lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Imam Aliyul Hadi (as) a cikin tsakiyar Zakuna

A zamanin Halifan Abbasiywa Almutawakkil an yi wata mata da ta yi da’aar cewa itace Zainab diyar Sarkin muminai Aliyu bn Abu Dalib (as) sai ta dinga karba kudade daga hannun mutane sai aka kamota aka kawota wurin Halifa Almutawakkil sai yace mata: ke gaki budurwa matashiya ki san kuma zamanin Manzon Allah (s.a.w) ya jima da shudewa tsahon shekaru, sai tace: hakika Manzon Allah (s.a.w) ya shafa kaina ya kuma roki Allah da ya dawo mini da yarintata da budurcina cikin bayan dukkanin shekaru arba’in ba bayyana gaban idon mutane ba har zuwan wannan lokaci sai dia cewa bukata ta tilastani ga bayyana wannan lokaci, sai Almutawakkil ya kirawo wasu shehunai daga dangin Abu Dalib da Abbas da Kuraishawa yayi musu bayanin wannan mata sai wasu ba’ari daga cikinsu suka ce: an rawaito cewa Sayyada Zainab (as) ta bar duniya a shekara kaza, sai Almutawakkil yace mata me zaki gameda wannan riwaya? Sai tace: wannan karya ce ziryan hakika al’amarina ya kasance boyayye daga barin idanun mutane babu wanda ya san rayuwata ko mutuwa, sai Almutawakkil yace musu: shin banda wannan riwaya kuna da wani dalili ko hujja kan wannan mata?

Sai suka ce: babu wani dalili da ya rage mana amma abinda yafi dacewa shine ka kirawo `dan gida Aliyul Rida (as) ta yiwu a samu wani abu daga hujja daga gareshi sabanin abinda yake hannunmu, sai ya aika a kira masa Imam Hadi (as) sai ya hallara ya zo sai suka bashi labarin da’awar da wannan mata take yi, sai Imam (as) yace: karya take hakika Sayyada Zainab ta bar duniya a shekara kaza a wata kaza a rana kaza.

Sai Almutawakkil yace: ai duk sun gaya mata hakasai dai cewa bata karbi riwayar ba ni kuma na rantse ba zan dauki mataki kanta face da hujja da zata lazimce ta.

Sai Imam (AS) yace: muna da hujja da zata lazimce ta ta kuma lazimci wanin ta, sai Almutawakkil yace: tana ina hujjja?

Sai Imam (as) yace: naman `ya`yan Fatima ya haramtyu ga Zakuna ka jefa cikin Zakuna idna tabbas ya kasance daga `ya`yan Fatima babu abinda Zakuna za su yi mata, sai Almutawakkil yace: me zaki kan wannan Magana? Sai tace yana son kasheni ni kawai.

Sai Imam (as) yace: anan wurin akwai jinin Fatima daga `ya`yan Hassan da Husaini (as) ka jefa duk wanda kake daga cikinsu, yace: wallahi fuskokin kowa da kowa sai da suka canja wasu ba’arin makiya Imam (as) suka ce to me zai hana shi da kansa ya shiga keji Zakunan maimakon dora shigar kan wuyan wasunsa? Sai Almutawakkil ya karbi wannan shawara da ra’ayi sakamakon cewa dama can yana neman hanyar da zia halaka Imam (as) ta yanda ba za a tuhume shi ba! Sai ya cewa Imam (as) me zai hana kai da kanka ka shiga? Sai Imam (as) ka samu hakan babu matsala, sai Almutawakkil yace: ka yi hakan ka shiga kawai.

Imam (as) ya shiga kejin wannan Zakuna wadanda suka kasance guda shida  sai suka tsaya kewaye da shi suka mikar da hannayensu kan kasa suka dora kawukansu kan hannayensu, sai Imam (as) ya dinga shafa kansu yayi musu ishara da su tsaya a gefe guda sai suka tsaya.

Sai daya daga ministocin Almutawakkil yace masa wannan abinda kake yana da hatsari kayi sauri ka fitar da shi tun kafin labarinsa ya yadu a gari ya bazu, sai Almutawakkil ya nemi Imam (as) da ya fito sai wannan Zakuna suka kewaye shi suna goga jikunsu jikin rigarsa sai Imam (as) ya dora kafarsa kan matattakala tsani ya umarci wadannan Zakuna su koma inda suke sai suka koma Imam (as) ya fito sai Almutawakkil yace: sauko.

Sai wannan mata tace Allah! Allah! Hakika na yi da’awar karya da cewa ni diyar wane ce, saboda haka yanzu ka dauki matakin kaina bisa abinda na fada. Sai Almutawakkil yace: ka wurga ta cikin Zakuna, sai dai cewa mahaifiyarsa ta nemi yayi mata kyautar ta.     

Tura tambaya