lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul karij 27 Shawwal shekara 1441 cikin bahasin Taklidi

Wuri: birnin Qum mai sarki_cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami-tareda Assayid Adil Alawi Allah ya kara masa kariya.

Lokaci: karfe 9 na Asubahi.

Usulul Fikhi (89)

Fasali: cikin Taklidi:

Mawallafin (ks) yace: shi taklidi shine riko da da yin aiki da ra'ayin wani Malami daga cikin Malamai domin yin aiki da shi cikin far'iyyat (rassa) ko kuma muce lazimtar ra'ayinsa cikin akidu a bautance ba tareda da binciken dalilan da ya dogara dasu ba.

Ina cewa: bahasi na faraway a bayana sanin ma'anar Kalmar ihtihadi a luggance da isdilhai da abind aya ta'allaka da shi daga hukunce-hukunce cikin taklidi, hakika magana ta gabata dangane da ijtihadi wanda yake matsayin Katima hattamawa ga ilimin Usul kamar yanda muka sani shi mawallafin bai wofintuwa daga munasaba, sai dia cewa bahasi gameda taklidi lallai yana daga gamammen bahasi ba da ban kasantuwar hakan ba da sai muce muhallinsa yafi dacewa cikin ilimin fikhu.

Daga nan kuma sai Mawallafin ya karkata mas'aloli uku daga : ta farko: dalilan wajabcin Taklidi kan ba'amme, ta biyu: wajabcin taklidin A'alam, ta uku: Taklidi da Matacce.

Wannan fasali an kulla shi ne domin bayanin ma'anar taklidi a luggance da isdilahi da kuma bayani kan dalilan halascinsa a bautance da shari'a.

A luggance: yana da ma'anar sarkar d aake ratayawa a wuya, ya zo cikin Lisanul Arab: daga cikin ma'anarsa akwai taklidi a cikin addini da taklidi da majibantan lamurra ma'ana shugabanni, da taklidin dabbar hadaya a lokacin Hajji ma'ana rataya masu wata alama a wuya domin bayyanar da ita, da kuma ratayuwa da wani al'amari ; hakama rataya Takobi. (Lisanul Arab j 3 sh 366-367).

Allama Duraihi cikin Majma'ul Baharaini j 3 sh 132 yana cewa:

 (وقلّدته قلادة: جعلتها في عنقه، وفي حديث الخلافة: فقلّدها رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم علياً عليه السلام: أي ألزمه بها، أي: جعلها في رقبته ـ كالقلادة ـ وولّاه أمرها...

Na rataya masa sarka: ma'ana ya sanyata a wuyansa, ya zo cikin hadisin Halifanci: sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalansa ya ratayata a wuyan Aliyu (a.s) ma'ana ya lazimtata a gareshi , ai ya sanyata a cikin wuyansa kamar misalin sarka ya jibantar da shi lamarinta.

Taklidi a isdilahin ma'abota ilimi: shine karbar ra'ayi wani mutum ba tareda dalili ba kansa ba, saboda shi mai yin taklidi yana sanya abinda yake kudurcewa

 Daga ra'ayin waninsa matsayin gaskiya, bayan nan taklidi yana karkasuwa ya zuwa mai kyawu  da mara kyawu idan ya kasance ya ginu ya doru kan jahilci kamar misalin taklidin da `ya`ya suke yiwa Iyayensu cikin bautar gumaka kamar yanda bayanin haka ya zo cikin Kur'ani mai girma, haka mai kyawu yana kasancewa idan ya ginu kan ilimi kamar yanda yake cikin bahasinmu a yau ta yanda mai taklidi yake fadin wannan shine fatawar da mai fatawa ya fitar ita hukuncin Allah ce kan wuyana, yana daga kiyasi mai matsala na farko intajinsa saukakakke ne ingantacce ne bayan ingancin mukaddimominsa daga Sugra da Kubra.

Sannan taklidi cikin sigarsa  kan wazani sulasi daga kalada yukallidu yana daga fi'ili muta'addi ya zuwa ga maf'uli guda daya kamar yanda ake cewa: (kalada Zaidu Saifa) Zaidu ya rataya Takobi ya sanyata cikin wuyansa kamar Sarka idna ya kasance daga babin taf'ili mazidun fihi da tad'ifi lallai yana ta'addi zuwa ga maf'ulai biyu kamar yanda ake fadi:  (kallada Amru Zayadan Saifa) Amru ya rataya Takobi a wuyan Zayad.

Wannan duka bisa ma'anonin lugga da tartibi daga ciki akwai ma'anarsa a al'adance kamar yanda ake cewa: (kallada Zaidu Amran kaulahu wa fi'ilahu) Zaidu ya ratayawa Amru fadinsa da aikinsa, wannan yana daga hikayoyi zance da aiki.

Amma a Isdilahin fikhu da abinda Fakihai suke kai to hakika sun sassaba cikin bayani da ta'arifin menene taklidi cikin shardanta cewa dole ta'arifin ya kasancewa ya cika ya kori duk wani abu da bashi ba , sannan Malamai sun yi suka kan ba'arin wasu ta'arifofin taklidi sakamakon kasancewarsu basu tattaro komai ba da komai ba nasa basu kuma hana abinda bashi ba shiga cikinsa, abi kaddarawa cikin isdilahin Fikhu shine Mukallid  wasalin kasara yana aiki da fatawar Mukallad da fataha, kan haka Sarka ta waje da ake kwaikwayo bata kasance tana ishara ga dukkanin biyun ba kamar yanda ta kasance cikin misalin wanda ya rataya Takobi da wanda aka ratayawa, kan wannan zai zamana anyi amfani da ita majazan jeka na yika ba hakika ba daga babin abinda ake kira da isti'ara (aro) abinda ya dace da wannan ma'ana ta lugga domin kasance daga nakali da aka saba da shi daga gamammiyar ma'ana shine a tsaya a yi mulahaza da kaidi zai gasgagtu kanta da fataha ko kasara, da wasalin kasara ta fuskar sanya fatawar Mujtahidi Masani cikin wuyansa ya zamana kenan ya rataya da fatawar wannan Mujtahidi shi Mukallid da wasalin kasara, daga fuskar kasancewar fatawa a wuyansa misalin Sarka to anan shi Mukallad ne da fataha.

Na biyu: a wata fuska daban ba'amme ya zamana ya sanya addininsa cikin ibadoji da mu'amaloli ma'ana cikin rassa (furu'uddini) a matsayin sarka cikin wuyan Mujtahidi Masani wand aya cika sharudda  ya dora masa nauyin mas'uliyar ayyukansa daga ibadoji da mu'amala  da wasunsu, shi ba'amme a wannan yana kasancewa Mukallid da kasara sakamakon kasancewarsa mai ratayarwa da sanya Sarka wacce anan itace addini shi kuma Mujtahidi Mukallad da fahata sakamakon kasancewarsa maabocin Sarka da Jahili ba amme ke rataya masa.

Sannan magana tana kasancewa cikin mukami guda biyu: na farko: ta'arifin Taklidi a wurin Fakihai daga Ammawa da kebantattu a cikin jumla, na biyu: hukunce-hukuncen Taklidi a takaice.

Amma mukami na farko: hakika manyan Malamai sun sassaba cikinsa sun yi ta'arifinsa da unwanai masu tarin yawa:

Na farko: shine karba da riko da ra'ayi da fahimtar wani mutum domin yin aiki da shi ba tareda bincika dalili ba, wannan shine ta'arifin da mawallafin ya tafi kansa (ks) da kuma wasu adadi daga manyan Malamai.

Na biyu: karbar ra'ayi ba tareda hujja ba, wannan shine ra'ayin Gazzali da wasu.

Na uku: lazimtar aiki da maganar Mujtahidi ayyananne, ko da kuwa bai yi aki da shi ba daga baya, kamar yanda ya zo cikin urwatul wuska j 1 sh 15 mas'ala 8 kamar yanda wasu adadi suka zabe shi.

Na hudu: aiki da yake jingine ya zuwa fatawar Mujtahidi, ko kuma dabbaka aiki kan fatawarsa ko wani abu makamancinsa.

Na biyar: biyayya ga wani mutum, kamar yanda aka hakaito daga Risalatu Shaikul A'azam (ks) cikin Ijtihadi da Taklidi.

Na shida: lallai shi bibiyar Mujtahidi ne cikin aiki tareda kasancewa yana mai jingina kan ra'ayinsa cikin aiki, kamar yanda aka hakaitio daga Assayid Ha'iri Yazdi cikin ta'alikinsa kan littafin Urwatul Wuska.

Mawallafin (ks) ya gangara ya zuwa ga ma'ana ta farko da ta biyu sai ya zabi ta farko ya kuma yi munakashar ta hudu kamar yanda bayani zai zo nan gaba da yardar Allah ta'ala.

Gabanin tsunduma ckin maudu'I da kuma ra'ayin da muka zaba daga ra'ayoyi babu laifi mu dan gangara ya zuwa ga abinda mawallafin littafin Urwatul Wuska ya fada da kuma abinda ya gangara kansa cikin talikinsa:

Assayid Yazdi Allah ya tsarkake sirrinsa mai daraja cikin mas'alar Ijtihad da Taklid mas'ala 8 yace: taklidi shine lazimtuwa da aiki da fadin Ayyanannen Mujtahidi ko da kuwa daga baya baiyi aiki ba bari dai ko da ma bai dauki fatawarsa ba, idan ya dauki risalarsa ya lazimtu da aiki da abinda yake kunshe cikinta  ya wadatar cikin hakkakuwar taklidi.

Akwai cigaba da yardar Allah.


Tura tambaya