lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

mafhumin addini

 

Kalmar addini tanada ma'anoni masu tarin yawa a cikin lugga daga cikinsu akwai: al'ada da sha'ani da sakamako da sakawa da da'a da muslunci.

Amma cikin isdilahi: lallai Kalmar (addini) na nufin wasu tarin adadin akidu da umarnoni da koyarwar  Akhlak wadanda Allah subhanahu wata'ala ya aiko su zuwa ga mutane ta hanyar annabawansa da manzanninsa, ga dukkanin abin da za a iya la'akari da shi a matsayin addini aikakke daga Allah madaukaki zuwa ga mutane wasu adadin kwafi, sannan kwafi na karshe shi ne addinin muslunci mabayyani wanda aka aiko da shi ta hanyar shugabanmu Muhammad bn Abdullah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da iyalansa tsarkaka.

B) larurar samar da hukuma da rashinta:

Da sannu cikin wannan juzu'I daga wannan littafi za mu fara bahasin dalilai kebantattu kan larurar samar da hukuma da wadancan abubuwa da suka ratayu da ita da masu sabani da samar da ita.

1- dalilai kan samar da hukuma

Daidaikun mutane tun farko faruwar tarihi sun al'adantu kan rayuwa da tsarin jama'a jama'a ta yanda rayuwar zamantakewa da mutuntaka ta fara da na farko mafi kankantar taron jama'a abin da muke nufi d ahaka shi ne iyali guda daya sannan suka fadada domin haifar da taro jama'a-jama'a mafi girma da adadi kamar kabila da alkarya sannan daula sannan yanki (continent) haka dai zuwa dauloli.

Mutum ya kasance bai kuma gushe ba har yanzu yana fifita rayuwa cikin jama'a maimakon rayuwa shi kadai da dayantuwa da kadaita, hakan ya faru ne sakamakon jingunuwa da larurar hankali da zabinsa na hankali domin riskarsa da cewa lallai shi bai da iko amsa dukkanin bukatunsa na madiya da ma'anawiya yana halin nesantuwa daga rayuwa cikin jama'a.

Bayyananne abu ne rayuwa ta kasance ta zamatakewa mabanbanciya da shakali mai girma daga rayuwar kadaita ta yanda rayuwar zamantakewa ke siffantuwa ga mutum da wasu ba'arin wajibai da abin da larura ke hukuntawa, sai dai cewa tare da haka rayuwa zamantakewa tana da tata matsalar a kebance da ta kebantu da ita da kuma wahalhalu masu tarin yawa da tuba-tubai wadanda ba a samunsu cikin rayuwar kadaituwa, tare da rashin kubutar ta daga adadin alfanoni da fifiko masu yawan gaske, sai dai cewa sakamakon kasantuwar rayuwar zamantakewa da juna ta fifitu kan `yar'uwarta ta kadaituwa hakika wasu ba'rin daidaikun mutane sun zabarwa kawukansu wannan nau'i daga rayuwa, lallai tilas ne a himmatu da abubuwan da wannan rayuwa ta ke lazimtarwa da abubuwa da take hukuntawa, da daukar kebantattu matakai da natijojinsu da karshensu.

Cikin abin da zai zo da sannu za mu yi ishara da nuni zuwa ba'arin wasu abubuwa da rayuwar zamantakewa da juna take hukuntawa, za kuma mu tunatar kan mas'alar larurar samar da hukuma da abin da yake dacewa da dukkanin daya daga wadancan abubuwan da ta hukunta

Cin karo da junan maslahohi:

Ana la’akari da maudu’in cin karo da junan masalahohi cikin amfani daga baiwowi da akai tarayya cikinsu samammu cikin wasu jama’a matsayin daya daga lazimai da suke shakkala rayuwar zamantakewar juna, tare da lura da sassabawar daidaikun bil adam sashensu ga sashe da hukuncin larura ta fuskanin halitta da dabi’u da al’adu da ahasis da karkata da kwadaye-kwadaye da halaye, daga cikin abin da babu shakka da kokwanto cikinsa shi ne lallai wadancan sassabawar da sannu zata tuke da dabi’ar yana yi zuwa ga sassabawar haduffa da burace-burace, sannan sassabar cikin aiki da tasarrafi abin da ke karkarewa zuwa ga bayyanar adadin fuskokin cin karo da juna na ilimi cikin al’umma.

Domin warware wadancan sabanunnuka da matsalolin cin karo da juna cikin al’umma, babu maguda gaban daidaikun al’umma daga sanya adadin dokoki da ka’idoji domin baki dayansu su samu damar amfanuwa da tanadi da suke da shi da yana yi mafi dacewa da kuma daidaito.

Tura tambaya