Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Jarrabawar Allah mai girma da `daukaka ga wasiyyan annabawa cikin rayuwar annabawa (as)
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Jarrabawar Allah mai girma da `daukaka ga wasiyyan annabawa cikin rayuwar annabawa (as)

قال: إنّا نجد في الكتاب: أن الله عز وجل إذا بعث نبياً أوحى إليه أن يتخذ من أهل بيته من يقوم بأمر أمته من بعده، وأن يعهد إليهم فيه عهداً يحتذى عليه، ويعمل به في أمته من بعده.

وأن الله عز وجل يمتحن الأوصياء في حياة الأنبياء، ويمتحنهم بعد وفاتهم. فأخبرني كم يمتحن الله الأوصياء في حياة الأنبياء؟! وكم يمتحنهم بعد وفاتهم من مرة؟!

وإلى ما يصير آخر أمر الأوصياء إذا رضي محنتهم؟!

فقال له علي×: والله الذي لا إله غيره، الذي فلق البحر لبني إسرائيل، وأنزل التوراة على موسى×، لئن أخبرتك بحق عما تسأل عنه لتقرن به؟!

قال: نعم.

Sai ya ce: mu mun samu cikin littafi: lallai Allah mai girma da `daukaka idan ya aiko annabi yana yin wahayi gare shi da ya zaba daga Ahlin gidansa wanda zai jagoranci al’amarin al’ummarsa bayansa, kuma ya riki alkawali zuwa ga al’ummarsa cikinsa zai bi sawunsa kuma zai aiki da shi cikin al’ummarsa bayansa, sannan kuma lallai Allah yana jarraba wasiyyai cikin rayuwar annabawa haka ma yana jarrabasu bayan wafatinsu. Saboda haka ka bani labari karo nawa Allah yake jarrabar wasiyyai lokacin rayuwar annabawa haka ma sau nawa yake jarrabarsu bayan wafatinsu?

Sannan zuwa ga mene ne al’amarin wasiyyai ke tukewa idan sun cinye jarrabawar?

sai Ali (as) ya ce masa: na rantse wanda babu abin bauta face shi, wanda ya tsaga tafki ga banu Isra’ila ya kuma saukar da littafin attaura ga Musa (as) shin idan na baka labarin abin da ka tambaya zaka yi imani da shi?

Sai bahayuden ya ce: eh

قال: والذي فلق البحر لبني إسرائيل، وأنزل التوراة على موسى× لئن أجبتك لتسلمن؟!

قال: نعم.

فقال له علي×: إن الله عز وجل يمتحن الأوصياء في حياة الأنبياء في سبعة مواطن ليبتلي طاعتهم، فإذا رضي طاعتهم ومحنتهم أمر الأنبياء أن يتخذوهم أولياء في حياتهم وأوصياء بعد وفاتهم، ويصير طاعة الأوصياء في أعناق الأمم ممن يقول بطاعة الأنبياء.

ثم يمتحن الأوصياء بعد وفاة الأنبياء «عليهم السلام» في سبعة مواطن ليبلو صبرهم، فإذا رضي محنتهم ختم لهم بالسعادة، ليلحقهم بالأنبياء، وقد أكمل لهم السعادة.

قال له رأس اليهود: صدقت يا أمير المؤمنين، فأخبرني كم امتحنك الله في حياة محمد من

وكم امتحنك بعد وفاته من مرة؟!

وإلى ما يصير أخر أمرك؟!

فأخذ علي× بيده وقال: انهض بنا أنبئك بذلك.

فقام إليه جماعة من أصحابه، فقالوا: يا أمير المؤمنين، أنبئنا بذلك معه.

فقال: إني أخاف أن لا تحتمله قلوبكم.

قالوا: ولم ذاك يا أمير المؤمنين؟!

قال: لأمور بدت لي من كثير منكم.

Ya ce na rantse da wanda ya tsaga tafki ga banu Isra’ila ya kuma saukarwa Musa (as) attaura idan na amsa abin da ka tamabaya zaka muslunta?

Sai ya ce: na’am

Sai Ali (as) ya ce: Allah mai girma da `daukaka ya na jarraba wasiyyai a wurare guda bakwai sa’ilin rayuwar annabawa domin ya gwada biyayyarsu, idan ya karbi biyayyarsu da jarrabarsu sai ya umarci annabawa da su rike su waliyansu cikin rayuwarsu da kuma wasiyyai bayan wafatinsu sai biyayya da wasiyyai ta ratayu a wuyan al’ummar da suke imani da biyayyar annabawa.

sannan sai ya jarrabawa wasiyyai bayan wafatin annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su a wurare bakwai domin gwada hakurinsu, idan ya yarda da jarrabawar ta su sai ya yi musu katama da farin ciki domin ya riskar da su da annabawa, hakika ya kammala musu azurta da farin ciki, sai wannan jagaban yahudawa ya ce masa: kayi gaskiya ya sarkin muminai, yanzu ka bani labari sau nawa Allah ya jarrabeka a lokacin rayuwar Muhammad hakama karo nawa ya jarrabaka bayan wafatinsa?? ga me karshen al’amrinka zai karkare ya tuke?

Sai Ali (as) ya kama hannunsa ya ce tashi muje in baka labarin wannan tambaya, sai ya tashi tare da jama’a daga sahabbansa suka ce ya sarkin muminai bamu labari tare da shi gameda wannan tambaya?

Sai ya ce: lallai ina tsoran ka da zuciyarku ta gaza dauka!

Sai suka ce: mene ne zai sanya hakan ya sarkin muminai ?

Sai ya ce : saboda wasu al’amura da suka bayyana gareni daga da yawa daga gare ku

فقام إليه الأشتر، فقال: يا أمير المؤمنين، أنبئنا بذلك، فوالله إنا لنعلم أنه ما على ظهر الأرض وصي نبي سواك، وإنّا لنعلم أن الله لا يبعث بعد نبينا | نبياً سواه، وأن طاعتك لفي أعناقنا موصولة بطاعة نبينا.

فجلس علي×، وأقبل على اليهودي فقال: يا أخا اليهود، إن الله عز وجل امتحنني في حياة نبينا محمد | في سبعة مواطن، فوجدني فيهن ـ من غير تزكية لنفسي ـ بنعمة الله له مطيعاً.

Sai Ashtar ya mike ya ce: ya sarkin muminai ka bamu labari game da waccan tambayar, wallahi mu mun san lallai babu wani wasiyyi dake doron kasa in banda kai, lallai mu mun san cewa lallai Allah bai turo wani annabi bayan annabi ba face shi, tabbas biyayyarka tana kan wuyayanmu sadaddarda da `da’ar annabinmu.

Sai Ali (as) ya zauna ya fuskanto wannan bayahude ya ce: ya kai bayahude, lallai Allah mai girma da `daukaka ya jarrabeni cikin rayuwar annabi Muhammad cikin wurare bakwai, sai ya same ni cikinsu mai `da’a bawai ina son zuga da tsarkake kaina bane

قال: وفيم يا أمير المؤمنين؟!

قال: أما أولهن فإن الله عز وجل أوحى إلى نبينا | وحمله الرسالة وأنا أحدث أهل بيتي سناً، أخدمه في بيته، وأسعى في قضاء بين يديه في أمره، فدعا صغير بني عبد المطلب وكبيرهم إلى شهادة أن لا إله إلا الله، وأنه رسول الله، فامتنعوا من ذلك وأنكروه عليه وهجروه، ونابذوه واعتزلوه، واجتنبوه وسائر الناس مقصين له ومخالفين عليه، قد استعظموا ما أورده عليهم مما لم تحتمله قلوبهم، وتدركه عقولهم.

فأجبت رسول الله | وحدي إلى ما دعا إليه مسرعاً مطيعاً موقناً، لم يتخالجني في ذلك شك، فمكثنا بذلك ثلاث حجج وما على وجه الأرض خلق يصلي أو يشهد لرسول الله | بما آتاه الله غيري وغير ابنة خويلد «رحمها الله» وقد فعل

Ya ce: cikin me fa ya sarkin muminai?

Sai ya ce: amma ta farkonsu shi ne lallai Allah mai girma da `daukaka ya yi wahayi zuwa ga annabinmu ya dora masa sako,  lokacin ni ne mafi karancin shekaru a gidanmu ina hidima cikin gidansa da fafutika da kai kawo cikin zartar da bukatun al’amrinsa, sai ya kirayi manya da kananan gidan Abdul-mudallib zuwa ga Kalmar shahada da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah da kuma cewa shi manzon Allah ne, sai suka ki Kalmar shahada sukai inkari suka kaurace masa suka guje masa sukai watsi da shi suka nesance shi, sauran mutane kuma daga mai nesa-nesa da shi sai wanda ya saba masa, hakika sun ga girman abin da ya zo musu da shi daga abin da zukatansu suka kasa dauka hankulansu suka kasa riska, sai ni kadai na amsawa manzon Allah abin da ya yi kira zuwa gare shi ina mai gaggawa ina halin gamsuwa tare da `da’a, kwata shakka bata zakke mini cikin hakan, muka zauna tsahon shekaru uku cikin wannan hali babu wani mutum da yake doron kasa da yake sallah tare da gasgata abin da manzon Allah ya zo da shi face ni da Khadija `yar kuwailid Allah ya rahamceta, hakika ya aikata.

ثم أقبل× على أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين.

Sai Ali (as) ya waiwaya ga sahabbansa ya ce shin ba haka bane.

Sai suka ce: haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: وأما الثانية، يا أخا اليهود، فإن قريشاً لم تزل تخيل الآراء، وتعمل الحيل في قتل النبي |، حتى كان آخر ما اجتمعت في ذلك يوم الدار ـ دار الندوة ـ وإبليس الملعون حاضر في صورة أعور ثقيف، فلم تزل تضرب أمرها ظهراً لبطن حتى اجتمعت آراؤها على أن ينتدب من كل فخذ من قريش رجل، ثم يأخذ كل رجل منهم سيفه، ثم يأتي النبي | وهو نائم على فراشه، فيضربونه جميعاً بأسيافهم ضربة رجل واحد فيقتلوه، وإذا قتلوه منعت قريش رجالها ولم تسلمها فيمضي دمه هدراً.

فهبط جبرئيل× على النبي | فأنبأه بذلك، وأخبره بالليلة التي يجتمعون فيها، والساعة التي يأتون فراشه فيها، وأمره بالخروج في الوقت الذي خرج فيه إلى الغار.

فأخبرني رسول الله | بالخبر، وأمرني أن أضطجع في مضجعه، وأقيه بنفسي، فأسرعت إلى ذلك مطيعاً له، مسروراً لنفسي بأن أقتل دونه.

فمضى× لوجهه، واضطجعت في مضجعه، وأقبلت رجالات قريش موقنة في أنفسها: أن تقتل النبي |، فلما استوى بي وبهم البيت الذي أنا فيه ناهضتهم بسيفي، فدفعتهم عن نفسي بما قد علمه الله والناس

Sai ya ce: amma jarrabawa ta biyu, ya kai bayahude, lallai kuraishawa basu gushe ba suna hiyalin ra’ayoyi suna ta shirya dabaru kan ya zasu kashe annabi har ya kasance daga karshe suka tattaru cikin wannan gidan nuduwa iblisu ya la’ananne ya halarci taron nasu cikin surar a’awar sakifu basu gushe ba suna ta shawarwari har suka kai ga cimma cewa cikin kowanne gidan kuraihsawa a zabi mutum guda ya dauki takobi ya jewa annabi lokacin da yake kwance kan shimfidar barcinsa sai dukkaninsu suyi tgarayya cikin sara masa takubbansu saran mutum guda su kashe shi sai kurasihawa su hana mazajensu daukar fansarsa suki sallama su sai jininsa ya tafi sakaka babu kisasi babu fansa.

Sai Jibrilu ya sauko wajen annabi ya bashi labarin shirye-shiryensu da daren da zasu taru cikinsa da lokacin da zasu zo shimfidarsa, ya kuma umarce shi da fita lokacin da zai fita zuwa kogo, sai manzon Allah ya bani labari ya umarce ni in kwanta kan shimfidarsa mazajensa kuraishawa suka fuskanto alhalin suna cikin yakini da kawukansu na cewa zasu kashe annabi yayin da gida ya tattaru ni da su sai na yake su da takobina na kare kaina da abin da hakika Allah ya sanar da shi tare da mutane

ثم أقبل× على أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

sai ya waiwayi sahabbansa ya ce: shin ba haka bane?

Sai suka ce: na’am haka ne ya sarkin muminai

فقال×: وأما الثالثة يا أخا اليهود فإن ابني ربيعة وابن عتبة كانوا فرسان قريش دعوا إلى البراز يوم بدر، فلم يبرز لهم خلق من قريش، فأنهضني رسول الله | مع صاحبي ـ رضي الله عنهما ـ وقد فعل وأنا أحدث أصحابي سناً، وأقلهم للحرب تجربة، فقتل الله عز وجل بيدي وليداً وشيبة، سوى من قتلت من جحاجحة قريش في ذلك اليوم، وسوى من أسرت، وكان مني أكثر مما كان من أصحابي، واستشهد ابن عمي في ذلك رحمة الله عليه

Sai ya ce: amma jarrabawa ta uku ya kai bahayude hakika bn rabi’atu da bn utubatu sun kasance sadaukan kuraishawa sun gayyaci kwamawa gaba da gaba ranar yakin badar babu wanda ya fito buga yaki da su bisa sanin abin da ka iya wakana, sai Allah mai girma `daukaka ya halaka walidu da shaibatu a hannuna, face wanda manyan kauraishawa suka kar wannan rana da wadanda saka kama matsayin ribatattun yaki, sannan abin da ya kasance daga gare ni ya zarce abin da ya kasance daga abokanaina, baffana ya yi shahada a wannan rana Allah ya jikansa.

ثم التفت إلى أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Ya waiwaya ga sahabbansa ya ce: shin ba haka bane?

Sai suka kwarai da gaske ya sarkin muminai.

فقال علي×: وأما الرابعة يا أخا اليهود، فإن أهل مكة أقبلوا إلينا على بكرة أبيهم، قد استحاشوا [أو استجاشوا] من يليهم من قبايل العرب وقريش، طالبين بثأر مشركي قريش في يوم بدر

Sai Ali (as) ya ce: amma jarrabawa ta hudu ya bahayahude, lallai mutane garin makka sun tattaru sun fuskanto mu lokacin suka firgita daga wadanda ke kusa da su daga kabilun larabwa da kuraishawa suna neman fansar mushrikan kuraishawa a ranar badar

فهبط جبرئيل× على النبي |، فأنبأه بذلك، فذهب النبي | وعسكر بأصحابه في سد أحد، وأقبل المشركون إلينا، فحملوا إلينا [لعل الصحيح: علينا] حملة رجل واحد، واستشهد من المسلمين من استشهد، وكان ممن بقي من الهزيمة، وبقيت مع رسول الله |.

ومضى المهاجرون والأنصار إلى منازلهم من المدينة كل يقول: قتل النبي | وقتل أصحابه، ثم ضرب الله عز وجل وجوه المشركين. وقد جرحت بين يدي رسول الله | نيفاً وسبعين جرحة منها هذه وهذه ـ ثم ألقى× رداءه، وأمر يده على جراحاته ـ وكان مني في ذلك ما على الله عز وجل ثوابه إن شاء الله.

ثم التفت× إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sai jibrilu ya sauka wajen annabi (s.a.w) ya bashi labari sai annabi (s.a.w) ya tafi tare da sahabbansa, mushrikai suka nufo mu suka kai mana hari irin harin mutum guda wanda sukai shahada daga musulmai sukai shahada, daga cikin wanda suka wanzu daga faduwa suka kasance, ni kuma na kasance tare da annabi, mutanen makka da madina suka tafi gidajensu, hakika na samu rauni a gaban manzon Allah (s.a.w) kusan rauni fiye da saba’in daga wannan da wancan, sannan manzon Allah (s.a.w) ya sanya rigarsa kan rauni ya murza hannunsa kai, ya kasance daga gareni abin da kadai ladansa na wajen Allah insha’Allah.

Sai ya waiwayi sahabbansa ya ce: ko ba haka bane?

Suka ce kwarai da gaske

فقال×: وأما الخامسة يا أخا اليهود، فإن قريشاً والعرب تجمعت وعقدت بينها عقداً وميثاقاً لا ترجع من وجهها حتى تقتل رسول الله، وتقتلنا معه معاشر بني عبد المطلب.

ثم أقبلت بحدها وحديدها حتى أناخت علينا بالمدينة، واثقة بأنفسها فيما توجهت له

فهبط جبرئيل× على النبي |، فأنبأه بذلك، فخندق على نفسه ومن معه من المهاجرين والأنصار.

فقدمت قريش، فأقامت على الخندق محاصرة لنا، ترى في أنفسها القوة، وفينا الضعف، ترعد وتبرق ورسول الله | يدعوها إلى الله عز وجل، ويناشدها بالقرابة والرحم، فتأبى، ولا يزيدها ذلك إلا عتواً، وفارسها وفارس العرب يومئذ عمرو بن عبد ود، يهدر كالبعير المغتلم يدعو إلى البراز، ويرتجز ويخطر برمحه مرة، وبسيفه مرة، لا يقدم عليه مقدم، ولا يطمع فيه طامع، ولا حمية تهيجه ولا بصيرة تشجعه.

فأنهضني إليه رسول الله |، وعممني بيده، وأعطاني سيفه هذا، وضرب بيده إلى ذي الفقار، فخرجت إليه ونساء أهل المدينة بواك إشفاقاً عليّ من ابن عبد ود، فقتله الله عز وجل بيدي، والعرب لا تعد لها فارساً غيره، وضربني هذه الضربة ـ وأومأ بيده إلى هامته

فهزم الله قريشاً والعرب بذلك، وبما كان مني فيهم من النكاية.

ثم التفت× إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين.

Sannan ya ce: amma jarrabawa ta biyar ya kai bayahude, lallai kuraishawa da ragowar larabawa sun tattara kansu sunyi taro sun kulla yarjejeniya da alkawali da cewa ba zasu komo makka ba har sai sun kashe manzon Allah (s.a.w) da `ya`yan Abdul-mudallib sannan suka fito da dukkanin karfinsu suka sauka kanmu a madina suna masu yarda da imani da kawukansu cikin abin da suka nufa , sai mala’ika Jibrilu ya sauka wajen annabi (s.a.w) ya bashi labari shirin da suke, sai ya haka rami domin kare kansa da kuma kare wadansda suke tare da shi daga muhajirun da ansar, sai kuraishawa suka fuskanto suka tsaya bakin ramin suna masu yi mana kawanya da kewaya da taskace mu suna ganin kansu masu karfi suna kallon mu raunana suna ta walkawa da rawar daji shi ko manzon Allah (s.a.w) yana ta kiransu zuwa ga Allah mai girma da `daukaka yana ta rokonsu da su yi imani yana hada su da kusanci da zumunci ke tsakaninsu suka ki sannan babu abin da kiran ya kara musu face dagawa da tsaurin kai, a wannan rana sadaukin cikinsu sadaukin cikin larabawa amru bn zul wuddi yana ta rawar daji yana ta wulwula mashin a yake a hannunsa da takobinsa an rasa wanda zai fito daga cikin musulmi ya kwama da shi gaba da gaba babu mai kwadayi cikin yaki da shi babu wanda wani kishinsa ya motsa da zai buga da shi babu wani da aka iya samu basirarsa ta karfafa fa shi da yin yaki da shi.

Sai manzon Allah (s.a.w) ya tashe ni ya nada mini rawani da hannusa ya bani wannan takobin tasa na ya buga hannu zuwa ga takobin zulfikar sannan na fito mubaraza da shi matayen madina suna ta rusa kuka saboda tausayina kan hatsarin wanda zan yaki da shi amru bn zul wuddi. Allah mai girma da `daukaka ya halaka shi da hannuna, wanda larabawa basu da wani sadauki jarumi in banda shi. Ya sare ni wannan sara ya sunkuyar da hannunsa ga wuyansa. Sai Allah ya karya larabawa da kuraishawa da wannan da jarumtar da ta kasance daga gare ni cikinsu daga halaka ibn zul wuddu da yaye bakin ciki.

Sai ya waiwayi sahabbansa ya ce shin ba haka bane?

Suka ce: na’am hakane ya sarkin muminai

فقال×: وأما السادسة يا أخا اليهود، فإنا وردنا مع رسول الله | مدينة أصحابك خيبر على رجال من اليهود وفرسانها من قريش وغيرها، فتلقونا بأمثال الجبال من الخيل والرجال والسلاح، وهم في أمنع دار، وأكثر عدد، كل ينادي ويدعو ويبادر إلى القتال، فلم يبرز إليهم من أصحابي أحد إلا قتلوه، حتى إذا احمرت الحدق، ودعيت إلى النزال وأهمت كل امرئ نفسهوالتفت بعض أصحابي إلى بعض وكل يقول: يا أبا الحسن انهض، فأنهضني رسول الله | إلى دارهم، فلم يبرز إلي منهم أحد إلا قتلته، ولا يثبت لي فارس إلا طحنته، ثم شددت عليهم شدَّة الليث على فريسته، حتى أدخلتهم جوف مدينتهم مسدداً عليهم، فاقتلعت باب حصنهم بيدي، حتى دخلت عليهم مدينتهم وحدي، أقتل من يظهر فيها من رجالها، وأسبي من أجد من نسائها حتى أفتتحها وحدي، ولم يكن لي فيها معاون إلا الله وحده.

ثم التفت× إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sannan ya ce:amma jarrabawa ta shida ya kai bayahude, lallai mu tare da manzon Allah (s.a.w) mun gangara garin mutanenka mutanen kaibar kan wasu mazaje daga yahudawa da jarumansu daga kurasihawa da wasunsu sai suka tarbe mu da misalin duwatsu da dawakai da mazaje da makamai, sun kasance cikin mafi kariyar gida da mafi yawan adadi, kowannensu yana kira zuwa ga yaki babu wani mutum dai zai fito daga abokaina face sun kashe shi har lokacin da ido ya yi jajawur aka kira ni zuwa ga kwamawa da mubaraza abokaina junansu ya waiwayi juna kowannensu yana fadin ya baban Hassan tashi mana, sai manzon Allah (s.a.w) ya tashe ni zuwa shingensu babu wani mutum da ya fito kaina face na halaka shi babu wani mahayi da zai tsaya gabana face na soke shi sannan na kai musu bara irin barar da zaki ke kaiwa abin farautarsa har ta kai da na kutsa tsakiyar garinsu na karya kofar shingensu  da hannuna na shiga ciki ni kadai ina hallaka dukkanin wanda ya tunkaro ni ina ribartar da wacce na samu daga matansu har sai da na karyasu ni kadai na bude garin ni kadai Allah kadai ya kasance mai taimakona cikin yakin babu kowa sai ni kadai.

Suka ce: haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: وأما السابعة يا أخا اليهود، فإن رسول الله | لما توجه لفتح مكة أحب أن يعذر إليهم، ويدعوهم إلى الله عز وجل آخراً كما دعاهم أولاً، فكتب إليهم كتاباً يحذرهم فيه وينذرهم عذاب الله، ويعدهم الصفح ويمنيهم مغفرة ربهم، ونسخ لهم في آخره سورة براءة ليقرأها عليهم، ثم عرض على جميع أصحابه المضي به، فكلهم يرى التثاقل فيه.

فلما رأى ذلك ندب منهم رجلاً، فوجهه به، فأتاه جبرئيل، فقال: يا محمد لا يؤدي عنك إلا أنت أو رجل منك، فأنبأني رسول الله | بذلك، ووجهني بكتابه ورسالته إلى أهل مكة، فأتيت مكة وأهلها من قد عرفتم ليس منهم أحد إلا ولو قدر أن يضع على كل جبل مني إرباً لفعل، ولو أن يبذل في ذلك نفسه وأهله وولده وماله.

فبلغتهم رسالة النبي | وقرأت عليهم كتابه، فكلهم يلقاني بالتهدد والوعيد، ويبدى لي البغضاء، ويظهر الشحناء من رجالهم ونسائهم، فكان مني في ذلك ما قد رأيتم.

ثم التفت إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sai ya ce: amma jarrabawa ta bakwai ya kai bayahude, lallai manzon Allah (s.a.w) sa’ailin da ya tafi bude makka ya so ya sama musu uzuri ya kira su zuwa ga Allah mai girma da `daukaka kamar yadda ya kirasu tun farko, sai ya rubuta wasika gare su yana tsoratar da su cikinta yana kuma yi musu gargadi daga azabar Allah ya kuma yi musu alkawarin afuwa da yafiya ya kwadaitar dasu gafarar ubangijinsu, daga karshen wasikar ya rubuta musu suratul bara’a domin dan sakon ya karanta musu sai ya bijiro da tafiya da wasikar ga baki dayan sahabbansa, sai dukkaninsu suka noke suka ga nauyin sakon, yayin da ya ga haka sai ya kirayi mutum daya daga cikinsu ya bashi ya tafi da sakon, sai mala’ika Jibrilu ya sauko take ya ce: ya Muhammadu babu mai sauke wannan sako sai kai da kanka ko kuma wani mutum daga gareka, sai manzon Allah (s.a.w) ya bani labari ya umarce ni da tafiya da wannan sako zuwa makka, sai na shiga makka da mutanenta wanda kuka riga kuka sani babu wani mutum daga gare su da ace zai samu iko sanya wani yanki kan kowanne dutse daga gabobin jikina da ya aikata, na isar musu da sakon annabi (s.a.w) na karanta musu wasikar kowannensu na yi mini barazana da alkawali da ukuba da nuna mini kiyayya. matsananciyar kiyayya na bayyana daga mazajensu da matansu, sai ya kasance daga gare ni abin da kuka gani.

Sannan ya waiwayi sahabbansa ya ce shin ba haka bane, suka ce: haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: يا أخا اليهود، هذه المواطن التي امتحنني فيها ربي عز وجل مع نبيه |، فوجدني فيها كلها بمنه مطيعاً، ليس لأحد فيها مثل الذي لي ولو شئت لوصفت ذلك، ولكن الله عز وجل نهى عن التزكيةفقالوا: يا أمير المؤمنين، صدقت والله، ولقد أعطاك الله عز وجل الفضيلة بالقرابة من نبينا | وسلم، وأسعدك بأن جعلك أخاه، تنزل منه بمنزلة هارون من موسى، وفضلك بالمواقف التي باشرتها، والأهوال التي ركبتها، وذخر لك الذي ذكرت وأكثر منه مما لم تذكره، ومما ليس لأحد من المسلمين مثله، يقول ذلك من شهدك منا مع نبينا |، ومن شهدك بعدهفأخبرنا يا أمير المؤمنين ما امتحنك الله عز وجل به بعد نبينا | فاحتملته وصبرت، فلو شئنا أن نصف ذلك لوصفناه علماً منا به، وظهوراً منا عليه، إلا أنّا نحب أن نسمع منك ذلك، كما سمعنا منك ما امتحنك الله به في حياته فأطعته فيه.

فقال×: يا أخا اليهود، إن الله عز وجل امتحنني بعد وفاة نبيه | في سبعة مواطن فوجدني فيهن ـ من غير تزكية لنفسي ـ منه [لعل الصحيح: بمنِّه] ونعمته صبورا ً

وأما أولهن يا أخا اليهود، فإنه لم يكن لي خاصة دون المسلمين عامة أحد آنس به أو أعتمد عليه، أو أستنيم إليه، أو أتقرب به غير رسول الله |. هو رباني صغيراً، وبوأني كبيراً، وكفاني العيلة، وجبرني من اليتم، وأغناني عن الطلب، ووقاني المكسب. وعال لي النفس والولد والأهلهذا في تصاريف أمر الدنيا مع ما خصني به من الدرجات التي قادتني إلى معالي الحق عند الله عز وجل.

فنزل بي من وفاة رسول الله | ما لم أكن أظن الجبال لو حملته عنوة كانت تنهض به، فرأيت الناس من أهل بيتي ما بين جازع لا يملك جزعه، ولا يضبط نفسه، ولا يقوي على حمل فادح ما نزل به، قد أذهب الجزع صبره، وأذهل عقله، وحال بينه وبين الفهم والافهام والقول والإسماع

وسائر الناس من غير بني عبد المطلب بين معز يأمر بالصبر، و بين مساعد باك لبكائهم، جازع لجزعهم.

وحملت نفسي على الصبر عند وفاته بلزوم الصمت والاشتغال بما أمرني به من تجهيزه، وتغسيله وتحنيطه وتكفينه، والصلاة عليه، ووضعه في حفرته، وجمع كتاب الله وعهده إلى خلقه، لا يشغلني عن ذلك بادر دمعة، ولا هائج زفرة، ولا لاذع حرقة، ولا جزيل مصيبة حتى أديت في ذلك الحق الواجب لله عز وجل ولرسوله | علي، وبلغت منه الذي أمرني به، واحتملته صابراً محتسباً.

ثم التفت× إلى أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sai ya ce: ya kai dan’uwa bayahude wadannan sune wurare

bakwai da Allah mai girma da daukaka ya jarraba ni cikinsu tare da annabinsa (s.a.w) sai ya same ni cikinsu mai biyayya tare da tallafawar karamcinsa, sai dai cewa Allah ya hana tsarkake kai sai suka ce:ya sarkin muminai wallahi kayi gaskiya, hakika Allah mai girma da `daukaka ya baka falala ta hanyar kusancinka da annabinmu (s.a.w) ya kuma azurtaka da sanyaka dan’uwan annabi kana matsayi da shi irin matsayin haruna daga musa, ya kuma fifita da wuraren da kai gogayya da su hatsarin da ka zakkewa, ya kuma tanadar maka abin da ka ambata da fiye da haka daga abubuwan a baka ambata ba. Daga abin da babu wanda yake da irinsu daga musulmi, wanda ya ganka daga cikinmu tare da annabinmu (s.a.w) yana shaida hakan da ma wanda ya zauna da kai bayan annabi (s.a.w) saboda haka ka bamu labari ya sarkin muminai da mene ne Allah mai girma da `daukaka ya jarrabceka bayan wafatin annabinmu (s.a.w) cikin wurare bakwai wanda ka jurewa jarrabawar kayi hakuri kai, lallai da mun so da mun siffanta hakan da kanmu sakamakon saninmu da hakan da kuma bayyanarsa garemu, sai dai cewa muna begen muji daga bakinka kamar yadda muka ji jarrabawar da Allah ya yi maka lokacin da annabi (s.a.w) yake raye kuma kayi masa biyayya cikinsu. Sai (as)  ya ce ya kai bayahude lallai Allah mai girma da `daukaka ya jarrabani bayan wafatin annabinsa (s.a.w) a wurare bakwai ba ina son wanke kaina da tsarkake shi sai cikinsu tare da ni’imarsa da karamcinsa ya same ni  mai hakuri.

Amma ta farkonsu ya kai bayahude, lallai yadda lamarin yake shi ne banda wani mutum kebance da ni koma bayan dukkanin  musulmai da bake nutsuwa da shi nake dogaro da shi ko kuma nake kusanta da shi face manzon Allah (s.a.w) shi ne wanda ya kula da tarbiya ta ina yaro karami ya bani masauki ina babba. Ya isar mini daga bukata, ya dora ni daga karayar maraici, ya wadatar daga nema, ya tseratar dani daga tsiwirwira, ya dauke mini nauyin kaina da `ya`yana da iyalina wannan duka cikin bukatun duniya kenan tare da abin da ya kebance ni daga darajoji da suka kaini madaukakan martabobin gaskiya  wajen Allah mai girma da `daukaka, bayan wafatinsa sai wani abu ya sauka kaina wanda bana tsammani ko kan duwatsu aka dora shi za su iya mikewa tsaye da shi, sai naga mutane gidana daga wanda yake raki ya kasa daure rakinsa ya kasa taushe zuciyarsa ya gaza daukar nauyin abin da ya sauka kansa. Hakika gigita ta tafi da hakurinsa ta buga kwakwalwarsa ta shiga tsakaninsa da tsakanin fahimta da fahimtarwa da magana da jiyarwa, ragowar mutane daga wadanda ba daga`ya`yan Abdul-mudallib suke ba daga ma’abocin izza yana umarni da hakuri da kuma mai taimako wanda yake kuka da saboda kukansu da kuma mai gigita da raki daga gigitarsu, sai na rarrashi kaina da yin hakuri lokacin wafatinsa (s.a.w) da kuma lazimta kame baki da shagaltuwa da abin da ya umarce ni da shi daga shirya jana’izarsa da yi masa wankan gawa da sanya masa turare da likkafani da yi masa sallah da sanya shi  cikin kabarinsa, da kuma tattara littafin Allah da alkawalinsa zuwa ga halittunsa, kuka rashinsa bai shagaltar dani daga shirya shi ba haka radadin da kunan zuciya, haka ma girman musiba da afku har sai da na sauke wannan hakki da yake wuyana na isar da abin da ya umarce ni, na danne nayi juriya da hakuri!

Sai ya waiwayi sahabannsa shin hakan ba ta faru ba?

Suka ce: haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: وأما الثانية يا أخا اليهود، فإن رسول الله | أمَّرني في حياته على جميع أمته، وأخذ على جميع من حضره منهم البيعة والسمع والطاعة لأمري، وأمرهم أن يبلغ الشاهد الغائب ذلك.

فكنت المؤدى إليهم عن رسول الله | أمره إذا حضرته، والأمير على من حضرني منهم إذا فارقته، لا تختلج في نفسي منازعة أحد من الخلق لي في شيء من الأمر في حياة النبي |، ولا بعد وفاتهثم أمر رسول الله | بتوجيه الجيش الذي وجهه مع أسامة بن زيد عند الذي أحدث الله به من المرض الذي توفاه فيه، فلم يدع النبي أحداً من أفناء العرب، ولا من الأوس والخزرج وغيرهم من سائر الناس، ممن يخاف على نقضه ومنازعته، ولا أحداً ممن يراني بعين البغضاء ممن قد وترته بقتل أبيه أو أخيه أو حميمه إلا وجهه في ذلك الجيش، ولا من المهاجرين والأنصار والمسلمين وغيرهم، والمؤلفة قلوبهم والمنافقين، لتصفو قلوب من يبقى معي بحضرته، ولئلا يقول قائل شيئاً مما أكرهه، ولا يدفعني دافع من الولاية والقيام بأمر رعيته من بعده.

ثم كان آخر ما تكلم به في شيء من أمر أمته أن يمضي جيش أسامة ولا يتخلف عنه أحد ممن أنهض معه، وتقدم في ذلك أشد التقدم، وأوعز فيه أبلغ الإيعاز، وأكد فيه أكثر التأكيد

فلم أشعر بعد أن قبض النبي | إلا برجال من بعث أسامة بن زيد وأهل عسكره قد تركوا مراكزهم، وأخلوا مواضعهم، وخالفوا أمر رسول الله | فيما أنهضهم له وأمرهم به، وتقدم إليهم من ملازمة أميرهم، والسير معه تحت لوائه، حتى ينفذ لوجهه الذي أنفذه إليه، فخلفوا أميرهم مقيماً في عسكره، وأقبلوا يتبادرون على الخيل ركضاً إلى حل عقدة عقدها الله عز وجل لي ولرسوله | في أعناقهم فحلوها، وعهد عاهدوا الله ورسوله فنكثوه.

وعقدوا لأنفسهم عقداً ضجت به أصواتهم واختصت به آراؤهم من غير مناظرة لأحد منا بني عبد المطلب، أو مشاركة في رأي أو استقالة لما في أعناقهم من بيعتي

فعلوا ذلك وأنا برسول الله | مشغول، وبتجهيزه عن سائر الأشياء مصدود، فإنه كان أهمها، وأحق ما بدئ به منها.

فكان هذا يا أخا اليهود أقرح ما ورد على قلبي مع الذي أنا فيه من عظيم الرزية، وفاجع المصيبة، وفقد من لا خلف منه إلا الله تبارك وتعالى

فصبرت عليها إذا أتت بعد أختها، على تقاربها وسرعة اتصالها.

ثم التفت× إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sai (as) ya ce ya kai bayahude, lallai manzon Allah (s.a.w) ya nada ni kan dukkanin al’ummarsa lokacin da yake raye ya kuma karbi muba’ya da dukkaninsu kan shugabancina ya kuma umarce su da wanda ya halarci taron karbar mubaya’ar ya sanar da wanda bai halarta ba, na kasance mai sauke wannan sako gare su daga manzon Allah (s.a.w) idan na halarta ma kuma kasance shugaba ga wanda ya halarce ni daga gare su idan na rabu da shi, jayayya wani mutum daga mutane gareni cikin wani daga wannan al’amari ba ta kutsa cikin raina ba lokacin rayuwar annabi (s.a.w) da bayan wafatinsa, sannan manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da dauko sojojin da ya yi tanadinsu tare da Usama bn Zaidu wanda cikin wannan al’amari Allah ya jarrabe shi da rashin lafiyar da ta kaishi da yin wafati, bai bar wani mutum daga `ya`yan larabawa daga wadanda yake jin tauye alkawarinsu da jayayya daga kabilun uwaisi da kazraj da wasunsu daga ragowar mutane, haka bai bar wani dukkanin wanda yake mini kallon kiyayya ba daga wadanda suke bina bashin jinin kisan iyayensu ko dan’uwansu ko masoyinsu face ya zuba su cikin wannan sojoji na rundunar Usamatu bn Zaidu, haka bai bar wani daga muhajirun da ansar ba da musulmi da wasunsu da munafukai da wadanda ake jawo zukatonsu face duk ya cusa su cikin wannan runduna da zata tafi yaki, domin zukatan wadanda suka wanzu tare dani a hallararsa tai dadi da tacewa, domin kada wani ya furta Kalmar da zata bakanta mini, kada wani mai tunkuda ya tunkude ni daga shugabanta da tsayuwa kan kiyaye al’amarinsa a bayansa, sannan karshen abin da ya yi magana cikin al’ummarsa shi ne rundunar Usamatu su tafi yaki kada kuma wani ya sake ya juya baya ga rundunanar Usamatu daga wadanda ya tura su tare, sannan ya tunkari batun  wannan runduna ta Usama da mafi tsananin tunkura ya karfafa tafiya wannan da mafi tsananin karfafawa. Bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) banga wasu mutane da suka ragu da rundunar Usamatu face wasu `yan tsiraru, wadanda aka sanya su cikin rundunar duk sun gudu sun juya baya sun sabawa umarnin manzon Allah cikin abin da ya tura su ya umarce su da shi da gabata zuwa gare su da lazimta wanda ya nada musu a wannan runduna da bin sawunsa da tafiya tare da shi karkashin tutarsa har sai ya zartar da fuskar da aka bashi umarni. amma sai suka sabawa Usamatu bn Zaidu da zaunawa cikin matsugunin rundanarsa, suka fuskanto suna sauri da gaggawa kan dawakai don su zo su warware igiyar Allah da manzonsa (s.a.w) da ya dora kan wuyayensu suka warwareta, haka alkawarin da suka daukarwa Allah da manzonsa shima suka saba masa, suka tafi suka kullawa kawukansu kulli, sautunka ya daga cikinsa ra’ayoyinsu suka kebantu  ciki ba tare da tuntubar wani guda daga cikinmu mu `ya`yan Abdul-mudallib, ko kuma tarayya cikin ra’ayi da zobaita daga abin da ke rataye cikin wuyayensu na mubaya’ata.

Suka aikata abinda suka aikata alhalin ni na shagaltu da shirya jana’izar manzon Allah (s.a.w) nayi watsi da duk wani abu koma bayan hakan, lallai hakan ya kasance mafi muhimmacinta, kuma mafi cancanta daga abin da aka fara da shi daga gareta hakan ya kasance mafi kunan da zafin abin da ya gangara cikin zuciyata ya dan’uwa bayahude tare da al’amarin da nake ciki daga girman bakin ciki da takaici da musiba akan rashin wanda babu mai maye gurbinsa face Allah matsarkaki

Sai na yi hakuri kan wannan jarrabawa lokacin da ta zo bayan `yar’uwarta data gushe, kan kusantarta da saurin sadarwarta

Sannan ya waiwayi sahabbansa ya ce: shin ba haka bane

Suka ce: haka ne ya sarkin muminai

فقال×: وأما الثالثة يا أخا اليهود، فإن القائم بعد النبي | كان يلقاني معتذراً في كل أيامه، ويلوم غيره([1]) ما ارتكبه من أخذ حقي، ونقض بيعتي وسألني تحليله.

فكنت أقول: تنقضي أيامه، ثم يرجع إلي حقي الذي جعله الله لي عفواً هنيئاً من غير أن أحدث في الإسلام مع حدوثه وقرب عهده بالجاهلية حدثاً في طلب حقي بمنازعة، لعل فلاناً يقول فيها: نعم، وفلاناً يقول: لا، فيؤول ذلك من القول إلى الفعل

sai ya ce: amma ta uku ya kai dan’uwa bayahude: lallai mai wanda ya hau karagar mulki bayan annabi (s.a.w) ya kasance yana haduwa da ni yana mai neman uzuri cikin dukkanin kwanakinsa yana mai zargin waninsa kan abin da ya aikata kan kwace hakkina da warware mubaya’ata ya tambaye ni warwareta na kasance ina cewa: kwanakinsa zasu kare, sannan hakkina wanda Allah ya sanya shi gare ni hani’an ba tare na kirkiri wata bidi’a cikin muslunci ba da kusancin zamanin muslunci da jahiliya cikin nemansa da jayayya ba da sannu zai dawo gare ni, me yiwuwa wani ya ce: na’am, wani kuma ya ce: a’a sai ya juyar da haka daga magana zuwa aiki    

وجماعة من خواص أصحاب محمد | أعرفهم بالنصح لله، ولرسوله، ولكتابه، ودينه الإسلام، يأتوني عوداً وبدءاً، وعلانية وسراً، فيدعوني إلى أخذ حقي، ويبذلون أنفسهم في نصرتي، ليؤدوا إلي بذلك بيعتي في أعناقهم، فأقول: رويداً وصبراً، لعل الله يأتيني بذلك عفواً بلا منازعة، ولا إراقة الدماء، فقد ارتاب كثير من الناس بعد وفاة النبي |، وطمع في الأمر بعده من ليس له بأهل، فقال كل قوم: منا أمير.

وما طمع القائلون في ذلك إلا لتناول غيري الأمرفلما دنت وفاة القائم، وانقضت أيامه صير الأمر بعده لصاحبه، فكانت هذه أخت أختها، ومحلها مني مثل محلها، وأخذا مني ما جعله الله لي.

فاجتمع إليَّ من أصحاب محمد | ممن مضى وممن بقي، ممن أخره الله من اجتمع، فقالوا لي فيها مثل الذي قالوا في أختها، فلم يَعْدُ قولي الثاني قولي الأول صبراً واحتساباً، ويقيناً وإشفاقاً من أن تفنى عصبة تألفهم رسول الله | باللين مرة، وبالشدة أخرى، وبالنُّذُرِ مرة، وبالسيف أخرى، حتى لقد كان من تألفه لهم أن كان الناس في الكر والفرار، والشبع والري، واللباس والوطاء والدثار، ونحن أهل بيت محمد | لا سقوف لبيوتنا، ولا أبواب ولا ستور إلا الجرائد، وما أشبهها، ولا وطاء لنا ولا دثار علينا، يتداول الثوب الواحد في الصلاة أكثرنا، ونطوي الليالي والأيام عامتنا، وربما أتانا الشيء مما أفاءه الله علينا، وصيره لنا خاصة دون غيرنا، ونحن على ما وصفت من حالنا، فيؤثر به رسول الله | أرباب النعم والأموال تألفاً منه لهم

da wasu jama’a daga kebanbtattun sahabban manzon Allah (s.a.w) wanda na sansu da yin nasiha don Allah da manzonsa  don littafin Allah da addinin muslunci, suna zuwa wurina a boye da bayyane a fari da dawowa, sai suka dinga kirana zuwa ga in zo, in karbi hakkina, suna kuma sadaukar da rayukansu cikin taimakona, domin ta hakan su samu damar sauke mubaya’ata da take wuyayansu, sai ince a saurara a jinkirta ayi hakuri. Tsammani Allah zai bani hakan cikin ruwan sanyi ba tare da jayayya ba, ba tare da zubar da jini ba, hakika da yawan mutane sunyi kokwanto bayan wafatin annabi (s.a.w) wanda ba ahlin wannan al’amari na jagorancin al’umma ba yayi kwadayi cikinsa. Kowacce kabila ta ce dole daga cikinmu shugaba zai kasance. Masu wadannan basu kalamai basu basu da wani kwadayi da ya wuce ace wanina ne ya wayi gari shugaban al’umma, yayin da wafatin wanda ya `dare karagar mulki bayan annabi ya kusanto kwanakinsa suka kare sai ya mika shugabanci ga abokinsa, wannan ta kasance `yar’uwar `yar’uwarta, mahallinta daga gareni misalin muhallinta. Ya kwace mini hakkin da Allah ya sanya shi gare ni, sai wasu daga sahabban muhammadu (s.a.w) daga wadanda suka gabata da wadanda suka wanzu suka taru zuwa gare ni, daga wadanda Allah ya jinkirta su daga wadanda suka taru, sai suka ce mini ina da hakki ciki wannan ala’amri misalin misalin abin da suka fadi kan wancan `yar’uwarta ta, sai dai na kara gaya musu irin abin da na gaya musu tun farko cewa ayi dai hakuri a daure, tatr da yakini da kuma tsoran kada tattara su da jawo su da manzon Allah (s.a.w) yayi wani lokaci da tausasawa ya watse. Wani lokacin kuma da tsanantawa, wani karon kuma da gargadi, wani loakcin kuma da takobi, kai hatta ya kasance daga hado su da yayi mutane sun kasance cikin farmaki da rantar ta kare da arcewa, da koshi da sha a koshi, da tufafi malullufi. Sai dai cewa mu Ahlin gidan Muhammadu (s.a.w) babu rufi a gidajenmu babu kofa, babu labule face itacen dabino da abin da yayi kama da shi, babu da tufafi babu da malullufi, yawancinmu suna kai kawo cikin sallah da tufafi guda daya rak, yawancin na kwana cikin yunwa, sau da yawan lokaci wani abu daga dukiyar da Allah ya kebance mu da ita kan zuwar mana cikin wannan hali na da nayi bayaninsa amma sai manzon Allah (s.a.w) ya fifita wasunmu da ita daga ma’botan ni’ima da dukiya dom ya hado kansu zuwa ga muslunci

فكنت أحق من لم يفرق هذه العصبة التي ألفها رسول الله |، ولم يحملها على الخطة التي لا خلاص لها منها دون بلوغها أو فناء آجالها، لأني لو نصبت نفسي فدعوتهم إلى نصرتي كانوا مني وفي أمري على إحدى منزلتين إما متبع مقاتل، وإما مقتول إن لم يتبع الجميع، وإما خاذل يكفر بخذلانه إن قصر في نصرتي أو أمسك عن طاعتي.

وقد علم الله أني منه بمنزلة هارون من موسى، يحل به في مخالفتي، والامساك عن نصرتي ما أحل قوم موسى بأنفسهم في مخالفة هارون وترك طاعته.

ورأيت تجرع الغصص، ورد أنفاس الصعداء، ولزوم الصبر حتى يفتح الله، أو يقضى بما أحب، أزيد لي في حظي، وأرفق بالعصابة التي وصفت أمرهم ﴿وَكَانَ أَمْرُ اللهِ قَدَراً مَقْدُوراً﴾([2]).

Na kasance mafi cancantuwa daga wanda zai kiyaye hada kan wannan jama’a wacce manzon Allah (s.a.w) ya hado kansu ya jawo ya tara su bai dora su kan layin da babu tsira daga cikinsa ba tare da isar musu ba ko karewar ajali, domin cewa lallai ni da na nada kaina na kira su zuwa ga taimakona da suna kasance daga gare ni ko dai mai biyayya ko mai kisa, ko kuma kasasshe idan yaki bin abin da akasari mutane suka zaba, ko kuma mai noke daga ba da taimako da kunyatawa da zai kafirta da ja bayansa idan ya takaita cikin taimakona ko yaki yarda yayi mini biyayya, hakika Allah ya san cewa lallai ni ina matsayin da Haruna yake da shi daga Musa, abin da ya sauka kan wadanda suka juyawa Haruna baya suka kame ga barin taimakonsa zai sauka kan wadanda suka juya mini baya suka ki taimakona. Sai na zabi shan takaici da danne zuciya da rungumar hakuri har sai Allah ya kawio budi, ko kuma yayi hukunci da abin da yake so shio yafi karuwa cikin rabona kuma shi yafi zama sauki ga jama’ar da na siffanta al’amarinsu.

Al’amarin Allah ya kasance kan mikdari kaddararre

ولو لم أتق هذه الحالة ـ يا أخا اليهود ـ ثم طلبت حقي لكنت أولى ممن طلبه، لعلم من مضى من أصحاب رسول الله |، ومن بحضرتك منه بأني كنت أكثر عدداً، وأعز عشيرة، وأمنع رجالاً، وأطوع أمراً، وأوضح حجة، وأكثر في هذا الدين مناقب وآثاراً لسوابقي، وقرابتي، ووراثتي، فضلاً عن استحقاقي ذلك بالوصية التي لا مخرج للعباد منها، والبيعة المتقدمة في أعناقهم ممن تناولها.

Ba da ban na yi jin wannan hali ba ya kai dan’uwa bayahude-sannan na nemi hakkina da na kasance mafi cancanta vda neman hakkina, sakamkon sanin wadanda suka tafi daga sahabban manzon Allah (s.a.w) da kuma wadanda suke hallararka da cewa lallai ni ne mafi yawan adadi mafi `daukaka a dangi. Mafi karfafar mazaje, mafi samun da`a cikin umarni, mafi bayyanar hujja, kuma ni ne wanda yafi kowa falaloli da kufaifayin sakamakon kyawawan halaye na da suka gabata, da kusanci na, da gado na, ballantana ma cancantata ta hanyar wasiyya da babu matserata ga al’umma daga gareta, da mubaya’a da ta gabata wacce take kan wuyayensu

وقد قبض محمد | وإن ولاية الأمة في يده وفي بيته، لا في يد الأولى تناولوها، ولا في بيوتهم. ولأهل بيته الذين أذهب الله عنهم الرجس وطهرهم تطهيراً أولى بالأمر من بعده من غيرهم في جميع الخصال.

ثم التفت× إلى أصحابه فقال: أليس كذلك؟!

فقالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Hakika Muhammadu (s.a.w) ya bar duniya lallai shugabantar al’umma na hannunsa tana kuma cikin gidansa ba ta cikin hannuna wadanda suka karbeta da farko ba kuma ta cikin gidansu, kadai dai tana cikin gidan Ahlil-baiti wadanda Allah ya tafiyar musu da datti ya tsarkake su tsarkakewa sune mafi cancantar shugabanci bayan manzon Allah (s.a.w) daga wadanda ba su ba cikin dukkanin dabi’u.

Sannan ya waiwayi sahabbansa ya ce: shin ba haka bane?

Suka ce: haka ne ya sarkin muminai

فقال×: وأما الرابعة يا أخا اليهود، فإن القائم بعد صاحبه كان يشاورني في موارد الأمور، فيصدرها عن أمري، ويناظرني في غوامضها فيمضيها عن رأيي، لا أعلم أحداً ولا يعلمه أصحابي يناظره في ذلك غيري، ولا يطمع في الأمر بعده سواي.

فلما (أن) أتته منيته على فجأة بلا مرض كان قبله، ولا أمر كان أمضاه في صحة من بدنه لم أشك أني قد استرجعت حقي في عافية بالمنزلة التي كنت أطلبها، والعاقبة التي كنت ألتمسها، وأن الله سيأتي بذلك على أحسن ما رجوت، وأفضل ما أملت

Sannan ya ce: amma ta hudu ya kai dan’uwan bayahude, hakika wanda ya `dare karagar mulki bayan annabi bayan abokinsa ya kasance yana shawarta ta cikin magangaru al’amura, sai ya fitar da su daga umarni. Yana neman ra’ayi na cikin masu wahalarsu sai ya zartar da su daga ra’ayi na, ban sani ba haka sahabbaina basu san wani mutum da yake neman jin ra’ayinsa ba banda ni, bai yin kwadayin neman ra’ayin wani face ni.

Lokacin da mutuwa da zakke masa ta zo masa ba tare da wata cuta da ya kasance ya gabata da ita gabanin mutuwar, ba tare da wani al’amari da ya zartar kan ingancin lafiyar jikinsa ba. bana kokwanto kan cewa ni tuni na dawo da hakkina cikin ruwan sanyi gwargwadon matsayin da na kasance ina nemansa da karshen da na kasance ina buri, da cewa lallai da sannu Allah zai zo da hakan da mafi kyawun dana kasance ina fata , da mafi fifita yadda na nayi burinsa   

وكان من فعله: أن ختم أمره بأن سمى قوماً أنا سادسهم، ولم يستوني بواحد منهم، ولا ذكر لي حالاً في وراثة الرسول، ولا قرابة، ولا صهر، ولا نسب، ولا لواحد منهم مثل سابقة من سوابقي، ولا أثر من آثاري.

وصيرها شورى بيننا، وصير ابنه فيها حاكماً علينا، وأمره أن يضرب أعناق النفر الستة الذين صير الأمر فيهم إن لم ينفذوا أمره

ya kasance wanda ya aikata haka, Allah ya kawo karshen ala’amarinsa ta yadda ya zabi mutane biyar wanda ni ne cikon na shidansu bai daidaita da daya daga cikinsu ba, bai ambaci wani hali daga gadom annabi bako makusantansa, ko surukutaka ko dangantaka, sannan babu wani cikin mutum biyar din da yake da falalar da nake da ita, babu wanda yake da kufaifayin da nake da su, sai ya mai da ala’amarin shawara tsakaninmu, ya sanya dansa shugaba cikin ala’amrin kanmu, ya kuma umarce shi da ya sarai kawukan mutane shida idan basu zartar da abin da ya umarta ba

وكفى بالصبر على هذا ـ يا أخا اليهود ـ صبراً، فمكث القوم أيامهم كلها كل يخطب لنفسه، وأنا ممسك عن أن سألوني عن أمري، فناظرتهم في أيامي وأيامهم، وآثاري وآثارهم، وأوضحت لهم ما لم يجهلوه من وجوه استحقاقي لها دونهم، وذكرتهم عهد رسول الله | إليهم، وتأكيد ما أكده من البيعة لي في أعناقهم، دعاهم حب الإمارة، وبسط الأيدي والألسن في الأمر والنهي، والركون إلى الدنيا، والاقتداء بالماضين قبلهم إلى تناول ما لم يجعل الله لهم.

فإذا خلوت بالواحد ذكرته أيام الله، وحذرته ما هو قادم عليه وصائر إليه، التمس مني شرطاً أن أصيرها له بعدي، فلما لم يجدوا عندي إلا المحجة البيضاء، والحمل على كتاب الله عز وجل ووصية الرسول، وإعطاء كل امرئ منهم ما جعله الله له، ومنعه ما لم يجعل الله له، أزالها عني إلى ابن عفان طمعاً في الشحيح معه فيها

Ya kai da’uwa bayahude hakuri ya kai hakuri kan wannan, sai mutane suka zauna kwanakinsu kowannensu na nemarwa kansa, ni kuma na kauda kai har zuwa lokacin da suka tambaye ni game da al’amarina, sai nayi musayen ra’ayin da su cikin kwanakina da kwanakinsu, da kufaifayina da kufaifayinsu nayi musu Karin bayani kan abin da basu jahilta ba daga fusaken cancantata ga wannan al’amarin na shugabanci koma bayan wani na, na tunatar da su alkawarin manzon Allah (s.a.w) da yake kansu don karfafa abin da ya karfafa kan mubaya’ata da take wuyayansu wacce son duniya da shugabanci da son shinfida hannuwa da harshe cikin umarni da hani da karkata zuwa ga son duniya da koyi da wadanda suka gabace su ya kai su ga neman abin da Allah bai basu ba, idan na kebanta da daya daga cikinsu na tunatar da shi kwanakin Allah na gargade kan abin da yake kokarin gabata kansa da karkata zuwa gare shi, sai ya nemi sanya mini sharadin cewa zan mika al’amari a a bayana zuwa gare shi, yayinda suka gaza samun wani abu gareni face hanyar shiriya da dora su kan littafin Allah da wasiyyar manzon Allah (s.a.w) da baiwar kowanne dayansu iya abin da Allah ya bashi da hanashi abin da Allah bai sanya gare shi ba sai yak i sallama al’amarin shugabancin gare ni ya mika shi ga bn affan bisa kwadayin da yake da shi cikinsa daga gare shi

وابن عفان رجل لم يستوبه (؟) وبواحد ممن حضره حال قط فضلاً عمن دونهم، لا ببدر التي هي سنام فخرهم، ولا غيرها من المآثر التي أكرم الله بها رسوله ومن اختصه معه من أهل بيته×.

ثم لم أعلم القوم أمسوا من يومهم ذلك حتى ظهرت ندامتهم، ونكصوا على أعقابهم، وأحال بعضهم على بعض، كل يلوم نفسه ويلوم أصحابه

sannan shi bn affanu mutum ne bai daidaita halin shi ba da daya daga cikin mutane da suka hallara ballantana daga wadanda suke koma bayansu, bai daidiata da badar wacce ita kololuwar alfaharinsu ba, haka ga wanin badar daga kufaifayin da Allah ya karrama manzonsa da wanda ya kebance shi tare da shi daga Ahlin gidansa, sannan ban san wasu mutane da suka yammatu daga yininsu da basu yi nadama, sashensu ya koma yana zargin sashe, kowannensu yana zargin kansa yana kuma zargin abokansa

ثم لم تطل الأيام بالمستبد بالأمر ابن عفان حتى أكفروه، وتبرؤوا منه، ومشى إلى أصحابه خاصة، وسائر أصحاب رسول الله | عامة يستقيلهم من بيعته، ويتوب إلى الله من فلتته.

فكانت هذه ـ يا أخا اليهود ـ أكبر من أختها وأفظع، وأحرى أن لا يصبر عليها، فنالني منها الذي لا يبلغ وصفه، ولا يحد وقته، ولم يكن عندي فيها إلا الصبر على ما أمض وأبلغ منها

Sannan kwanaki ba suyi tsayi ba da wadanda suka nada bn affanu har sai da takai ga sun dawo suna kafirta shi suna barranta daga gare shi, ya tafi zuwa ga sahabbansa a kebance, sannan sauran baki dayan sahabban manzon Allah (s.a.w) ya dinga kwabe su daga mubaya’arsa ya tuba ga Allah daga ba zatonta.

Wannan ta kasance mafi girma daga `yar’uwarta mafi munana ya kai dan’uwa bayahude, dayar kuma ba a iya hakuri kanta sai abin da da ba a iya siffanta shi ba a kuma iya iyaknce lokacinsa ya zakke mini daga gare ta, sai nayi hakuri kan abin da nake fuskanta cikinta da abin da nake riska daga gareta

ولقد أتاني الباقون من الستة من يومهم، كل راجع عما كان ركب مني، يسألني خلع ابن عفان، والوثوب عليه، وأخذ حقي. ويؤتيني صفقته وبيعته على الموت تحت رايتي، أو يرد الله عز وجل عليَّ حقي، فوالله ـ يا أخا اليهود ـ ما منعني منها إلا الذي منعني من أختيها قبلها، ورأيت الابقاء على من بقي من الطائفة أبهج لي، وآنس لقلبي من فنائها، وعلمت أني إن حملتها على دعوة الموت ركبته.

فأما نفسي فقد علم من حضر ممن ترى ومن غاب من أصحاب محمد | أن الموت عندي بمنزلة الشربة الباردة في اليوم الشديد الحر من ذي العطش الصدى

Hakika ragowar mutane daga shidan sun zo wajena a wannan rana, kowannensu ya nadama daga abin da ya aikata kan hakkina, yana kuma rookna kwabe bn affanu da kai masa hari da kwato hakkina, kowannensu ya mika mini mubaya’arsa da yarjejeniyarsa kan mutuwa karkashin umarnina da cewa zai wanzu har sai dai idan Allah ya dawo mini da hakkina , wallahi ya kai dan’uwa bayahude babu abin da ya hana ni daga gareta face dai abin da ya hana ni daga `yar’uwarta gabaninta, sai na zabi wanzuwa kan wanda ya wanzu daga kungiya shi ne yafi faranta gare ni shi kuma yafi nustuwa ga zuciyata daga bushewarta, na san cewa lallai ni idan na karbe ta kan da’awar mutuwa to na zakke mata. Amma raina hakika wadanda suka hallara anan da wadanda suka gabata daga sahabban Muhammadu (s.a.w) sun san cewa lallai mutuwa a wajena daidai take da shan ruwan sanyi cikin ranar da ake tsala zafi ga ma’abocin matsananciyar kishirwa

ولقد كنت عاهدت الله عز وجل ورسوله | أنا وعمي حمزة وأخي جعفر، وابن عمي عبيدة على أمر وفينا به لله عز وجل ولرسوله، فتقدمني أصحابي وتخلفت بعدهم لما أراد الله عز وجل، فأنزل الله فينا ﴿مِنَ الْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا مَا عَاهَدُوا اللهَ عَلَيْهِ فَمِنْهُمْ مَنْ قَضَى نَحْبَهُ وَمِنْهُمْ مَنْ يَنْتَظِرُ وَمَا بَدَّلُوا تَبْدِيلاً﴾([3]) حمزة وجعفر وعبيدة، وأنا والله المنتظر ـ يا أخ اليهود ـ وما بدلت تبديلاً

Hakika ni da baffana Hamza da `dan’uwana Jafar da `dan baffana ubaida mun riga mun daukarwa Allah mai girma da `daukaka da manzonsa (s.a.w) alkawari kan ala’amari cikinmu sai suka gabace ni sai na wanzu bayansu sakamkon abin da Allah mai girma da `daukaka ya nufa, sai Allah ya saukar wannan ayar kanmu (daga mazaje akwai da suka gasgata abin da sukaiwa Allah alkawari kai daga cikinsu akwai wanda ya biya bukatarsa sannan akwai wanda ke jira basu musanya ba musanyawa) sune Hamza d Jafar da Ubaida, ni wallahi ina tsimayi da jira ya kai da’uwa bayahude ban musanya ba musanyawa.

وما سكّتني عن ابن عفان، وحثّني على الامساك عنه إلا أني عرفت من أخلاقه فيما اختبرت منه بما لن يدعه حتى يستدعي الأباعد إلى قتله وخلعه، فضلا عن الأقارب وأنا في عزلة.

فصبرت حتى كان ذلك، لم أنطق فيه بحرف من «لا»، ولا «نعم

Babu abin da ya sanya yin shiru daga barin bn affanu da kwadaitar dani da kamewa daga barinsa face cewa lallai ni na sani daga dabi’unsa daga abin da na jarraba shi daga gareshi daga dabi’ar da bazai bari har sai ta kai ga sanya mutanen nesa sun kashe shi da kwabe shi daga shugabanci, ballantana na kusa-kusa, ni ina cikin nesata sai nayi hakuri har sai da hakan ta kasance ban furta harafi daya cikinsa daga fadin a’a ko na’am 

ثم أتاني القوم وأنا ـ عَلِمَ الله ـ كاره لمعرفتي بما تطاعموا به من اعتقال الأموال والمرح في الأرض، وعلمهم بأن تلك ليست لهم عندي، وشديد عادة منتزعة، فلما لم يجدوا عندي تعللوا الأعاليل.

ثم التفت× إلى أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

فقالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sannan mutane suka zo wajena alhalin ni Allah ya sani cewa ina kyama bisa sani na da abin da suka ciyar da junansu da su daga tsare dukiya da cin duniyarsu da tsinke, tare da saninsu cewa ba zasu samu haka waje na ba, da tsananin al’ada fizagagga, yayin da suka ga ba zasu samu bukatarsu ba wajena sai suka fake da uzurai!

. والوصي عليها، فحملوها على الجمل وشدوها على الرحال، وأقبلوا بها تخبط الفيافي، وتقطع البراري، وتنبح عليها كلاب الحوأب، وتظهر لهم علامات الندم في كل ساعة وعند كل حال، في عصبة قد بايعوني ثانية بعد بيعتهم الأولى في حياة النبي |، حتى أتت أهل بلدة قصيرة أيديهم، طويلة لحاهم، قليلة عقولهم، عازبة آراؤهم، وهم جيران بدو، ورواد بحر، فأخرجتهم يخبطون بسيوفهم من غير علم، ويرمون بسهامهم بغير فهم.

فوقفت من أمرهم على اثنتين، كلتاهما في محلة المكروه ممن إن كففت لم يرجع ولم يعقل، وإن أقمت كنت قد صرت إلى التي كرهت

Ni ne wanda akaiwa wasicci kanta, sai suka dora wannan mata a kan rakumi suka daura damara kan tafiya, suka fuskanto da ita tana fagarniya cikin jeji, tana keta garuruwa, sannan karnukan hau’abu na mata haushi, sannan alamomin nadama na ta bayyana kansu cikin kowanne hali, cikin wasu jama’a da sukai mini mubaya’a karo na biyu bayan mubaya’arsu ta farko cikin rayuwar annabi (s.a.w) har sai da wannan mata ta jewa wajen mutanen wannan gari da hannayensu ke gajejjeru gemukansu masu tsayi, hankulansu kanana,masu raunin ra’ayi, kauyawa, sai na tsinkayi abubuwa daga al’amarinsu, dukkanin biyun suna cikin muhallin da ba a so daga wadanda idan na kame ga barinsu basu dawo su hankalta, idan kuma na mikar zan kasantu cikin abin da na ke gudu

فقدمت الحجة بالأعذار والانذار، ودعوت المرأة إلى الرجوع إلى بيتها، والقوم الذين حملوها على الوفاء ببيعتهم لي، والترك لنقضهم عهد الله عز وجل فيَّ، وأعطيتهم من نفسي كل الذي قدرت عليه، وناظرت بعضهم فرجع، وذكّرت فذكر

ثم أقبلت على الناس بمثل ذلك فلم يزدادوا إلا جهلاً، وتمادياً وغيافلما أبوا إلا هي، ركبتها منهم فكانت عليهم الدبرة، وبهم الهزيمة، ولهم الحسرة، وفيهم الفناء والقتل، وحملت نفسي على التي لم أجد منها بداً، ولم يسعني إذ فعلت ذلك وأظهرته آخراً مثل الذي وسعني منه أولاً من الاغضاء والامساك، ورأيتني إن أمسكت كنت معيناً لهم علي بإمساكي على ما صاروا إليه، وطمعوا فيه من تناول الأطراف، وسفك الدماء وقتل الرعية، وتحكيم النساء النواقص العقول والحظوظ على كل حال، كعادة بنى الأصفر ومن مضى من ملوك سبأ والأمم الخالية، فأصير إلى ما كرهت أولاً وآخراً، وقد أهملت المرأة وجندها يفعلون ما وصفت بين الفريقين من الناس، ولم أهجم على الامر إلا بعدما قدمت وأخرت، وتأنيت وراجعت، وأرسلت وسافرت [وشافهت]، وأعذرت، وأنذرت، وأعطيت القوم كل شيء يلتمسوه بعد أن عرضت عليهم كل شيء لم يلتمسوه.

فلما أبوا إلا تلك، أقدمت عليها، فبلغ الله بي وبهم ما أراد، وكان لي عليهم بما كان مني إليهم شهيداً.

ثم التفت× إلى أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنينً.

Sai na gabatar da hujja da uzurai da gargadi na kira kuma wannan mata da ta koma gidanta sannan suka mutane da suka zuga ta fitowa yakata na kira su da cika alkawarin da suka dauka na mubaya’ata na kuma kira su da suyi watsi da tauye akawarin Allah mai girma da `daukaka cikin al’amarina, na sadaukar musu daga gare ni dukkanin abin da nake da iko a kansa, na tattauna da wasu ba’arinsu suka janye, na tunatar dasu suka tuna, sannan na fuskanto mutane da misalin irin wannan amma babu abin da ya kara musu face jahilci da tsaurin kai da bata, yayin da suka kafe sai dai yaki sai na hau yakin sai yakin ya zame musu hasara da faduwa da mutuwa da halaka, na dora kaina kan abin da babu makawa sai shi, sannan bai yalwace ni sa’ilin dana aikata haka na bayyanar da shi a karshe misalin yadda ya yalwace ni daga gare shi da farko daga kau dai kai da rintse idaniya  da kamewa, sai na samu kaina cikin halin da idan na kamewa zan kasance mai taimaka musu kan gamawa dani ta hanyar kamewa ta kan abin da suka nufa sukai kwadayi cikinsa daga neman geffa, da zubar da jini da kashe mutane, da hakimtar da mata masu tawayar kwakwale da rabo kan kowanne hali, kamar yadda al’adar `ya`yan ruwan dorawa take daga wadanda suka gabata daga sarakunan saba’i da al:ummun da suka shude, sai in kasantu cikin abin da na kyamata da farko da karshe, hakika na kyale mace da rundunarta su aikata abin da na siffanta tsakanin bangarori biyu  daga mutane, ban kai farmaki har sai bayan da na gabatar na jinkirta na matukar jinkiri na bibiya na aika sako na tattauna baki da baki da su na kafa uzuri na yi gargadi, na baiwa wadannan mutane dukkanin abin da suka bukata bayan na bijiro musu da dukkanin abin da ma basu nema ba, yayin da suka ki suka kafe sai dai yaki, sai na gabata kan yakin, sai Allah ya tabbatar da abin da ya nufa da ni da su, sai ya kasantu gareni kansu da abin da ya kasantu daga gareni zuwa gare su shahidi.

فقال×: وأما السادسة يا أخا اليهود فتحكيمهم [الحكمين]، ومحاربة ابن آكلة الأكباد، وهو طليق، معاند لله عز وجل، ولرسوله والمؤمنين منذ بعث الله محمداً إلى أن فتح الله عليه مكة عنوة.

فأخذت بيعته وبيعة أبيه لي معه في ذلك اليوم، وفي ثلاثة مواطن بعده، وأبوه بالأمس أول من سلم علي بإمرة المؤمنين، وجعل يحثني على النهوض في أخذ حقي من الماضين قبلي، ويجدد لي بيعته كلما أتاني.

وأعجب العجب أنه لما رأى ربي تبارك وتعالى قد رد إلي حقي وأقره في معدنه، وانقطع طمعه أن يصير في دين الله رابعاً، وفي أمانة حملناها حاكماً، كر على العاصي بن العاص فاستماله، فمال إليه، ثم أقبل به بعد أن أطعمه مصر، وحرام عليه أن يأخذ من الفيء دون قسمه درهماً، وحرام على الراعي إيصال درهم إليه فوق حقه، فأقبل يخبط البلاد بالظلم ويطأها بالغشم، فمن بايعه أرضاه، ومن خالفه ناواه

Sai (as) ya ce: amma ta shida ya kai da’uwa bayahude shi ne hukuncinsu da hukunci guda biyu, yakar `dan mai tauna hanta wanda shi sakakke ne mai yiwa Allah mai girma da `daukaka da manzonsa da muminai tsaurin kai tun lokacin da aka aiko Muhammad har zuwa bude garin makka ba tare da yaki ba.

Sai karbi mubaya’arsa data babansa a cikin wannan rana. Hakama  a wurare uku bayan fatahu makka, babansa a jiya shi ne farkon wanda ya fara sallama mini shugabancin muminai, ya kuma kasance yana zuga da in tashi in kwaci hakkina daga wadanda suka gabace ni kansa gabanina, duk sa’ailin da yazo wurina ya kan jaddada mubaya’arsa a gareni, abu mafi ban mamaki shine lokacin da ya ga ubangiji ya dawo mini da hakkina ya kuma tabbatar da shi a muhallinsa, sannan da yaga burinsa cikin addinin Allah na ganin ya zama mutum na hudu daga halifofi ya yanke, cikin amanar da muka dora mata shugaba, sai ya riabci asi bn asi ya jawo hankalinsa zuwa gare shi sai ko shi din ya karkata gare shi, sannan ya fuskanto da shi bayan da ya ciyar da shi mulkin misra ya kuma haramta masa diban dirhami daga ganima koma bayan kasonsa,haramun ne ga mai kiwo sadar da dirhami zuwa gare shi sama da hakkinsa, sai ya fuskanto yana fagarniya yana kasashe da zalunci yana takasu da danniya, duk wanda yayi masa mubaya’a sai ya yardarm da shi duk kuma wanda ya `saba masa sai ya nisanta shi  

ثم توجه إلي ناكثاً علينا مغيراً في البلاد شرقاً وغرباً، ويميناً وشمالاً، والأنباء تأتيني والأخبار ترد علي بذلك.

فأتاني أعور ثقيف، فأشار علي أن أوليه البلاد التي هو بها، لأداريه بما أوليه منها.

وفي الذي أشار به الرأي في أمر الدنيا لو وجدت عند الله عز وجل في توليته لي مخرجاً، وأصبت لنفسي في ذلك عذراً، فأعملت الرأي في ذلك، وشاورت من أثق بنصيحته لله عز وجل ولرسوله | ولي وللمؤمنين، فكان رأيه في ابن آكلة الأكباد كرأيي، ينهاني عن توليته، ويحذرني أن أدخل في أمر المسلمين يده، ولم يكن الله ليراني أتخذ المضلين عضداً.

Sannan ya fuskanto gareni yana tauye mubaya’a kanmu yana canjawa cikin kasashe gabas da yamma, hagu da dama , labarii suna zuwar mini kan wannan aiki nasa, sai mai ido daya ya zo wurina yana son in bar masa mulkin garin da yake ciki, in bishi a hankali cikin abin da zan nada shi kai daga gareta cikin abin da yayi ishara zuwa gare shi cikin al’amarin duniya, da ace na samu mafita cikin abin da yake son in nada shi da ace zan iya samarwa kaina uzuri kan hakan, sai na bayyanar da ra’ayi cikin ala’amarin nayi shawara da wanda na yarda da nasiharsa don Allah da manzonsa don muminai, sai ya zama ra’ayinsa kan `dan mai tauna hanta irin ra’ayi na ya kasance yana hana ni nada `dan mai tauna hanta, ya kuma gargade ni da kada in sake in shigar da hannunsa cikin al’amarin musulmai.

Sannan Allah bai kasance yana gani na ba ina rikar batattu mataimaka ba.

فوجهت إليه أخا بجيلة مرة، وأخا الأشعريين مرة، كلاهما ركن إلى الدنيا وتابع هواه فيما أرضاه.

فلما لم أره يزداد فيما انتهك من محارم الله إلا تماديا شاورت من معي من أصحاب محمد | البدريين والذين ارتضى الله عز وجل أمرهم، ورضي عنهم بعد بيعتهم، وغيرهم من صلحاء المسلمين والتابعين، فكل يوافق رأيه رأيي في غزوه ومحاربته، ومنعه مما نالت يده، وإني نهضت إليه بأصحابي، أنفذ إليه من كل موضع كتبي، وأوجه إليه رسلي، أدعوه إلى الرجوع عما هو فيه، والدخول فيما فيه الناس معيفكتب يتحكم علي، ويتمنى علي الأماني، ويشترط علي شروطاً لا يرضاها الله عز وجل ورسوله ولا المسلمون، ويشترط في بعضها: أن أدفع إليه أقواماً من أصحاب محمد | أبراراً، فيهم عمار بن ياسر، وأين مثل عمار؟! والله لقد رأيتنا مع النبي | وما يعد منا خمسة إلا كان سادسهم، ولا أربعة إلا كان خامسهم ـ اشترط دفعهم إليه ـ ليقتلهم ويصلبهم، وانتحل دم عثمان، ولعمرو الله ما ألب على عثمان ولا جمع الناس على قتله إلا هو وأشباهه من أهل بيته أغصان الشجرة الملعونة في القرآن

Sai na fuskantar masa da `dan’uwan bajila a karo farko, a wani karon kuma `da’uwan ash’arawa, dukkanin biyun sun karkatu zuwa ga duniya kowanne ya biye ma son zuciyarsa cikin abin da yake yarda, ba same shi yana karuwa da komai cikin abin da yake keta alfarmarsa ba face kara tsaurin kai, na shawarci abokaina daga mutanen da suka je yakin badar wadanda Allah ya yarda da su suka yarda da shi hakama nayi shawara da salihan musulmai da tabi’ai sai na samu dukkaninsu ra’ayinsu ya dace da ra’ayina kan yakarsa da kuma hana shi abin da hannunsa take nema. Lallai ni na mike na fuskance tare da sahabbaina ina zartar da rubutuna zuwa gare shi a kowanne muhalli. Ina aika masa `yan sakona ya zuwa gare shi, ina kiransa zuwa ga janyewa daga abin da yake kai da kuma shigowa cikin abin da mutane ke ciki tare da ni, sai ya aiko da amsar wasika gareni yana hakimta kaina, yana kuma fatan wasu burace-burace kaina, yana kuma sanya mini sharudda wadamda Allah mai girma da `daukaka da manzonsa da musulmai basu yarda, cikin wasu ba’ari yana shardanta cewa in mika masa wasu mutane daga rabautattun sahabban Muhammad (s.a.w) cikinsu akwai Ammar bn Yasir, ina Ammar? wallahi na ganmu tare da annabi (s.a.w) ba a kidaya mutum biyar daga cikinmu face Ammar ya kasance na shidanmu, ba kuma a kidaya hudu face ya kasance cikin na biyar din, amma sai ya sanya sharadin in sallam musu gare shi ya kashe su ya tsire su ya danganta da jinin usman, na rantse da Allah babu mutumin da ya kaishi maitar jinin Usman da kashe shi babu wasu mutane da suka taru kan kashe Usman face shi da masu kama da shi daga iyalan gidansa rassan tsinanniyar bishiya cikin kur’ani.    

فلما لم أجب إلى ما اشترط من ذلك كرَّ مستعلياً في نفسه بطغيانه وبغيه، بحمير لا عقول لهم ولا بصائر، فموه لهم أمراً فاتبعوه، وأعطاهم من الدنيا ما أمالهم به إليه.

فناجزناهم وحاكمناهم إلى الله عز وجل بعد الاعذار والانذار

Yayinda ya ga na ki amsa sharuddansa sai ya kai farmaki yana halin jin `daukakar kansa da dagawarsa da zaluncinsa tare da wasu jakauna da yake tare da su da basu da hankali, sai ya boye musu al’amari su kuma suka bishi, ya basu daga duniya abin da ya jawo su zuw gare shi. Sai muka yake su mukai kai su gaban Allah bayan mun gargade su mun yanke musu uzuri

فلما لم يزده ذلك إلا تمادياً وبغياً لقيناه بعادة الله التي عودناه من النصر على أعدائه وعدونا، وراية رسول الله | بأيدينا، لم يزل الله تبارك وتعالى يفل حزب الشيطان بها حتى يقضي الموت عليه، وهو معلم رايات أبيه التي لم أزل أقاتلها مع رسول الله | في كل المواطن، فلم يجد من الموت منجى إلا الهرب فركب فرسه وقلب رايته، لا يدري كيف يحتال فاستعان برأي ابن العاص، فأشار إليه بإظهار المصاحف ورفعها على الاعلام والدعاء إلى ما فيها، وقال: إن ابن أبي طالب وحزبه أهل بصائر ورحمة وبقياً. وقد دعوك إلى كتاب الله أولاً وهم مجيبوك إليه آخراً، فأطاعه فيما أشار به عليه إذ رأى أنه لا منجى له من القتل أو الهرب غيره، فرفع المصاحف يدعو إلى ما فيها بزعمه، فمالت إلى المصاحف قلوب من بقي من أصحابي بعد فناء أخيارهم، وجهدهم في جهاد أعداء الله وأعدائهم على بصائرهم، وظنوا أن ابن آكلة الأكباد له الوفاء بما دعا إليه، فأصغوا إلى دعوته، وأقبلوا بأجمعهم في إجابته، فأعلمتهم أن ذلك منه مكر، ومن ابن

الأكباد له الوفاء بما دعا إليه، فأصغوا إلى دعوته، وأقبلوا بأجمعهم في إجابته، فأعلمتهم أن ذلك منه مكر، ومن ابن العاص معه، وأنهما إلى النكث أقرب منهما إلى الوفاء، فلم يقبلوا قولي ولم يطيعوا أمري، وأبوا إلا إجابته كرهت أم هويت، شئت أو أبيت، حتى أخذ بعضهم يقول لبعض: إن لم يفعل فألحقوه بابن عفان، أو ادفعوه إلى ابن هند برمته.

فجهدت ـ علم الله جهدي ـ ولم أدع علة في نفسي إلا بلغتها في أن يخلوني ورأيي فلم يفعلوا، وراودتهم على الصبر على مقدار فواق الناقة أو ركضة الفرس، فلم يجيبوا ما خلا هذا الشيخ ـ وأومأ بيده إلى الأشتر ـ وعصبة من أهل بيتي

Babu abin da hakan ya kara masa face tsaurin kai da bata sai muka hadu sa shi da alkawarin Allah da muka saba da shi daga samun nasara kan makiyansa da makiyanmu, tutar manzon Allah tana hannunmu Allah matsarkaki madaukai bai gushe ba yana gusar da rundunar shaidan yana hukunta mutuwa kansu. Shi kuwa mu’awiya yana dauke da tutar babansa wacce ban gushe ba ina yakarta tare da manzon Allah (s.a.w) a kowanne bigire, da yaga ba zai samu matsera daga kisa ba sai ya ari ta kare ya hau dokinsa ya juya tutarsa bai son ma dabarar da zai yi ba. sai ya nemi taimako da dabarar ibn asi, ya yi masa ishara da fito da kur’anai da kuma `daga su zuwa ga mutane da kira zuwa gare su, ya ce lallai ibn Abi dalib da rundunarsa ma’abota basira da jin kai ne da wanzuwa, hakika sun kiraka zuw aga littafin Allah da farko kuma su masu amsa maka ne zuwa gare shi daga karshe, sai mu’awiya ya bi ra’ayin ibn Asi cikin abin da yayi masa ishara zuwa gare shi yayin da ya ga fa babu matserata daga kisa ko dai rantar ta kare, sai mu’awiya ya sa aka `daga kur’anai yana kira zuwa ga abin da ya ke cikinsu bisa rayawarsa, sai zukatan wadanda suka wanzu tare da ni ta karkata zuwa ga kur’ani bayan mutuwar mafiya alherin cikinsu, da wahalarsu cikin yakar makiyansu  kan basirarsu , sai sukai zaton cewa `dan mai tauna hanta yana da cika alkawari cikin abin da yayi kira zuwa gare shi, sai suka juya zuwa ga abin da ya kira su suka tafi baki dayansu  cikin amsa kiransa. na sanar musu da cewa hakan makirci daga gare shi da kuma ibn Asi da yake tare da shi, lallai su biyun sun fi kusa zuwa ga saba alakwari daga cika shi, sai suka ki karbar magana da suka kin bin umarni na, suka dage kan amsa masa zuciya tana so ne ku ba ta so , na ki ko na so, har wani ba’arinsu ya fara fadawa wani ba’ari idan `dan abu dalibi yaki aikata ku riskar da shi da ibn Affan, ko kuma ku tunkuda baki dayansa zuwa`ibn Hindu, nayi baki kokarina Allah ne ya san kokarina, ban bar wata illa cikin zuciya ta ba face na fade ta kancewa su kyaleni kan abin da nake gani amma sai suka ki, na jawo hankalinsu kan hakuri gwargwadon jinkirin tatsar nonon taguwa da sukuwar doki amma suka ki in banda wannan tsohon ya nuni da hannunsa zuwa Malikul Ashtar da wasu jama’a daga Ahlin gidana

فوالله ما منعني أن أمضي على بصيرتي إلا مخافة أن يقتل هذان ـ وأومأ بيده إلى الحسن والحسين «عليهما السلام» ـ فينقطع نسل رسول الله | وذريته من أمته، ومخافة أن يقتل هذا وهذا ـ وأومأ بيده إلى عبد الله بن جعفر ومحمد بن الحنفية رضي الله عنهما ـ فإني أعلم لولا مكاني لم يقفا ذلك الموقف.

فلذلك صبرت على ما أراد القوم مع ما سبق فيه من علم الله عز وجل

فلما رفعنا عن القوم سيوفنا تحكموا في الأمور وتخيروا الأحكام والآراء، وتركوا المصاحف وما دعوا إليه من حكم القرآن، وما كنت أحكم في دين الله أحداً إذ كان التحكيم في ذلك الخطأ الذي لا شك فيه ولا امتراء.

فلما أبوا إلا ذلك أردت أن أحكم رجلاً من أهل بيتي، أو رجلاً ممن أرضى رأيه وعقله، وأثق بنصيحته ومودته ودينه.

وأقبلت لا أسمي أحداً إلا امتنع منه ابن هند، ولا أدعوه إلى شيء من الحق إلا أدبر عنه، وأقبل ابن هند يسومنا عسفاً، وما ذاك إلا باتباع أصحابي له على ذلك.

فلما أبوا إلا غلبتي على التحكم تبرأت إلى الله عز وجل منهم، وفوضت ذلك إليهم فقلدوه امرءاً، فخدعه ابن العاص خديعة ظهرت في شرق الأرض وغربها، وأظهر المخدوع عليها ندماً.

ثم أقبل× على أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Wallahi babu abin da ya hana ni tafiya kan basirata face tsoran kashe wadannan guda biyu sai ya yi ishara zuwa ga Hassan da Husaini (as) ya zamanto tsatson manzon Allah (s.a.w) da zuriyarsa ya yanke daga cikin al’ummarsa, da kuma gudun kada a kashe wannan da wannan ya kara ishara da hannunsa zuwa ga Abdullah ibn Jafar da Muhammad bn hanafiya (rd) lallai ni na san ba da ban matsayata ba da bai dau wannan mataki ba , saboda haka ne na hakuri  kan abin da mutane suka zaba tare da abin da ya gabata  cikinsa daga ilimin Allah mai girma da `daukaka yayin da muka `dage takubbanmu daga mutanen sai suka karfafa kan al’amura sukai zabi cikin ra’ayoyi  da hukunce-hukunce, suka bar kur’anai da abin da aka kirasu zuwa gare shi daga hukuncin kur’ani,ban kasance ina wakilta wani mutum ba cikin addinin Allah ba idan cikin hakimta shi akwai kuskure da babu shakka da jayayya cikinsa, yayin da suka kafe sai dai sai na so wakilta wani mutum daga Ahlina ko kuma dai wani mutum da na yarda da ra’ayinsa da hankalinsa, na kuma aminta da nasiharsa  da kaunarsa da addininsa na fuskanto ban ayyana kowa ba face `dan Hindu mai mai tauna hanta yaki yarda da shi, ban kira zuwa ga wani abu ba daga gaskiya face ya juya masa baya, sai `dan Hindu ya fuskanto yana kuntata mana ba da komai ba face da biyayyar da sahabbaina sukai masa kan zabinsa.

Yayinda suka kafe kan tilastani kan hakimta mutane biyu sai na barranta zuwa ga Allah mai girma da `daukaka daga gare su, na sallama hakan gare su, sai suka rataya al’amarin ga abu musal Ash’ari suka zabe shi wakili daga garemu, sai ibn Asi ya yaudare shi da yaudarar da ta bayyanar gabashin kasa da yammacinta, wanda aka yaudara yayi nadama.

Sai ya waiwayi sahabbansa ya ce: shin ba ai haka ba?

Suka ce: haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: وأما السابعة يا أخا اليهود، فإن رسول الله | كان عهد إلي أن أقاتل في آخر الزمان من أيامي قوماً من أصحابي يصومون النهار ويقومون الليل، ويتلون الكتاب، يمرقون بخلافهم علي ومحاربتهم إياي من الدين مروق السهم من الرمية، فيهم ذو الثدية. يختم لي بقتلهم بالسعادة.

فلما انصرفت إلى موضعي هذا ـ يعني بعد الحكمين ـ أقبل بعض القوم على بعض باللائمة فيما صاروا إليه من تحكيم الحكمين، فلم يجدوا لأنفسهم من ذلك مخرجاً إلا أن قالوا: كان ينبغي لأميرنا أن لا يبايع من أخطأ، وأن يقضى بحقيقة رأيه على قتل نفسه وقتل من خالفه منا، فقد كفر بمتابعته إيانا وطاعته لنا في الخطأ، وأحل لنا بذلك قتله، وسفك دمه.

Sai (as) ya ce: amma ta bakwai ya kai dan’uwa bayahude, lallai manzon Allah (s.a.w) ya karbi alkawari daga gare ni da in yaki wasu mutane daga sahabbaina wadanda suke azumi da yini suke raya dare da ibada suna kuma karanta kur’ani a karshen kwanakin zamani na suna fita daga addini kamar yadda kibiya ke fita daga kwari da baka, acikin akwai zul sudayya, yakarsu zai hattama mini da farin ciki.

Yayin da na juya daga mahallina wannan bayan gama hakimtawa, sai mutane ba’arinsu ya dinga zargi ba’ari cikin abin da suka aikata daga hakimta mutane biyu, basu samarwa kansu mafita daga hakan ba sai gashi sun ce: tun farko kamata yayi ace sarkinmu bai yi mubaya’a ga anda ya tafka kuskure ba, kamata yayi ya yi hukunci da gaskiya daga ra’ayin da yake gani, daga kashe kansa da kashe da kashe duk wanda ya saba masa daga cikinmu, sabodaa haka yanzu jininsa ya halasta sakamakon biye mana da yayi kan kuskure.

فتجمعوا على ذلك، وخرجوا راكبين رؤوسهم ينادون بأعلى أصواتهم: لا حكم إلا لله.

ثم تفرقوا فرقة بالنخيلة، وأخرى بحروراء، وأخرى راكبة رأسها تخبط الأرض شرقاً حتى عبرت دجلة، فلم تمر بمسلم إلا امتحنته، فمن تابعها استحيته، ومن خالفها قتلته.

فخرجت إلى الأوليين واحدة بعد أخرى أدعوهم إلى طاعة الله عز وجل والرجوع إليه، فأبيا إلا السيف لا يقنعهما غير ذلك.

sai sukai ittifaki kan haka, suka fito suna hawan kansu suna `daga sauti suna shela babu hukunci sai na Allah, sannan suka watse wasu suka nufi nukaila wasu kuma suka nufi harura, wasunsu kuma nusa suka tsallake dajala, basu wuce ta gefan wani musulmi face sun jarraba shi idan ra’ayinsu ya zo daya sai su barshi raye, idan kuma ra’ayinsa ya saba nasu sai su kashe shi.

Sai na fito na fara da kashin farko ina kiransu daya bayan daya zuwa biyayya ga Allah da komowa gare shi, sai suka ki sai yaki babu abin da zai gamsar da su in ba takobi ba.

فلما أعيت الحيلة فيهما حاكمتهما إلى الله عز وجل، فقتل الله هذه وهذه، وكانوا ـ يا أخا اليهود ـ لولا ما فعلوا لكانوا ركناً قوياً وسداً منيعاً، فأبى الله إلا ما صاروا إليه

Sa’ilin da duk da bara ta kare cikinsu sain kai kararsu zuwa ga Allah mai girma `daukaka, sai Allah ya halaka wannan kungiya da wancan kungiya daga cikinsu, ya dan’uwa bayahude haka suka kasance ba da ban abin da sukai ba da sun kasanc wani karfaffan rukuni, wani shinge katangagge, sai Allah yaki face makomar da suka zaba ma kansu.

ثم كتبت إلى الفرقة الثالثة، ووجهت رسلي تترى، وكانوا من جلة أصحابي، وأهل التعبد منهم والزهد في الدنيا، فأبت إلا اتباع أختيها، والاحتذاء على مثالهما، وأسرعت في قتل من خالفها من المسلمين، وتتابعت إلي الاخبار بفعلهم.

فخرجت حتى قطعت إليهم دجلة، أوجه السفراء والنصحاء، وأطلب العتبى بجهدي بهذا مرة، وبهذا مرة ـ أومأ بيده إلى الأشتر، والأحنف بن قيس، وسعيد بن قيس الأرحبي والأشعث بن قيس الكندي ـ فلما أبوا إلا تلك ركبتها منهم، فقتلهم الله ـ يا أخا اليهود ـ عن آخرهم، وهم أربعة آلاف أو يزيدون، حتى لم يفلت منهم مخبر.

فاستخرجت ذا الثدية من قتلاهم بحضرة من ترى، له ثدي كثدي المرأة.

ثم التفت× إلى أصحابه، فقال: أليس كذلك؟!

قالوا: بلى يا أمير المؤمنين

Sannan na rubutu aikawa wasika ga kungiya ta uku daga cikinsu, na tura `yan aikena babu yankewa, sun kasance daga mafi yawan sahabbaina, sun kuma kasance daga ma’abota ibada da gudun duniya, amma sai ita wannan kungiya ta uku ta kafe sai tafiya kan abin da `yan’uwanta suka tafi kai, da bin sawunsu, sukai gaggawa cikin kashe dukkanin wanda ya saba da su daga musulmai, labarii suka ka zo mini dangane da aikin da suke, sai na fito na keta garin dajala. Ina halin aika `yan masu yi musu nasiha da tura jakadu garesu, ina kokarin yardarsu da kaikawona a wannan lokacin, wani lokacin kuma da wadancan sai ya nuna malikul Ashtar da Ahnaf bn kaisu da Sa’idu bn kaisu Arhabi da Ash’as bn Kaisu Alkindi, yayinda suka kafe sai dai abin da `yan’uwansu suka zaba na yaki sai na yake su, Allah ya halakasu ya kai baki dayansu ya kai `dan’uwa bayahude, sun kai dubu hudu koma fiya da hakan har ya kasance hatta mai kai labari bai tsira ba daga cikinsu, sai na fito da zul sudaiya (mai nono) wanda yake da nono misalin nonon mata daga cikin wadanda aka halaka da hallarar wanda kake gani,

Sannan ya waiawayi sahabbansa ya ce: shin ba haka bane?

Suka ce haka ne ya sarkin muminai.

فقال×: قد وفيت سبعاً وسبعاً يا أخا اليهود، وبقيت الأخرى، وأوشك بها، فكأن قد..

فبكى أصحاب علي× وبكى رأس اليهود وقالوا: يا أمير المؤمنين، أخبرنا بالأخرى.

فقال: الأخرى: أن تخضب هذه ـ وأومأ بيده إلى لحيته ـ من هذه ـ أومأ بيده إلى هامته.

قال: وارتفعت أصوات الناس في المسجد الجامع بالضجة والبكاء، حتى لم يبق بالكوفة دار إلا خرج أهلها فزعاً.

وأسلم رأس اليهود على يدي علي× من ساعته، ولم يزل مقيماً حتى قتل أمير المؤمنين×، وأخذ ابن ملجم «لعنه الله»، فأقبل رأس اليهود حتى وقف على الحسن×، والناس حوله، وابن ملجم «لعنه الله» بين يديه، فقال له: يا أبا محمد اقتله قتله الله، فإني رأيت في الكتب التي أنزلت على موسى×: أن هذا أعظم عند الله عز وجل جرماً من ابن آدم قاتل أخيه، ومن القدار عاقر ناقة ثمود([4]).

Sai (as) ya ce: hakika na cika bakwai da bakwai ya kai `dan’uwa bayahude, dayar ta ragu na kusa da ita.

Sai sahabbnasa suka fashe da kuka shima bayahuden ya fashe da kuka, suka ce: ya sarkin muminai, ka bani labarin `dayar, sai ya ce: `dayar zata yiwa wannan da wannan kunshi da jini sai yayi nuni da gemunsa da wuyansa, sai masallacin ya cika da kuka da `daga sauti da kuka , har sai da ya zamanto dukkanin mutanen dake garin kufa sun fito waje saboda razana da tsoro, daga karshe bayahuden ya muslunta a hannun Ali (as) a wannan lokaci, sannan bai gushe yana garin har sai da a shahadantar da sarkin muminai (as) aka kama ibn muljama la’ananne sai wannan bayahude ya zo ya tsaya kan hassan (as) alhalin ibn muljam tsinanne yana gabansa  mutane kuma na kewaye da shi, sai bayahuden ya ce: ya Abu Muhammad ka kashe shi kawai Allah ya tsine masa, lallai ni na karanta cikin littattafan da aka saukarwa da Musa (as) da cewa wannan tsinannen yafi girman ta’addanci daga ta’addanci da `dan Adamu ya yi na kashe `dan’uwansa haka daga ta’addanci kuddaru na soke taguwar samudawa

الهوامش

([1]) لعل الصواب إضافة كلمة «على».

([2]) الآية 38 من سورة الأحزاب.

([3]) الآية 23 من سورة الأحزاب.

([4]) الخصال (مؤسسة النشر الإسلامي سنة 1424 هـ ق) ج2 ص400 ـ 418 و (ط أخرى) ج2 ص14 ـ 25 و (منشورات مركز النشر الإسلامي _ قم المقدسة سنة 1403هـ) ص364 ـ 382 والاختصاص ص163 ـ 181 وبحار الأنوار ج38 ص167 ـ 184 وحلية الأبرار ج2 ص359 ـ 381 وغاية المرام ج4 ص317.

الصفحة السابقةالصفحة التاليةفهرس الكتب

امتحان الله عزّ وجل أوصياء الأنبياء في حياة الأنبياء

Jarrabawar Allah mai girma da `daukaka ga wasiyyan annabawa cikin rayuwar annabawa (as)

بسم الله الرحمن الرحیم

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

حدثنا أبي ومحمد بن الحسن (رضي الله عنهما) قالا: حدثنا سعد بن عبد الله قال: حدثنا أحمد بن الحسين بن سعيد قال: حدثني جعفر بن محمد النوفلي، عن يعقوب بن يزيد قال: قال أبو عبد الله جعفر بن أحمد بن محمد بن عيسى بن محمد بن علي بن عبد الله بن جعفر بن أبي طالب قال: حدثنا يعقوب بن عبد الله الكوفي قال: حدثنا موسى بن عبيدة، عن عمرو بن أبي المقدام، عن أبي إسحاق، عن الحارث، عن محمد بن الحنفية «رضي الله عنه»، وعمرو بن أبي المقدام، عن جابر الجعفي، عن أبي جعفر قال:

أتى رأس اليهود علي بن أبي طالب× عند منصرفه عن وقعة النهروان، وهو جالس في مسجد الكوفة، فقال:

يا أمير المؤمنين، إني أريد أن أسألك عن أشياء لا يعلمها إلا نبي أو وصي نبي.

قال: سل عما بدا لك يا أخا اليهود؟

Babana da Muhammad bn Hassan (rd) sun zantar da ni sun ce Ahmad bn Husaini bn Sa’id ya ce: Jafar bn Muhammad naufali ya zantar dani daga Yakub bn Yazid ya ce: Abu Abdullah Jafar bn Muhammmad Isa bn Muhammad bn Ali bn Abdullah bn Jafar bn Abu dalib ya ce: Yakub bn Abdullah kufi ya ce: Musa bn ubaida ya zantar da mu daga Amru bn Abu Mikdam daga Abu is’haku daga Harisu daga Muhammad bn hanafiya (rd) da Amru bn Abi: jagoran yahudawa ya je wajen Ali lokacin da yake juyawa daga yakin naharawan lokacin da yake zaune cikin masallacin kufa sai wannan bayahude ya ce ni ina son tambayarka wasu abubuwa da babu wanda ya sansu sai annabi ko wasiyinsa, sai ya ce masa: tambayi abin da kake son tambaya ya kai dan’uwa bayahude?

Tura tambaya