lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

DAGA CIKIN SIRRIKAN TARON MINA

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah ubangiji talikai tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa zababbu tsarkaka.

Bayan haka:

1-cikin rana ta goma ga watan zul hijja mahajjata za su shiga mina wanda wani kwazzzabo ne tsakanin kwazazzabon Muhassar abayan mash'arul haram tsakanin Makka na da nisan kilomita 6  tsakankanin manyan duwatsu biyu wadanda haddin tsayinsu ya kai mita dari biyar da fadi- domin jifan Jamarat Akaba (Shaidan mafi girma) sannan kuma a gabatar da abin hadaya a yanka sannan daga baya a yi aski sannan mahajjaci  zai wanzu a Mina har zuwa rana ta 12 a wani fadin har zuwa rana ta 13, a mina zai dinga kwana a nan ne zai yi jifan Shaidanu karo uku ma'ana rana ta 11 zuwa ta 12 ta yiwu ya kai ta 13 ga wanda ya zauna har darensa.

2-an kiraye ta da suna Mina saboda Allah matsarkaki yayin da ya gafartawa Adamu (as) ya san abin da ya sani a Arafat ya nemi kusnaci daga ubangijinsa a Muzdalifa, sai ya nemi Adamu ya yi burin wani abu daga gareshi, sai Jibrilu ya sauko ya cewa Adamu ka yi buri daga Allah, sai Adamu ya ce: mai zanyi buri? Sai Jibrilu ya ce masa aljanna, sai ya nemi aljanna, Allah ya amsa masa.

 عن الصادق  7: إن جبرئيل  7 أتى ابراهيم  7 فقال له تمنّ يا إبراهيم وكانت أمنيته أن يبدل ذبح اسماعيل بكبش ، فأجابه الله سبحانه .

3-daga Imam Sadik (as) lalle Jibrilu ya je wajen Ibrahim (as) sai ya ce masa: ya Ibrahim ka yi buri burin Ibrahim ya kasance canja yankan dansa Isma'il da rago, sai Allah ya amsa masa wannan buri nasa ya sauya masa da rago.

4- ana kiranta da Mina sakamakon jinin abin hadaya da ke kwarara cikinta.

5 a kasar Mina tsarkakka ake jifa uku na shaidanu( SugraWusda,Kubra ) a cikin akwai Maslak da masallacin Haifa wanda Annabawa dari bakwai su ka yi sallah cikinsa, ana kiransa da Haifa kasantuwarsa a saman dutse ko kuma daukakarsa daga ban kasa.

6- daga cikin sirrikan Mina shi ne lalle hannun Allah na tare da jama'a adadin mai tarin yawa na yin tajalli cikin taron mahajjata a Arafat ya zuwa Mash'arul haram sannan daga nan su kwarara zuwa Mina cikin wannan dubun dubata jama'a ake mantawa da fadin ni ni ya zuwa fadin mu mu, zamu kasance kamar igiyar ruwa da faila cikin gangarowarmu da kwararmu tare da mutane, domin mu tabbatar da fatanmu da burace buracenmu cikin tsarkakakkiyar kasa:

 (ثُمَّ أَفِيضُوا مِنْ حَيْثُ أَفَاضَ آلنَّاسُ وَآسْتَغْفِرُوا آللهَ إِنَّ آللهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ * فَإِذَا قَضَيْتُمْ مَنَاسِكَكُمْ فَاذْكُرُوا آللهَ كَذِكْرِكُمْ آبَاءَكُمْ أَوْ أَشَدَّ ذِكْراً فَمِنَ آلنَّاسِ مَن يَقُولُ رَبَّنَا آتِنَا فِي آلدُّنْيَا وَمَا لَهُ فِي آلآخِرَةِ مِنْ خَلاَقٍ[1])

Sannan ku kwararo ta inda mutane suke kwarara ku nemi gafarar Allah lalle Allah mai gafara ne da rahama* idan kuka kammala ibadarku ku ambaci Allah kamar yadda kuke Ambato mahaifanku ku kuma mafi tsanani daga haka, daga cikin mutane akwai wanda ke cewa ya ubangijina ka bani cikin duniya bai da wani rabo a lahira.

ونقول : (رَبَّنَا آتِنَا فِي آلدُّنْيَا حَسَنَةً وَفِي آلاْخِرَةِ حَسَنَةً وَقِنَا عَذَابَ آلنَّارِ). [2]

Mu kuma muna cewa: ya ubangijinmu ka bamu kyakkyawa a duniya ka bamu da kyakkyawa da lahira ka tsare mu daga azabar lahira.

7- Mina kasar zikirin Allah: mushrikai zamanin jahiliya ta farko sun kasance suna masu alfahari da iyayensu da kakanninsu cikin kwanakin tashrik, ma'ana kwanakin (11,12,13 daga Zul hijja) a Mina, sai Allah ya umarci musulmai da su bar wannan al'ada su yi zikirin Allah na yin hakan kamar yadda suke ambaton iyayensu ko mafi tsanani daga haka, daga cikin zikiri a Mina akwai jifan Jamarat Akaba a ranar idi kamar yadda ya zo cikin hadisi fadin wannan zikiri:

 (الله أكبر، الله أكبر، لا إله إلّا الله، والله أكبر، وله الحمد، الله أكبر على ما هدانا، الله أكبر على ما رزقنا من بهيمة الأنعام )[3]

 Maimaita wannan kabarbari bayan sallolin mina.

8- Mina kasar sabuwar haihuwa, hakika ya zo cikin hadisai masu daraja yayin fitowa mahajjaci daga Mina lalle za a yafe masa dukkanin zunubansa ya wayi gari kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifeshi, sai ya ake sabbin aiki da da'ar Allah da manzonsa da Imamai tsarkaka.

9- Mina mahalli ne na neman rahamar Allah da kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, bayan ya ambaci Allah da yawa cikin Arafat da Mash'arul haram, lalle zuciyarsa zata nutsu sai ya dan zauna a Mina tsawon kwanaki uku sai ya fita da cikinta gabanin faduwar rana idan ya tsaya har rana ta fadi to ya zama tilas kansa ya yi jifan jamarat rana ta sha uku.

10- Mina kasar burace burace na hakika da gasagata wanda kekawo azurta duniya da lahira, lalle Allah ya yiwa Adamu lamini aljanna. Ita aljanna gidan aminci ne da arziki 

(أمّا الذين سعدوا ففي الجنّة )

Amma wadanda suka azurta suna aljanna.

Sannan banbantar burace burace na biye da banbantar martabobi da imani da ilimi da sakafa, daga cikin mutane akwai wanda ke burin duniya da tarkacenta, daga cikinsu akwai mai burin lahira da ni'imomonta.

11- Mina kasar tabbatar da burace burace na hakika, lalle mutum yana son dawwama hakan bai tabbatuwa face cikin aljanna, mumini ma'abocin hanakali da hikima yana burin Allah cikin kasar Mina da ni'imominta, shi mumini bai burin burace buracen karya da tatsuniya wadda suka ginu kan rudu da wahami


[1] Bakara:199-200

[2] Bakara:201

[3] Kafi:juz 4 sh 516

Tura tambaya