lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

falsafa da siyasa a cikin muslunci kashi na farko

Darasi na farko: mafhumai da mas'aloli masu gamewa

Cikin wannan darasi:

1-ta'arifi na lugga da isdilahi ga mafhumin siyasa;

2-gabatar da sura bayyananniya daga fagen dirasosin falsafa cikin muslunci;

Tabbatar larura samar da hukuma;

3-sanin dalilan masu inkarin samar da hukuma da gabatar da gamsassun amsoshi gare su.

Gabanin bijiro da bahasosi mafi muhimmanci cikin fagen falsafar siyasar muslunci, ya kama ce mu mu yi dan takaitaccen karin bayani gameda mafhumin ba'arin wasu isdilahohida mufradat muhimmai cikin fagen da muka ambata a sama tare da lura da dandakewa, sannan mu yi kokarin tabbatar da samar da hukuma tare da kallon abubuwa da rayuwar zamantakewa ke lazimtarwa da hukuntawa, daga karshe za mu kawo ra'ayoyi masu inkarin kafa hukuma sannan za mu yi bahasi kansu da kuma kalubalantarsu.

A) mafhumai

Cikin abin da zai zo za mu yi bakin kokarinmu wajen yin karin bayani kan mafhuman siyasa da falsafa cikin muslunci da addini ta yana yi na bayani filla-filla

1-mafhumin siyasa:

Siyasa (policy) a luggance tana nufin tafiyarwa da maslaha da nisan nazari da gadi da kiyayewa kan mulki, da bada kariya da inaya da gadi da hukuncin wadanda ake mulka da hukuma da shugabanci da Alkalanci, hakama tana nufin azabtarwa da azaba da ukuba.

Ibn Manzur cikin littafinsa (lisanul Arab) yana cewa:

«و السِّياسةُ: القيامُ على الشّيءِ بما يُصْلِحه؛ و السياسةُ: فِعْلُ السّائِس، يُقال: هو يَسُوسُ الدّوابَّ، إِذا قامَ عَليها و راضَها، و الوالي يَسُوسُ رَعِيَّتَه»[1].

Siyasa shi ne tsayuwa kan abu da abin da zai gyara shi;

Ita siyasa itace aikin dan siyasa,

Ana cewa: shi yana jagoranta dabbobi idan ya tsayu kansu ya rene su.

Shugaba yana jagorantar wanda yake shugabantarsu.

Amma cikin isdilahi, lallai ita siyasa tanada kebantaccen mafhumi, daga cikinsa akwai tafiyarwa da gudanarwa wacce hukuma ke dauka domin zartar da al'amuran gari da iyakance nishadinta, ta yanda wadancan tafiyarwar da gudanarwa da tsaretsare sun kasu zuwa nau'i biyu: na ciki da na waje.

Ya kamata a wannan wuri mu yi ishara da cewa ita fa siyasa bata nuni zuwa ga kowanne mafhumi ko ma'ana mara kyawu a cikin lugga ko a cikin isdilahi, sai dai cewa sakamakon tasarrufi na kuskure da ayyuka na wauta da wasu `yan {siyasa} suka aikata kuma basu gushe ba suna yi, sai Kalmar siyasa ta rinu da rini mara kyau da wasu ma'anoni, hatta cikin sakafar muslunci lallai mu bamu ga wani kufai ga zargin siyasa ko la'akari da ita matsayin abin zargi, tuntuni tun dcan ake danganta siyasa zuwa ga imamai amincin Allah ya kara tabbata gare su, cikin wasu abubuwa da wadannan imamai ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata a gare su suka cancance su.

Alal misali, wannan jumla ta zo    

«ساسَةُ العِبادِ و أَرْكانِ البِلادِ»

Shugabannin bayi sune rukunan gari.

Hakama ya zo cikin ziyara madaukakiya sananniya wacce aka fi sani da sunan (Ziyaratu Aljami'a) wacce ma'anarta kamar yadda yake bayyane shi ne

 (قادة العباد السياسيّين).

Jagororin mutane sune `yan siyasa.

Haka dai, lallai abin da kae nufi da Kalmar (siyasa) cikin waccan ziyara madaukakiya ba shi ne tafiyar da al'amura ba da sha'anin kasa da mutane ta hanyar wayo da yaudara da makirci da dasisoshi ba, bari abin nufi shi ne uslubin gudanar da kasa da hanyar saukake sha'anonin mutane, da kalma mafi dandakewa za mu iya cewa: lallaiita siyasa cikin bahasinmu wannan tana nufin gudanar da al'amura jama'a da shakali cikinsa akwai lamincin maslahohi daga abin da ke cikinta daga mada da ma'anawiyya.

2-mafhumin falsafa da siyasa cikin muslunci:

Falsafar siyasa ya tattaro bahasi da bayani muhimman mas'aloli da suka kebanci jama'a da hukuma da daula da tafiyar da kasa da rayuwa da zamantakewar al'umma da hakkokin daidaiku da wajiban daidaiku da jama'a kishiyar kowanne daga cikinsu, kamar yanda falsafar siyasa take bahasin maudu'ai muhimmai daban misalin dokoki da adalci da dukiya da sarauta da hukuma.

Ana misalta tambayar mai cewa: wane ne yafi cancanta da hukuma?

Da tambaya ta asasi da tushe cikin kashin bayan falsafar siyasa sai dai cewa ilimin siyasa bai bada wani muhimmanci ga misalin wadannan tambayoyi yana takaita bahasinsa cikin wadannan maudu'ai kan falasafar ilimin siyasa kadai.

Ana bijiro da wasu tambayoyi cikin falsafar siyasa da suke da muhimmanci mai girma wadanda suke bayyana asasin bahasosin siyasa, hakika ma'abota tunani sun yi bakin kokari a tsawon tarihi cikin ba da amsar wadancan tambayoyi, daga cikin jumlar amsoshin akwai:

-shin ana la'akari da hukuma matsayin larura cikin al'ummun mutane?

-idan ya kasance haka ne, to wane ne shugaba ko sarki da ya fi cancantuwa da wannan mukami mene ne siffofin da ya siffantu da su?

Mene ne mafi falalar nau'o'in hukunci ko hukuma?

Wannan ne hali tare da falsafar muslunci ta yanda take tsayuwa kan yin bayani da karin bayani kan masl'aloli muhimmai cikin fagen siyasa, sai dai cewa tushen wadancan bahasosi da ma'aunansu an ciro su ne  daga asalan muslunci da koyarwar addinin muslunci mai karkata zuwa ga shiriya, kuma kansa ne, sannan uslubi da hanya da ake bi cikin falsafar siyasar muslunci shi ne hanyar hankali, sai dai cewa ya kamata hankali ya kasance hankali mai lazimta da za amfani da shi cikin kewayen asalai da ka'idojin muslunci masu gamewa domin ya kasance mafi cancanta da haifar da tunani da lura.

Idan ya zamanto haka, to lallai musluntakar falsafa na boye cikin kasantuwar muslunci shi ne wanda yake ajiye dokoki da farillu wadanda asasin ke cika kan shiga bahasosin falsafar siyasa, ya yin da aka ce lallai hanyar falsafar siyasa  shi ne hanyar hankali bai nufin cewa hankali shi ne ke yin tunani da haifar da tunanunnuka ba tare da jingina da kowanne ma'auni ba ko ayyananniyar doka ba, bari dai abin da ake nufi shi ne lallai shi hankali cikin falsafar siyasar muslunci hankali mai lazimta ba zai yiwu ya fita daga zuciyar falsafar siyasa ba domin tukewa ga rashi ko  rashintuwa wacce ake kira da (Nihilism) hankali mai lazimta shi ne hankalin da ke misalta (Anthrophology) ilimin ma'arifa da ilimin halittu da ya bubbugo daga addinin muslunci mabayyani.


[1] ‌ابن ‌منظور، محمد ‌بن ‌مكرم، لسان ‌العرب، ج 6، ص 429.

Tura tambaya