sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Fikhu » Bahasul karijul fikhi shekara 1442- Ruku’u
- » KARIJUL FIKHU 24 MUHARRAM CIKIN MAS'ALAR HALASCIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA MUDLAKAN CIKIN SALLOLIN NAFILA KO DA KUWA YA KAI GA KARANTA RABI
- » gudummawar imam sadik (as) cikin gina al'umma ta gari
- » Mai ceton baki dayan al’umma Al’imamul Muntazar
- » Zazzakar zuma kan falalar daren Lailatul Kadri
- » DAGA ZANTUKAN IMAM MUHAMMAM BAKIR A.S
- » Siyasar muslunci zama na Arba’in
- Tarihi » nasiha da nusantar al'umma
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » Mene ne ma’anar fadin jumlar (iliminsa yafi hankalinsa yawa) shin wannan jumla za ai la’akari da ita suka zuwa ga Sayyid Kamalul Haidari?
- » ?mai yasa mukeso musan Ahalulbait
- » SHIN MUTUM YANA DA ZABI KO KUMA AN MASA TILAS NE_TAREDA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
- Fikhu » bahasul karijul fikhi shekara 1442 h 6 watan Jimada Awwal
- » Daukakar himma
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Wuri: Muntada Jabalul Amil Islami-tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi
Lokaci: karfe 9 na safe.
Fikhu (88) 23 ga watan Shawwal shekara ta 1442 hijiri
Cigaba kan bahasin d aya gabata: Assayidul Yazdi Allah ya tsarkake ruhinsa cikin littafin Urwatul Wuska karkashin masl’alar taklidi mas’ala mai lamba 30 kamar haka: da Mujtahidinsa na farko da ya fara taklidi da shi fatawowinsa za su saba Mujtahid na biyu da ya dawo yana taklidi da shi babu banbanci cikin ibada ne ko mu’amala kamar misalin cikin tasbihatul arba da ake karantawa a raka ta uku da ta hudu cikin kasancewar fatawar Mujtahidin farko ta tafi kan wadatuwa da karanta kafa daya kuma kan hakane waccan da yake taklidi da shi abaya yayi aiki kai gabanin komawa wurin na biyu sai dai cewa kuma Mujtahidi na biyu da ya koma gareshi shi fatawarsa ta tafi kan wajabcin karanta kafa uku, kamar yanda yake cikin indancin taimama idan ya kasance na farko yana ganin wadatuwa da buga kasa sau daya ya wadatar koma bayan na biyun da ya tafi kan jerantawa, daga wannan misali ne ake sanin ingancin ibada baya ginuwa kan hadisin: (la tu’adu) wanda ya kebantu da sallah da cikin mu’amaloli cikin kebantacciyyar ma’ana muna nufin cikin (ukudu) kulla ma’amala daga bangare biyu da kuma (Ika’at) zartar da ita daga bangare guda kamar misalin sakin aure, cikin misalin ace Mujtahidi na farko yana da fatwar ingancin kulla aure cikin yaren farisanci shi kuma na biyu ace ya shardanta kulla shi cikin harshen larabci, a irin wannan hali za a tafi kan ingancin kullawa da fatawar na farko ko da kuwa ya kasance cikin farisancin ne, na’am da ace zai yanka Akuya da kwalaba sai ya zamana Mujtahidi na biyu shi ya shardanta yankata da Wukar karfe to cikin wannan hali abinda yaci gabanin komawa wajen na biyu zai kasance yaci haramun Kenan, amma abind aya rage daga naman lallai bai halasta ya ci shi ba kamar yanda bai halasta ya sayarwa da wani kasancewa da hukuncin mushe, misalin wannan kaddarawa shin a farko baya hukunta najasarsa shi kuma na biyu ya tafi kan najasarsa, sallarsa cikin tufafin kan fatawar Mujtahidin farko ingantacciya ce amma sallolin da zai yi su nan gaba lallai wasu malaman suna ganin rashin ingancinsu, Assayid Yazdi ya zabi inganci cikin ayyukan da suka gabata cikin ibada ne ko mu’amala da kebantacciyar ma’ana ma’ana Ukudu da Ika’at shi ya tafi kan wadatarwarsu babu bukatar maimaitawa.
Amma cikin wanin ibada da mu’amala da kebantacciyar ma’ana kamai misalin cikin gamammiyar ma’ana lallai Assayid ya zabi kiyaye ijtihadin guda biyu cikin maudu’ai koma bayan hukunce-hukunce lallai ba zai yiwu a tattara tsakanin ijtihdi biyu ba.
Wannan shine ra’ayin da Sahibul Fusul ya tafi kansa kan inganci da wadatarwa cikin ayyukan da suka gabata cikin maudu’ai koma bayan hukunce-hukunce ya kuma kafa hujja da cewa maimaicin zai lazimta kunci da tsanani wadanda zasu jo rikicewar tsari.
Sai dai cewa dalilan kore tsanani da kuntata suna shiryarwa kan cewa tsananin da kuncin guda daya ne bawai na kowa da kowa kamar yanda yake cikin ka’idar kore cutuwa da cutarwa sai ya zamana ya lazimta warwara cikin ka’idar kore tsanani da kuntata kowanne guda yana da hukuncinsa, idan maimaici bai haifar da kuntatuwa da tsanani ba to taklifin maimaicin baya faduwa, ko kuma ace: faduwar taklifi gwargwadon kunci da tsanani.
Kankanin tsanani ba zai tabbatar da wadatuwa da faduwar maimaici ba, amma wanda yake jawo halakar dukiyar mutane da rigima da fadace-fadace da ruguje tsari lallai cikinsa Musanniful Kurasani Allah ya tsarkake sirrinsa ya tafi kan ka’ida Awwaliya daga gurbatar ayyukan da suka gabata da rashin wadatuwa sakamakon samuwar hukunci gud adaya a waki’i kuma akasinsa bai tabbatu ba, ka’ida ta hukunta rashin wadatuwa face dai abinda ya fita da dalili kamar yanda cikin sallah da hadisin La tu’adu da bayani kansa ya gabata.
Cikin canjawar ra’ayi da sabawar Mujtahidai biyu Magana tana kasancewa cikin mukamai guda biyu: na farko shine wadatuwa da rashinsa bisa ka’ida, na biyu: bayan tabbatuwar rashin wadatarwa bisa dacewa da Ka’idatul Awwaliya a wannan mukami, ta iya yiwuwa ijtihadin Mujtahidi na biyu yana kashafi da bayyanarwa a yakinance kan cewa ayyukan da suka gabata sun sabawa hakika, lallai dalili cikin ijtihadi kadai yana shiryarwa kan ingancin ayyuka da zasu zo koma bayan wadanda suka gabata, a bayyane yake cewa ayyuka da ya zo da su a baya karkashin ijtihadin Mujtahidinsa na farko sun kasance kan asasin hujjojin hankali da na shari’a, kamar yanda yanzu ma a ijtihdi na biyu yana kan hujjojin hankali da shari’a, da za a ce ijtihadin farko ya rushe ya gushe sakamakon na biyun yana abin la’karin a lokacin da akayi shi dangane da ingancin ayyukan da suka gabata, babu cin karo da juna ubangiji ya bautar damu d ana farko cikin wannan ma’anar.
Sai dai cewa akwai ishkali da zai gangara kansa da farko dai wannan baya kara la’akarin shari’a da riko da ilimi n agama gari da hadisin Sika ya fa’idantar daga ilimi na yankan shakku da yakini, lallai da zai samu yakini da yankewa kan wani lamari sai kuma daga baya ya gushe ya fada cikin shakku cewa yakininsa da yankwarsa ta farko ya kasance cikakke ko gurbatacce lallai cikin dukkanin surorin guda biyu babu la’akari cikin yankewarsa da yakininsa na farko, lallai shakka cikin hujja tana matsayin rashin hujja kwata-kwata, anan cikin wannan mukami idan ya kasance tabbatuwar hukuncin farko ya kasance da dalilin na zato da ake la’akari da shi da ilimi na gama gari da mfi cancantuwar hanya ana tafiya ne kan rashin la’akari da zatonsa na farko, babu wahamin wadatarwa, lallai abind aya kasance gareni a baya ba zai kasance fiye da ilimin wujdan da yakini ba, abinda zai kasance gareni nan gaba zai sauka ne masaukar ilimi tunda farko to ta yaya za a zabi wadatarwa a wannan yanayin sai dai idan za a zabi gurbataccen tasiwibi d ayake a mazhabarmu.
Wannan Kenan amma sabani zai bayyana kuma bayyana ta kasance daga bayyana ta hakika baki daya kamar yanda yake cikin yankewa da ilimi na yakini, amma da bayyanar da yayewar zasu kasance daga yayewa ta la’akarin shari’a cikin ba’ari kamar yanda yake a zahiri cikin Kalmar Nikahu (aure) da cewa shi wurga igiya ne da karbarta tareda ayyanarwa daga shari’a cikin lafazinsa, yayewar farko a wannan lokaci ba zata kasance daga yayewa ta hakika ba cikin Lauhul mahfuz, a wannan lokaci mai bayanin shari’a zai iya la’akari da ilimi na yanke shakku da ya gabata hatta cikin gushewarsa da ilimi na biyu tareda tafiya kan gurbacewar taswibi, haka lamarin yake cikin ilimi na la’akari na shari’a kamar misalin cikin riko da hadisin Sika, kamar ikirarin Zaidu cewa wannan gida na Amru ne sai kuma ya dawo ya janye ikirarinsa da yayi da farko, ya yi ikirari da cewa wannan gida na Bakar ne, akwai tsammanin rashin ingancin ikirarin farko d aingancin ikirari na biyu, kamar yanda akwai tsammanin dacewa da hakika, domin ikirarinsa na farko hujja ne kamar yanda na biyu ma haka hujja ne, da farko da yayi wannan ikirari ya mika gida ga Amru na lazimtawa Bakar asarar gidan sakamakon ya mika shi ga Amru, dole cikin wadannan ikirari biy daya ya dace da hakika.
Haka al’amarin yake cikin bahasinmu, lallai ba da ban yayewa da kashafin ya kasance yankakke na yakini da hakika ba, ijtihadin farko ya dace da zuhurin hujja ne, haka wajibi gareshi yayi aiki da na biyu dangane da ayyukan da zai yi nan gaba, kan wannan ne muka zabi wadatarwa a wannan magangara ba tareda hakan ya lazimta tafiya kan taswibi ba.
Ishkali kadai cikin wannan Magana shine cewa bamu da dalili kan yiwuwar hakan a hankalce, da ma’anar cewa bai fada kan harshen dalili ba kan wannan ne shi rashin dalili dalili ne kan rashinsa, saboda haka babu dalili kan la’akari da ijtihadin farko tareda samuwar na biyu, lallai da ace ya kasance abin la’akari da ya bukatu zuwa ga kaidi da dabaibayi ma’ana tafi kan la’akari da shi saki babu kaidi ko da kuwa sabaninsa ya bayyanu ta hanyar ijtihadi na biyu, sakamakon dalili kan lazimcin rashin wadatarwa bai samu ba dangane da ayyukan da suka gabata, ko da ma mun zabi yiwuwarsa a zatinsa sai dai cewa babu dalili kansa.
Ba za ace lallai shi cikin maudu’ai yake ba kadai dai muna zabi wadatarwa dangane da ayyukan da suka gabata sakamakon riko da dalilan Asaru da Haraju (kore kuntata da tsanani) an bada amsa da cewa tsanani ne na mutum guda daya bawai na nau’I ba da na kowa da kowa da zai sassabawa da sabawar mutane da zamani da wurare da hususiyar kowanne mutum guda.
Bari dai muna zabi ingancin ayyukan da suka gabata sakamakon abinda ake fahimta daga ruhin shari’a tsarkakka daga saukaka da saukakawa, shi addini sauki ne.