lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ili yasin cikin kur’ani_tareda Assayid Muhammad Alawi

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Me ake nufi da (Ili yasin) da ya zo cikin kur’ani mai girma?

Hakika Allah cikin kur’ani mai girma cikin suratul Safat ya ambaci Nuhu (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin talikai) bayansa kuma ya kawo Ibrahim (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Ibrahim) bayansa ya kawo Musa da Haruna (as) ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Musa da Haruna) bayansu sai Ambato Iliyas (as) ya ce: sai suka karyata shi, bayan haka sai ya ce: (amincin Allah ya tabbata ga Iliyasin) bayansa ya ce: lallai shi, wanda lamirin da yazo mufradi ne na mutum daya rak.

Ka sani hakika tafsirai da maganganun malamai sun sassaba cikin ma’anar wadannan ayoyi masu daraja sai dai cewa ra’ayin da yafi shahara daga malamai ya tafi kan rubuta aya  wannan aya da yanayi rabewa da juna tsakanin Al da Yasin sannan daga cikin maganganun akwai wacce take dacewa da rabewa sai dai cewa yana cin karo da siyaki zuben ayoyin da suka gabace da wadanda suka zo a bayanta , daga cikin maganganu akwai wanda ya sabawa rubutu sai dai cewa ya dace tareda siyakin gangarowa da salsalar ayar.

Mashhur din malaman tafsiri suna kan ra’ayoyi uku:

 

1-   Fuska ta farko: Sun tafi kan cewa Al yasin shi ne dai sunan wannan Annabi Allah wato Annabi Iliyasu wanda aka ambata cikin ayar data gabata, sannan Karin da akayi ciki da harafin ya’un da nunun a karshen Kalmar hakan na daga sanannen abu ne wurin larabawa a wancan lokaci daga abin da suka nakalto dana yarukan ajamawa wadanda ba larabawa ba ya zuwa harshen larabci, kamar misalin Sina’u da siniyin.

Abin da yake karfafar hakan shi ne siyakin da ya zo cikin ayoyi yana goyan bayan wannan tafsiri.

 

Ishkali : da farko dia wannan da’awa taku ba ta tabbata ba cikin harshen larabci dangance da Kalmar Yasin, sannan na biyu shi ne hakan na cin karo da rubutun Kalmar Al yasin a rarrabe da ya zo cikin wannan aya, na uku: wannan Magana taku tana cin karo da riwayoyi da suka zo daga Ahlil-baiti (as), na hudu: yana cin karo da tafsirai da shahararrun maganganu da hadisai da suka gangaro ta hanyar Ahlil-sunna.

 

2-    Fuska ta biyu:Il yasin shi ne mahaifin Iliyasu ko kuma da ma’anar Kabilar Iliyasu, abin da yake karfafar wannan fuska ta biyu: shi ne rarrabewa cikin rubutun Kalmar na karfafar wannan ra’ayi.

 

Ishkali kan wannan fuska ta biyu: da farko dai bai tabbata ba cikin tarihi da riwayoyi cewa Ilyasu yana da wani mahaifi mai suna Yas ko Yasin ko makamancin haka, na biyu: hakan na cin karo da siyakin ayoyin da suka gabata, na uku: yana cin karo da riwayoyin da suka gangaro daga Ahlil-baiti (as), na hudu: wannan Magana tana cin karo da tafsirai da maganganu shahararru da hadisai da suka zo daga hanyar Ahlus-sunna.

 

3-fuska ta uku: Alu Yasin ya zo ne da ma’anar iyalan Manzon Allah (s.a.w) wadanda sune Ahlil-baiti (as).

Abin da yake tabbatar da haka shi ne: rarrabewa da take tsakanin Alu da Yasin, na biyu: riwayoyi masu tarin yawa da suka zo daga hanyar Ahlil-baiti, na uku: tafsirai da mashhuran maganganu da hadisai da suka gangaro ta hanyar Ahlus-sunna.

 

Ishkali kan wannan fuska: dukkanin riwayoyin da suka kan karfafar wannan fuska basu tabbatu b aba za a iya dogaro da sub a, na biyu: wannan Magana tana cin karo da shahararriyar Kira’ar kur’ani, na uku: wannan fuska tana cin karo da shahararren rubutun kur’ani wanda yake a hannunmu ai cin karo a rubuce, na hudu: wannan fuska tana cin karo da siyakin ayoyin da suka gabaceta, kamar yanda yake cin karo da tafsirai da shahararrun maganganu da hadisai da suka gangaro ta hanyar Ahlus-sunna ko kuma ma ace ta hanyarmu kamar yanda yake wurin Saduk.

 

Cikin bad amsa ina cewa: Allah ne masani hakikanin al’amura, amma amsa kan ishkalin farko: lallai riwayoyin da suka zo cikin wannan babi suna matukar yawa sun kai haddin tsallake raunantuwa da suka cikinsu, kuma wannan ra’ayi ya samu karfafa daga maganganun da aka nakalto daga manya-manyan malaman tafsiri daga Ahlus-sunnam daga cikinsu: abin da Allah ya jikan rai Saduk ya nakalto daga cikin littafinsa mai daraja mai wato Uyunul Akbar Rida (a.s) daga Rayyan bn Saltu daga Imam Rida (as) cikin wani hadisi mai tsayi cikin banbanci tsakanin Itra da Umma, ya koro hadisin har zuwa inda yake cewa: ka bani labari daga fadin Allah Azza wa Jalla me yake nufi da fadinsa (Yasin) ? sai ya ce: malamai sunce Yasin sune Muhammad babu wani mutum da yake shakka cikin haka, Abu Hassan (as) ya ce: hakika Allah Azza wa Jalla ya baiwa Muhammad da iyalansa daga haka falala wani mutum bai iya kaiwa ga kurewarsu da siffarsa face wanda ya hankalce shi, hakan ya faru saboda Allah Azza wa Jalla bai yi gaisuwa ga wani mutum face sai Annabawa: sai Allah ta’ala ya ce: (aminci ya tabbata ga Nuhu cikin talikai) ya kuma ce: (aminci ya tabbata ga Musa da Haruna) bai ce: aminci ya tabbatu ga iyalan Nuhu ba ko iyalan Ibrahim ba ko na Musa da Haruna, amma sai ya ce: (Aminci ya tabbata ga Alu Yasin) ma’ana iyalan Muhammad.

Daga cikinsu: akwai abin da ya zo daga sabani cikin kira’ar Hamza bn Habibul Zayyat shahararren malamin kira’ar nan daga masana kira’a guda bakwai da kuma kira’ar malaminsa Imam Assadik (as) ta yanda ya bishi cikin kira’a sai cikin wurare guda goma kidayantattu daga cikinsu akwai wannan ayar wacce ya kasance yana karanta ta da (salamun ala Il yasin) kishiyar kira’ar malaminsa Imam Assadik (as) wanda ya kasance yana karanta ta da (salamun ala Alu yasin).

Sai kuma kira’ar Hamzatul Wasidi (625/2) kira’ar Imam Assadik (as) littafin Ibn Jazari: j 1 sh 196.

Salamun ala Nuhun fil Alamin, ya ce: salamun ala Ibrahim, ya ce: salamun ala Musa wa Haruna, sannan ya ce: salamun ala Alu Yasin, ma’ana iyalan Muhammad.

 

Cikin wannan babi akwai wasu riwayoyin daban da suke karfafar wannan tafsiri da wannan kira’a wajibi ga mai bibiya ya koma zuwa garesu.

 

Amsa kan ishkali na biyu: wannan kira’a tana daga kira’o’I bakwai na da ake karanta wannan aya dasu, karatu na da yancin zabar kowacce daga cikinsu.

 

Amsa kan ishkali na uku: rubutu a karnonin farko daga hijira sun kasance babu digo cikin haruffa da wasali saboda hakane rubutun kalma (Al) cikin (Il yasin) da (Alu yasin) aka rubuta dukkaninsu da shakali guda day aba tareda banbanci ba shi ne (Al yasin) babu cin karo.

 

Amsa kan ishkali na karshe: zamu iya hada tsakanin wannan Magana da kuma siyakin ayoyin da suka gabata mu ce: mun samu cikin ayar data gabaci wannan aya mai albarka bayanin kan fadin

        

   (تَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ)

Muka barshi kansa cikin mutanen karshe.

 

Wanda bangarori biyu sun yi ittifaki kan cewa lallai al’ummar Muhammad (s.a.w) ake nufi sune karshen al’umma tsakanin al’ummu. Wannan aya kadai dai ta maimaitu cikin ayoyin da suka gabata yayin ambaton kowannce Annabi sai dai cewa cikin Annbawa bayan Ilyasu bamu samu wannan aya tareda ambatonta ba cikin Ilyasu, shi ne ambatonta na karshe cikin wannan siyaki, saboda hakane Allah ya nufi bayyana manufarsa daga mutanen karshe cikin wannan aya da cikin ayoyin da suka gabata, suna wadanda suke bin Alu Yasin suna Imani da su bawai kowacce al’umma ba.

 

Tambihi: wannan tattara da hadawa babu wani da ya taba yin misalin haka a baya, kadai dai hadawa ce da akai domin neman lada tsakankanin riwayoyi da suka zo daga Ahlil-baiti da tsakanin siyakin ayoyi cikin wanna sura mai albarka, bai buya ga wanda ga wanda bai yarda da riwayoyin ba da jingina su ga Ahlil-baiti (as) to wajibi dole gareshi yayi Imani da daya daga cikin shahararrun maganganu da aka ambata anan, ko kuma dai yayi Imani da daya daga cikin maganganu wadanda basu shahara ba.

.

 

Tura tambaya