lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU RABI’U AWWAL 1441 CIKIN BAYYANAR DA KARATU DA BOYE SHI Qum mai tsarki-Muntada Jabalu Amil Islami tareda Assayid Adil-Alawi

Lokaci: karfe 8 na safiya Fikhu, karfe 9 bahasin Usu.

Cigaba kan bahasin da ya gabata cikin bayyanar da karatu da boye shi: maganacikin mukami na hudu: cikin sallar Azuhur din ranar Juma’a, shin bayyanar da karatu wajibi ko kuma dai mustahabbi ne cikinta? Manya malamai sun yi sabani cikin haka Akaramakallahu Alhilli ya tafi kan mustahabbancin bayyanarwa cikin sallar juma’a da Magana mafi karfi.

An karbo daga Ibn Idris cikin littafin Assara’ir juz 1 sh 298 cewa ihtiyadi shine boyewabisa riko da ka’idar ishtigal sai dai cewa wannan Magana tana daga ratsatsts

iyar Magana barabuwa, mashhur sun tafi kan mustahabbancin bayyanarwa cikin Azuhur din ranar Juma’a bisa riko da jumlar riwayoyi; daga cikinsu akwai Sahihatu Muhammad Ibn Muslim.

عن أبي عبد الله عليه السلام قال لنا: صلوا في السّفر صلاة الجمعة جماعة بغير خطبة، وأجهروا بالقراءة، فقلت إنّه ينكر علينا المجهر بها في السّفر، فقال عليه السلام: إجهروا بها([1]).

An karbo daga Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi ya gaya mana: ku yi sallah cikin halin tafiya sallar juma’a ba tareda karanta huduba ba ku bayyanar da karatunta, sai nace za a yi inkarin bayyanarwar a kanmu a halin tafiya, sai Imam (a.s) yace: ku bayyanar da karatunta.

Daga cikinsu akwai hadisi da Marwan ya rawaito.

قال: سألت أبا عبد الله عليه السلام عن صلاة ظهر يوم الجمعة كيف نصليها في السّفر؟ فقال عليه السلام: تصليها في السفر ركعتين، والقراءة فيها جهراً.

Yace: na tambayi Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi dangane da sallar ranar juma’a yaya za mu sallaceta a halin tafiya? Sai amincin Allah ya tabbata agareshi yace: ku sallaceta raka’a biyu a halin tafiya sannan ku bayyanar da karatu.

ومنها: صحيحة عمران الحلبي: عن الرجل يصلي الجمعة أربع ركعات، أيجهر فيها بالقراءة؟ قال: نعم.

Daga cikinsu akwai Sahihatu Imrana Alhalabi: dangane da mutumin yayi sallar juma’a raka’a hudu sun zai bayyanar da karatu ne? sai yace: na’am.

Fuskar kafa hujja: zahiri daga hadisan da aka ambata a sama shie dora su kan kan ma’anar wajabci, sai dia cewa kuma malamai sun dauke hannu daga hakan sun tafi kan mustahabbanci sakamakon wasu fuskoki:

Daga cikinsu: kadai dai an dora ta kan mustahabbanci bisa tattaro tsakankanin hadisan a cikin Sahihatu Jamilu:

 سألت أبا عبد الله عليه السلام عن الجماعة يوم الجمعة في السّفر؟ فقال عليه السلام: يصنعون كما يصنعون في غير الجمعة في الظهر، ولا يجهر الإمام فيها بالقراءة، إنّما يجهر إذا كانت خطبة([2]). أي لو كانت صلاة الجمعة فيجهر بها.

Na tambayi Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi dangane da sallar jam’i ranar juma’a cikin halin tafiya?, sai Imam (a.s) yace: su yi kamar yanda suke a ranar da ba juma’a ba a sallar Azuhur, limami ba zai bayyanar da karatu ba, kadai dai yana bayyanar da karatu ne idan akwai huduba tareda ita.

 

وصحيحة محمد بن مسلم قال: سألت عن صلاة الجمعة في السفر، فقال: تصنعون كما تصنعون في الظهر ولا يجهر الإمام فيها بالقراءة، وإنّما يجهر إذا كانت خطية([3]).

Na tambayi Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi dangane da sallar juma’a a halin tafiya, sai yace: kuyi kamar yanda kuke a sallar Azuhur limami ba zai bayyanar da karatu ba cikinta, kadai dai zai bayyanar idan ta kasance tareda huduba.

Ana dora hani cikinta kan kore wajabci bisa dogaro da wajabtuwarsa cikin sallar juma’a kamar yanda ba’ari daga manyan malamai suka tafi a kai ko a dora shi kan kore karfafar mustahabbanci bisa mustahabbantuwarsa mai karfi cikin sallar juma’a.

Sai dai kuma cikin wannan fuska ya nufi rashin bayyanar kasantuwarsa daga jam’ul urfi dalali kamar dora Ammi kan Kassi ko da kuwa ya kasance tabarru’i  ya zama dole ya samo shaida, daga nan ne riko da zahirin nassoshi daga bangare na farko da suke shiryarwa da zahirinsu kan wajabci ya ayyana, kamar yanda malamai suka dogara kansu, amma hani cikin bangare na biyu daga nassoshi lallai ana dora su kan takiyya kamar yanda aka nakalto daga Shaik (K) kamar yanda yake ishara zuwa gareta cikin Sahihatu Muhammad Ibn Muslim ta farko cikin maganar mai tambaya

 (إنّه ينكر علينا الجهر بها في السّفر).

Za ayi inkari kanmu a halin tafiya.

Sannan Assayid Hakim (k) ya tafi da cewa tafiya kan wajabcin bayyanarwa mudlakan cikin sallar juma’a da sallar Azuhur da La’asar din ranakun Juma’a shine mafi zama ihtiyadi wujubi wand aba a barin aiki da shi idan ba a samu fatawa ba.

Daga cikinsu: kadai dai ana dora bangare na farko daga riwayoyin kan mustahabbanci koma bayan wajabci sakamakon shaida gamammiya da akai riko da ita cikin akasarin babin fikhu itace ka’idar (lau kana labana) da ya kasance da ya bayyanu a fili, hakika mas’alar yayin da ta kasance mahallin ibtila’in mukallafai cikin kowanne sati cikin sallar Azuhur a ranar Juma’a da bayyanar da karatu ya kasance wajibi da ya bayyanu ya yadu wurin kowa da kowa da kuma ya kasance daga sallamammun abubuwa a wurin shi’a da ba a samu sabani cikinsa ba, sai dai kuma ba haka bane ta kaka Mashhur suka tafi kan mustahabbanci kai bari dukkanin malamai ma sun tafi kan haka in banda Ibn Idris.

Kamar yanda Siratu Mutasharri’atu take shirywarwa kansa sakamakon abinda ya kasance ya kafu cikin kwakwalensu da cewa bayyanar da karatu cikin sallolin Azuhur da La’asar a ranar Juma’a kadai dai mustahabbi ne ba wajibi ba.

Wannan shine ra’ayin da babban malaminmu Assayid Ku’i (K) ya tafi a kai, lallai Siratul Mutasharri’atu ta tafi kan haka har ya zuwa zamanin da muke ciki, sannan an nakalto daga malaminsa Muhakkikul Na’ini (K) cikin mukamin aiki cewa ya kasance yana yin ihtiyadi a wasu lokutan ta hanyar maimaita sallar sai bayyana karatu da daya a dayar ya boye, domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Rashin wajabci ya bayyana ya kuma kasance wurin malamai daga sallamammen lamari d aka gama da shi, ta kai ga Ibn Idris ya sanya boyewa shine ihtiyadi a wurinsa, kamar yanda hakan bai buy aba da ace bayyanarwa shine yake wajabi ko kuma ana tsammanin wajabcinsa da ihtiyadi bai da wata ma’ana kamar yanda bai buy aba.

Idan aka ce: wannan fuska ta (lau kana labana) da Siratul mutasharri’atu da kansu suna gudana cikin sallar juma’a, ta kaka zaku zabi wajabcin bayyanarwa cikinta babu banbanci cikin kasantuwarsa da yanayin fatawa da mafi karfafa da bayyana cikin wajabci kuma kuka ki lazimtar mustahabbanci kamar yanda yake a mukamin.

Amsa zata kasance: lallai kiyasi a wurin da bai dace ayi shi ba, lallai sallar ba ta kasance ta yadu ba a jarrabtu da ita ba a zamaninsu amincin Allah ya kara tabbata a garesu sakamakon mulki da hukuma da tsayar da sallar juma’a na hannun Sarakunan zalunci, kamar yanda ta kasance a zamanin gaiba ba a tsayar da ita sakamakon sassabawar fatawowi cikinta daga wadanda suka tafi kan wajabci da kuma wanda suka haramta ta, ba ta kasance ibtila’in shi’a ba da har zata kai ga gudanar ka’idar (lau kana labana) sai ya zama zahirin nassoshin da suke umarni da bayyanarwa sun wanzu lafiya lau daga karina da shaida kan sabani, sabanin sallar Azuhur din ranar Juma’a wacce take mahallin ibtila’in dukkanin mukallafai, babu mafita sai dora nassoshin kan mustahabbanci kamar yanda hakan shine ra’ayinmu.

Amma abinda aka hakaito daga Ibn Idris da cewa mafi ihtiyadi shine boye karatu da kin bayyanarwa mudlakan cikin sallolin Juma’a da Azuhur a ranar juma’ar, da farko: rinjayarwa ne ga nassoshin hani yayin cin karo da juna, na biyu: karfafarsu da idlakokin boyewa cikin sallar yini, na uku: ka’idar ishtigal lallai bai kasance a muhallinsa ba, da farko dai: bayan gangarowar nassoshi masu yawa da suke nuni kan wajabci ko mustahabbanci a wurin malamai, na biyu: an nakalto ijma’I daga Shaik Dusi kan ingancin abinda suka kunsa.

Na uku: ka’idar ishtigal ga ilmul ijmali kadai dai daga asali take wanda ya kasance dalili a lokacin da babu dalili, abinda Ibn Idris ya fada zai kasance ratsatstsiyar Magana jefaffiya.

Assayidul Murtada ya tafi kan faifaicewa cikin mas’alar cikin sallar Azuhur din ranar Juma’a idna ta kasance cikin jam’i to limami zai bayyanar da karatu idan kuma ba jam’i bane sai a boye karatu bisa riko da riwayar Aliyu Ibn Jafar

علي بن جعفر قال: سألته عن رجل صلّى العيدين وحده والجمعة هل يجهر فيهما بالقراءة؟

قال: لا يجهر إلّا الإمام([4]).

Yace: na tambaye shi dangane da mutumin da ya sallaci sallolin idi guda biyu shi daya da juma’a shin zai bayyanar da karatu cikinsu? Sai yace: babu wanda yake bayyanar da karatu in banda limami.

Anyi masa ishkali: da farko dai isnadin riwayar yanada rauni lallai malamai basu yi aiki da ita ba, na biyu: ta ci karo da Sahihatu Alhalabi da ta gabata da take umarni da bayyanarwa tareda bayani karara daga mai tambaya da cewa yana sallah shi kadai, abinda yafi bayyanuwa shine tabbatar mustahabbanci cikin limami da wand ayake yi shi kadai duk da cewa boyewa cikin mai sallah shi kadai yafi zama ihtiyadi istihbabi. A lura.

 


([1]).الوسائل: باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأوّل.

([2]).الوسائل: باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثامن.

([3]).الوسائل: باب 73 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث التاسع.

([4]).الوسائل: باب 73 من أبواب القراءة الحديث العاشر.


Tura tambaya