageranci sosai kan bayyanar da akidunsa a fili, da inkari kan musulmi, sai lalatattu daga mutane suka bishi bisa kakkausar dabi'asru da son suga ana kai hare-hare da cin ganima da fadada iko nan da can.

Masdarorin tarihinsa sun kawo cewa yaje kasar Iran ya zauna a Isfahan, Ahmad Amin Almisiri ya ambaci cewa Muhammad bn Abdul-Wahab yayi yawo cikin garuruwa kasashen musulmi daban-daban ya zauna shekaru hudu a garin Basara yayi shekaru biyar a garin Bagdad, sannan ya zauna tsawon Shekara guda cir a Kurdistan, yayi shekaru biyu a garin Hamadan, sannan ya tafi Isfahan a can ya karanta Falsafatul Ishrak da Sufanci, sannan ya bar garin ya tafi garin Qum daga nan ne ya koma Kasarsa ta haihuwa wato Saudiyya.

Wannan yawon da yayi bai kasance kara zube babu hadafi da hannun girman kai da makircinsu, bari daio hadafin wannan yawace-yaace nasa shi ne ya san al'adun musulmai da tsarin zamantakewarsa a garuruwansu da kuma neman faka da kafofin da za ayi amfani da su don mallake su da samun dama kansu da gudanar da da'awa kansu.

Shahararren `dan leken asiri dan asalin kasar Birtaniya Mista Hamfar cikin Muzakkararsa yana cewa: na samu sanin wani Matashi da ya  kware cikin yare guda uku Turkanci da Farisanci da Larabci, sunansa Muhammad bn Abdul-Wahab ya kasance matashi mai tsananin buri da tsananin ta'assubanci, ya kasance yana taklidi da kansa da fahimtar kansa cikin fahimtar Kur'ani da sunna yana watsi da ra'ayoyin sauran malamai bawai kadai malaman zamaninsa na mazhabobi hudu  musulmai kawai hatta ra'ayoyin Abubakar da Umar watsi yake da su, hakika na samu bukatata da nake ta cigiyarta, alaka mai karfi ta kullu tsakanina da shi, na kasa ina yawan angiza shi ina zuga shi ian zuzuta shi ina nuna masa yafi Aliyu da Umar baiwa, kuma Manzon Allah da yana raye a zamaninsa da shi zai zaba Halifansa, na kasance ina gaya masa fatana kan cewa ina burin ya jaddada muslunci, na yake shawara tare da shi kan munakasha kan Kur'ani mai girma kan asasin tunaninmu ni da shi, hadafina cikin yin haka shi ne jefa shi cikin tarko, na dinga janye rigar imani daga wuyansa a hankula a hankula, sannu sannu na dinga rura wuta cikin ruhinsa da ya kasance yanada wata hanya ta uku bayan  hanyar sunna da shi'a, ya kasance yana amsawa wannan sababbin tunannuka sabida ya kasance kan ganiyar rudunsa da jin kansa kuma yana biye musu, wata rana na kira shi da kulla `yan'uwantaka tsakanina da shi sai ya yarda muka kulla igiya `yan'uwantaka, daga wannan lokaci na kasance ina masa rakiya cikin dukkanin tafiye-tafiyensa duk inda ya kasance muna tare da juna, na kasance ina himmatuwa ina burin ganin bishiyar da na shuka ta bada `ya`ya wannan bishiya da kashe mata dukiya mai tarin yawa a lokacin samartakata, na kasance kowanne wata ina aikawa da sakamako da natija zuwa garin London, sannan amsa tana zuwa gareshi da karfafani da yabawa aikina, aikin da aka sani a kansa shi ne in ga na samar da ruhin shakku cikins, na kasance a koda yaushe ina yi masa bushara da cewa gobensa tana da haske da daukaka, yayinda ya ji baya kaunar cigaba da zama a garin Basara na rigaya na yi masa ishara da ya tafi kasar Iran, nace masa, kayi taka tsantsan da shi'a ka amfani zama a garinsu kayi kokarin sanin al'adunsu da halayensu, lallai hakan zai amfanar da kai nan gaba a rayuwarka, sai umarni ya zo mini daga London da cewa lallai inyi maza-zama na koma London sai na tafi can, bayan zuwan na gana da shugaban leken asiri ya kuma bayyana jin dadinsa da farin cikinsa bisa ikon da na samu kan Muhammad bn Abdul-Wahab ya ce mini lallai shi wannan matashi shi ne babbar Barewar da nuke ta Farautarta muke burin kamata, ya tambayeni shin da fatan dai har yanzu bn Abdul-Wahab yana nan kan tunani da akidun dana dora shi akai ko?!, lallai ta kai gay a buga waya zuwa ga yaranmu na garin Isfahan ya ce shi ne `dan'uwan Shaik Muhammad wato yana nufin shi ne ni, na zauna a London tsawon lokaci har zuwa lokacin da umarni ya zo mini da cewa in kara komawa kasar Iraki a karo na biyu domin kammala aikina tare da Muhammad bn Abdul-Wahab, an umarceni inyi magana da shi komai a bayyana karara babu wani boye-boye, sunce mini lallai yaronsu a Isfahan ya riga ma yayi magana da shi, Shaik ya yarda da kudirin `yan mulkin mallaka kan sharadin su bashi cikakkiyar kariya daga hukumomi da malamai da zsu yi tunani kai masa hari a lokacin da yake bayyanar da ra'ayoyinsa da tunaninsa, sannan ma'aikatar leken asirin ta tsinkayar dani kan shirinta da ya zama wajibi Shaik ya zartar, sune:

1-kafirta baki dayan musulmai da kwace dukiyarsu da keta alfarmarsu da mayar da mazansu da matansu su bayi cikin dabara.

2-ruguje dakin Ka'aba –idan dama ta samu- da hujjar la'akari da ita matsayin kufai ne na bautar gumaka, da hana mutane aikin hajji da zuga Kabilu su kwace dukiyar mahajjata su kashe su.

3-rusa Kubbobi da Kaburbura da wurare masu tsarki a wurin musulmai a cikin garin Makka da Madina da sauran garuruwan musulmai da hakan zai yiwuwa da hujjar cewa wurin bautar Gumakai ne da shirka, kaskantar da darajar Annabi Muhammad (S.A.W) da sauaran mazajen muslunci gwargwadon yanda aka samu iko kan haka

   4- yada rashin doka da oda da ta'addanci gwargwadon iko.

Yayin da na dawo gabas ta tsakiya na hadu da Shaik kuma yayi mini alkawarin zartar da wannan shiri da makircin girman kai yan leken asiri, bayan wasu `yan shekaru kan wannan aiki ma'aikatar leken asirin Birtaniya ta samu damar farauto (Muhammad bn Sa'ud) ta jawo shi jikinta, sai suka sanar dani cewa dole Bn Abdul-Wahab da Bn Sa'ud su yi aiki tare da juna kafada da kafada da juna, Muhammad bn Sa'ud ya rike bangaren hukuma shi kuma Muhammad bn Abdul-Wahab bangaren Malunta, da haka ne muka riki garin Addar'iyyatu Shelkwatar sabuwar hukuma da addini.

A hakane su biyu suka dinga ta biya kan tsare-tsarenmu.[1]

Dan'uwa mai karatu, karkashin wadanann abubuwa masu fadi wadanda muka kawo maka cikin gaggawa zaka fahimci cewa Wahabiyya kirkire da kagar Muhammad bn Abdul-Wahab kuma bata bakin komai face fitinar girman kai da yahudancin duniya, duk da sun lullube kansu da'awar karya ta tsantsar tauhidi da tafiya kan hanya magabata nagargarru, a hakika babu wani abu mai kama da haka kawai son yaudarar mutane ne da batar da su da amfani da raunana masu tsarkin zuciya da neman gaskiya, hakika sun yi nasara cikin manya-manyan garuruwan musulmai (Makka da Madina) sai dia cewa hakika ubangijinka yana madagata, lallai Allah yana jinkiri d akau da da daga kafa amma fa baya gafala, da sannu zai cika kasa da adalci da daidaiti bayan cikarta da zalunci da danniya, da sannu bayin nagargaru zasu gjae kasa.

Lallai Allah baya saba alkawarinsa.  

[1]


Tura tambaya