lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Amintaccen Attajiri

Akwai wani babban Attajiri da ya kasance sananne sakamakon rikon amanar sa ya kuma kasance mai tsoran Allah cikin ta’ammulin sa da mu’amalar sa da iyalin sa, a koda yaushe yana yawan tafiye-tafiye daga wannan wuri zuwa wancan sabida kasuwanci, sai ya yanke shawara da cewa fa yanzu lokaci yayi da zai zami wuri guda ya zauna sakamakon shekarunsa sun ja ya tsufa jikin sa ya raunana ba zai iya cigaba da jurewa wahalhalu tafiye-tafiye ba, sia ya tafi wani gari yana neman gida mai girma da zai dace da shgi da kuma kasuwancin sa, sai kwatsam ya samu labari wani mutum yana son sayar da gidan sa, sai ya dauki kafa ya tafi wajen sa sai ya ga gidan say a birge shi daga karshe ya saya, bayan wani lokaci sai yayi niyyar yin gyare-gyare cikin gidan yayi niyyar ruguje wani bango domin ya kara fadin gidna, yayin da ya rusa wnanan bango sai kawai cikin sag a wata tukunya binnanniya cike da gwale-gwale, sai yace wallahi wannan tukunya ba mallaka ta bace, ya zama wajibi in mayar da ita ga wanda na sayi gidan daga gareshi , sai ya tafi wurin sa ya mika masa wannan tukunya yace masa wannan tunkunya ba mallaka ta bace, sai mai gidna yace a a wallahi ba tawa bace na riga na sayar maka gidan da dukkanin abinda yake cikin sa. Sai rigima ta kaure tsakanin su, daga karshe suka yanke shawarar tafiya wajen Alkali don yanke rigimar dake tsakanin su kan wanda zai karbi wannan tukunya, yayin da Alkali ya gansu sai yace: wallahi cikin rayuwata ban taba ganin amintattun mutane misalin ku ba kuna rigima kan kin karbar taska maimakon yin rigima kan mallakarta, sai ya tambaye su shin kuna da `ya`ya sai dan kasuwar yace: ina da `da wanda ya sayar masa da gidan shi kuma yace ina da `diya mace, sai Alkali yace: to `danka ya auri diyar sasai ku raba musu taskar , sai suka gamsu da wannan hukunci suka amince kan auren suka rayu cikin kwanciyar hankali da ni’ima da farin ciki da nutsuwa.

Tura tambaya