Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Falalar ilimi da malamai
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Falalar ilimi da malamai

Idan har ilimi ya kasance taskoki to lallai tambaya za ta kasance mabudinsa, kadai mu na tambayar ma’abota Ambato wato daga malamai nagargaru daga shugabanni Muhammad (s.a.w)da iyalansa tsarkaka, lallai tatacaccen ilimi da ayoyi mabayyana suna cikin kirazan wadanda aka baiwa ilimi, sannan babu inda za a samu wannan ilimi face daga mabubbugarsa ta haske da

mashayarsa daddada, idan kaso na nufi gabas ko yamma ba zakat aba samun abinda zai warkar da mara lafiya da kosar da mai kishi ba face cikin kur’ani da sunnar annabi da tsatsonsa tsarkaka, babu wani abu mafi falala bayan ma’arifa-daga sallah, wannan na nufin gabatuwar ma’arifa da ilimi kan sallah wacce ta kasance itace ginshikin addini kuma itace mafi falalar ayyuka, raka’a biyu da malami yake sallatarta tafi alheri daga raya daren jahili da yin ibada, hakan ya kasance sakamakon shi jahili ta yiwu ya raurawa ya girgiza cikin akidarsa da ibadarsa sakamakon gangarowar shubuha ko wasiwasi kansa daga shaidani, ko kuma wahami da karkata da zasu sanya yabar ibada, amma shi malami yana kan ilimi da yakini cikin ibadarsa, lallai shi malami kamar misalin kafaffen dutse ne da guguwa daga gayyar tunanunnukan bata da shubuhohi ba ta iya motsa shi, da ilimi ake bautawa Allah ake kuma kadaita shi, lallai kawarijawa sun kasance daga sahabban sarkin muminai Ali (as) sun kasance suna tsayar da sallah lallai su sun kasance ma’abota bakaken goshi sakamakon yawan sujjada, sai dai cewa su basu kasance ma’abota cikakkiyar ma’arifa da ilimi mai amfanarwa, sai suka juya suna yakar imamin zamaninsu suka fito suna kalubalantarsa.

Ya zo cikin tarihi cewa daya daga cikin sahabban sarkin muminai (as) cikin wani dare ya ksance yana tafiya tareda shi cikin daya daga lungunan kufa sai yaji muryar wanda yake karanta kur’ani da murya wanda yake cikin halin bakin cikin fadinsa madaukaki:  

 

(أمَّنْ هُوَ قَانِتٌ آنَاءَ اللَّيْلِ سَاجِدآ وَقَائِمآ)

Shin wanda ya kasance mai tawali’u gefan cikin lokutan dare yana halin sujjada da tsayuwa ga sallah.

Sai matsayin mutumin da yake karanta kur’ani da kusancinsa ga Allah ya darsu cikin zuciyar wanda suke tare da imam, sai imam yace: kada ya rudeka lallaoi shi yana daga Ahalin wuta, sai kwanaki suka shuda sai kawai ga wannan mai karanta kur’ani cikin halakakkun kawarijawa da a ka kashe a yaki, Allah ya fifita malami da iliminsa matukar dai iliminsa ya cudanyu da aiki nigari, ya siffantu da halaye nagargaru yana kuma tsoran Allah  

 

 (إنَّمَا يَخْشَى اللهَ مِنْ عِبَادِهِ العُلَمَا

Kadai masu tsoran daga bayinsa sune malamai.

 Abinda ake nufi da malamai anan sune wadanda aikinsu ya gasgatar da zancensu, da misali wadannan malaman ne ake cewa idan malami ya gyaru baki dayan duniya zata kasance cikin albarka, zai kuma kasance albarka kan halittu, sai ya tseratar da bayin Allah daga jahilci da shubuhohi da karkacewa ya shiryar da mutane da raunana zuwa ga sanin Allah da manzonsa da imamin zamaninsu har rayuwarsu da mutuwarsu ta kasance kan gaskiya da ilimi.  

Tura tambaya