lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya

Mukaddima

 

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yake shafe abin da ya so ya kuma tabbatar da abin da ya so kuma gurin sa uwar littafi take, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittun sa shugaban manzanni Muhammad da iyalansa ma'asumai, dawwamammiyar na tsinuwa ta tabbata kan makiyan su har zuwa tashin kiyama.

Ya ubangiji ka buda bakini da da fadin shiriya ka kuma kimsa mini tsoran ka.

Bayan haka; hakika matsarkaki madaukaki yace: 

 (وَلا تَقْفُ ما لَيْسَ لَکَ بِهِ عِلْمٌ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُوادَ كُلُّ أُولئِکَ كانَ عَنْهُ مَسْوُلاً)[2] .

Ka da ka bibiyi abin da baka da sani kansa hakika ji da gani da zuciya dukkanin su ababen tambaya ne.

Lallai daga ciki kage da tuhume-tuhume da ake likawa shi'a da shi'anci daga fuskanin makiyan su, musammam ma mabiya makarantar Umayyawa yaran Ibn Taimiya, cewa shi'a sun yi imani da Bada'u ma'anarsa shi ne danganta jahilci ga Allah, lallai Allah ya tsarkaka daga haka, abin da `yan shi'a suke fadi yana lazimta kafirci da da bata.

Batun yaran Ibn Taimiya a takaice shine komar da Bada'au zuw aga jahilci da nadama wanda hakan ya koru ga barin sa matsarkaki, sannan takaitacciyar amsa: lallai Bada'u da wannan ma'ana da suke bashi babu shakka yana kasancewa daga kafirci da bata, sai dai kuma shi Bada'u a fahimtar makarantar Ahlil-baiti (as) yana da ma'anar kebantacciyar bayyanuw, abinda abokan rigima ke fadi yana komawa ne ga kuskurarriyar fahimtar su, hakan na kasancewa idan mun yi nufin kyautata musu zato, idan ba haka to lallai batun sun a daga karya da kage wanda ya samo asali daga binnanniyar kiyayya da take zukatan su tun lokacin da suka sunnan ta zagin Sarkin muminai (as) kan mimbarorin su da kashe shugaban shahidai da iyalan sa a ranar Ashura, (babu wani mutum daga garemu face kasashshe ko kuma wanda aka shayar da shi guba)hakan ba komai bane face matsananciyar kiyayya da yaudara da munafunci da tsabar neman rigima da kafirci, da zaluntar Ahlil-baiti da kwace hakkokin su bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w)

Amma bayani filla-filla da sanin tambaya da amsa lallai yana lazimta fara bayyana wasu ala'amura:

Na farko: abin da abokin dauki ba dadi yake fadi kan batacciyar Bada'u.

Na biyu: Bada'u a luggance da isdilhance.

Na uku: Bada'u a makarantar Ahlil-baiti da mabiyan su daga malamai da manyan masana.

Na hudu: hujjojin imamiya kan Bada'u wanda ya dace da hankali.

Na biyar: Bada'u karkashin hasken kur'ani da Ahlil-baiti.

Na shida: natijar imani da Bada'u

Na bakwai: tambayoyi tare da amsa kan imani da Bada'u

Katima: takaice bahasi.

Ba buya ba cewa maudu'in Bada'u ana kirga shi daga mas'aloli da aka buga jayayya kansa a ilimin tauhdi, wanda kansa aka bijiro da bahasi mai fadin gaske tsakanin malaman ilimin tauhidi tun farkon karnin fark, sabanin a wancan zamani cikin mas'alolin ilimin tauhidi, ana kirga Bada'u daga larurar mazhabar imamiya isna ashariya, kamar yanda yake bayyana daga hadisai da suka kan wannan mukami, sai dai cewa ba kamar yanda abokan rigima suke tunani da suranta shi ba ko kuma mu ce yanda suke sharara karya da kage kan shi'a, lallai Bada'u idan ya kasance da ma'anar sauya ra'ayi wanda haka ya bubbugo daga jahilci da nadama, to lallai wannan ba zai taba yiwuwa ba har abada kan hakkin sa madaukaki matsarkaki, imamiya basu tafi kan wannan ma'ana basu yi imani da ita  ba ta kowacce irin fuska, bari imamiya sun tafi kan cewa hakan ba zai taba sabuwa ba har abada kuma hakan kafirci ne duk wanda yayi imani da wannan ma'ana kafiri ne, kuma wajibi a barranata daga gareshi domin shi lallai batace ne mai batarwa.

Idan Bada'u ya kasance da maanar sa wacce hanakali ya ke karba- da sannu zai bayyana-wanda wajibi imani da shi, shine wanda aya mai albarka ta bayyana shi da :

(يَمْحُوا اللهُ ما يَشاءُ وَيُثْبِتُ وَعِنْدَهُ أُمُّ الْكِتابِ )[3] ،

Allah yana shafe abin da ya so ya tabbatar da abin da ya so wurin sa uwar littafi take.

Wannan da ma'anar sa ta lugga kenan daga mudalakin bayyanuw, da kuma ma'anar sa a isdilahance daga kebantacce bayyanuwa.

Wanan shafewa da tabbatarwa yana tajalli cikin abin da Allah yake bayyanarwa kan harshen Annabin sa ko waliyin sa da wasiyin sa cikin zahirin hali sakamakon maslaha da take hukunta bayyanar da shi, sannan ya shafe shi, sai ya zama ya sauya abin da ya bayyanar, tare da gabatar sanin sa madaukaki.

Wannan shi ne Bada'u cikin kasantattu wand ayake kama da nasaki cikin nassosin shari'a, lallai Bada'u na hankali yana kama da nasakin hukunce-hukuncen shari'a d ata gabata da sabuwar shari'ar Annabin mu Muhammad (s.a.w) ko kuma muce yana kama da nasakin ba'arin hukuncehukunce da shari'ar Annabin  mu (s.a.w) ta zo da ita kamar misalin sallah ana halin karkata zuwa masallacin baitul mukaddar matsayin akibla, wanda daga baya akai nasakin sa da juyowa zuwa ga dakin Ka'aba mai daraja.

Sannan shi'a ba su yi imani da irin wannan Bada'u da nasakin ba, hakika hakan na nuna iyakance ikon Allah da iradar sa da basu da kaidi da dabaibaiyi, kamar yanda kur'ani mia gima yayi ishara zuw aga haka cikin jumlar daga akidojin Yahudawa cikin fadin sa madaukaki  

 (وَقالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللهِ مَغْلُولَةٌ غُلَّتْ أَيْديهِمْ وَلُعِنُوا بِما قالُوا)[4]

Yahudawa suka ce hannun Allah kulle yake Allah ya daure hannayen su ya kuma tsine musu bisa abin da suka fada.

Wannan abin da ya sadada zuwa cikin akidun wasu kungiyoyin muslunci wadanda ba Imamiya ba,[1] a lura sosai

Sannan babu abinda ya rage mana face tsunduma cikin maudu'I kamar yanda muka tsara cikin mukaddima daga bayanin al'amura bakwai da Katima mda yardar Allah, daga Allah muke neman dacewa da damdagatar.

Akwai cigaba


[1] Mun ciro daga littafin Aka'idul imamiya na Shaik Rida Muzaffar sh 45-46.


Tura tambaya