lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h

Wuri: birnin Qum mai tsarki Muntada Jabalul Amil Islami tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi (h).

Lokaci: 8-9 na safe

Usul (60) 8 ga Jimada Awwal shekara 1442 hijiri.

Cigaba kan bahasin da ya gabata: cikin abin da Mawallafi Allah ya tsarkake sirrinsa ya fada: shi wada'u wani nau'in kebance lafazi da ma'ana da samar da dangantaka tsakaninsu, a wani lokaci hakan yana faru sakamakon kebantuwar wannan lafazi daga yawan amfani da shi cikin wannan ma'ana, a wani karon kuma sabid awani mutum guda ya kebantar da shi kan ayyananniyar ma'ana, da wannan ne ya inganta a kasa shi zuwa ta'ayini da ta'ayyuni kamar yanda hakan bai buya ba.

Ina cewa shi cikin al'amari na biyu cikin al'amuran da ya ambace su cikin wannan mukaddima Mawallafin ya gangara zuwa ga bayanin mukaddimar wada'in lafuzza ga ma'anoninsu gamammu da kebantattu ciki akwai fuskoki daga bahasi daga ciki akwai abin da bai da natija ta ilimi sai ya kaurace masa kamar misalin bahasi kan wanda ya sa fara wada'in lafuzza ga ma'anoni shi ne Allah matsarkaki kamar yanda aka danganta wannan magana zuwa ga Abu Hassan Ash'ari yana mai kafa hujja da fadin Allah maudakaki (kuma ya sanar da Adamu sunaye baki dayansu) ko kuma wand aya fara wada'in lafuzza ga ma'anoni shi ne mutum guda daya ko fiye da daya, ko kuma a cikin wasu ba'ari a wada'u muna bukatuwa garesu cikin tanbihi kan sanyawar Allah matsarkaki wasu kuma daga bangaren mutane, koma dai ya kasance abin da dai yake tabbace a larurance bayyanar da abin da yake kunshe cikin kirazan da zukata ya dogara na da magana wanda hakan ne ya haifar da wada'in lafuzza kan ma'anoni.

Mawallafin ya karkata ga bayanin kaifiyya wada'u da rabe-rabensa, lallai shi wada'u yana daga ma'noni na la'akari da suranta su da hankalto su da fahimtarsu ya dogara ne kan wasu ma'anoni na daban kamar misalin ilimi idna an la'akari da ma'abocinsa masani da kuma abin da aka sani din, shi wada'u yana dogara kan maudu'u wanda shi ne lafazi sannan ana kiran ma'anar da aka sanya lafazi domin cimma da sunan (maudu'u lahu) sannan wanda yake kallon dangantaka da alaka tsakanin lafazi da ma'ana ana kiransa da (wadi'u)

Sannan wada'u shin yana daga masdari ma'ana mujarradi afkuwa (hadasu) daga bangaren wadi'u ba tareda cudanyuwa da daya daga zamani uku da aiki yake afukuwa cikinsu ba ma'ana mazi da muzari'I da amri, ko kuma dai daga ismul masdar yake da kuma abin da yake samuwa daga wada'u daga fuskar wadi'u ko kuma wata hususiya ce da take samuwa tsakanin lafazi da ma'ana.

Ko muce: shin wada'u na nufin kebance lafazi da ma'ana har ya kasance daga siffa d atake tsaye da wadi'u ko kuma kebance lafazi da ma'ana sai ya kasance daga siffar lafazi.

Mawallafin yayi ta'arifin wada'u da cewa: shi kebance lafazi da ma'ana da wata dangantaka tsakaninsu d ata bubbugo daga kebance lafazin da ma'ana da kuma yawan amfani da shi cikin ma'anar.

Tushen dangantakar da alakar ya samu ne daga kebancewar daga ta hannun wadi'u kamar  misalin wada'in ruwa sunan ruwa kan kebantaccen wani abu mai kwarara sannan daga cikin abin da ya fifitu da shi shi ne baida launi bai da dandano, da kebancewar wadi'u ne da karfaffar dangantaka zurfaffa tsakanin lafazi da ma'ana da kuma yawan aiki da shi cikin ma'ana a wani karon kamar misalin wada'in lafazin kan sallar da muke yi wacce a da a luggance ya kasance da ma'anar addu'a, lallai ba tareda sanya wata karina da shaida ba ana amfani da lafazin sallah kuma ana fahimtar sallah ta yau da ake yi ba sakamakon yawan aiki da lafazin cikin wannan ma'ana, da wannan ma'ana ne ya inganta a kasa wada'u zuwa ga ta'ayini wanda yake samuwa ta hanyar wadi'u da kuma ta'ayyuni wanda yake samuwa sakamakon yawan aiki da lafazi cikin wata ayyananniyar ma'ana , idan wada'u ya kasance daga fuskar kebance shi ba daga kebantuwarsa da kansa ba, lallai hakan zai lazimta rashin halascin rarraba shi kai kace abin da Mawallafin yake nufi da inganci da halascin rarraba shi da yake kafa dalili kansa ya kuma ke goyan bayan abin da ya tafi kansa cikin wada'u shi ne dangantaka tsakanin lafazi da ma'ana yana daga kebantuwar lafazi da kankin kansa bawai daga kebancewar mai kebancewa ba, sannann cikinn wannan mukami akwai maganganu da yawa da ra'yoyi daban daban daga wasu Jumla daga manya manyan Malamai, hakika a baya mun danyi ishara zuwa ga abin da Almuhakkikul Komfani ya fada da kuma ishkalin da Mawallafi ya gangarar a kansa.

Za mu cigaba cikin magana ta uku a wannan mukami.  

Tura tambaya