lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Fushi da hakuri

Na farko: yin hakuri kan zaluntarsa- sai dai kuma cewa kamar yanda bayani ya gabata abind ake nufi da shi zalunci da ya tsaya iya kanka, kamar alal misali ace dan’uwansa ya zalunce shi kowani daga makusantasa ko makotansa, lallai da fari ya kamta ne ace yak are kansa daga zaluncin idan bai samu dam aba kan hakan sai yayi hakuri, idan ya samu dama da iko kan ramawa nan ma sai ya kara yin hakuri bisa abinda ya faru da shi kuma yayi afuwa kai, ya kau da kansa ma’ana kada yayi ukuba bayan yin afuwa kuma kada yayi gorin afuwar da yayi, kadai ya yi ramuwa da misalin abind akai masa, lallai kad aya gaza kasancewa kasa da bishiyar dabino da kananan yara ke jifanta da duwatsu amma kuma ita sai tayi musu yayyafin zakakan`ya`yan dabino, dukkanin wanda ya nuna maka yarinta cikin mu’amalarka da shi yayi maka tsageranci cikin zama da juna ya munana maka, to abinda yafi dacewa kada ka zama irinsa bari dai ka kyautata masa kai masa afuwa ka saka masa da mafi kyawu ka kare kanka da abinda yafi kyawu, don ka samu aboki masoyi mai tace soyayya, lallai su mutane bayin kyautatawa ne. sannan daga cikin kyawawan dabi’u duniya da lahira shine yin afuwa ga wanda ya munana maka ya zalunceka.

Na biyu: danne fushi da danne zuciya da hakuri kan wanda ya fusata ka ya kona maka zuciya, ka bar hakan wurin Allah matsarkaki madaukaki

 

Na uku: afuw ada yin gafara daga wanda ya munana maka Magana da aiki ya zamanto bai gimamaka da mutuntaka ba, bai mutunta matsayinka da girmanka cikin jama’a, sannan riba ta duniya da lahira na biyo wadnanan kyawawan dabi’u uku wato hakuri danne fushi da afuwa, daga cikin ribar akwai: mutum zai kasance daga wadand aAllah zai shigar da su cikin aljanna ba tareda hisabi ba, da kuma samun yin ceto kamar yanda yake ga annabawa da wasiyyai da shuhada da malamai, sai yayi ceto cikin misalin manyan kabilu larabawa biyu.

Tura tambaya