lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

TUFA barbeloli masu yawan gaske sun sauka kan wata qatuwar bishiya, sannan iskar ta kasance iskar kak

 

TUFA

barbeloli masu yawan gaske sun sauka kan wata qatuwar bishiya, sannan iskar ta kasance iskar kaka, iskar asubahi mai sanyi na karkaxawa . wasu adadi daga abokai da sanannun fuskoki sun kasance baqi cikin gidan Imam Rida (a.s) imam ya fto waje daga cikin xakin baqi.

Lokacin da ya taka qafarsa a farfajiyar gidan sai ya ji sautin qarar `ya`yan tsuntsaye, sai ya xaga kansa ya kalli rufin farfajiyar, tswan lokacin wannan `ya`yan tsuntsaye suna kan rufin katakon farfajiya sannan sun kafa shek.

Imam Rida (a.s) duk lokacin da ya gifta ta wannan sheka sai ya xaga kansa sama ya kalle su yayi farin ciki , yace yanzu sun qara girma xan kaxan, Imam sai a ga mahaifiyar wannan tsuntsaye ta dawo ta sauka kan wannan sheka `ya`yanta na cikin halin yunwa sai ta buxe bakinta ta sanya abinci cikin bakin xayansu, sannan ta qara tashi sama.

Imam (a.s) yayi murmushi ya shiga farfajiya yayi alwala, lokacin da yake dawowa sai ya hango wani abu a loko, sai ya xan tsaya ya faxa cikin mamaki kan abinda ya gani, daga baya sai ya xan qara gaba ya xauke wannan abun, ransa yayi matuqar vaci ta kai ga ya girgiza kansa saboda tsananin takaicin abinda ya gani sannan ya zauna saman matattakalar rufin, baqin da suke jiran dawowar Imam (a.s) sai suka shiga cikin damuwa sakamakon jinkiri, xaya daga cikin masoyan Imam (a.s) ya fuskanci abinda yake faruwa, sai ya fito waje yace ya farincikina! Me ya sanya ba zaka shigo ciki ba?

Imam (as.) yayi masa shiru,  sai mutumin ya matso gaba ya xaga kansa ya kalli fuskar Imam (a.s) ya qara cewa: farincikina! Shin wani abu ya vata maka rai ne? sai Imam ya nuna wata guntuwar tufa da aka ci rabinta aka yar da take hannunsa yace: wane ne yaci wannan tufar haka? sai wannan mutumi ya xaga sautinsa yana cewa: wanne mutum ne yayiwa wannan tufar irin wannan cin? Baqi suka fiffito daga cikin xaki, wannan mutum ya karvi wannan tufa daga hannun Imam ya qara maimaiata tambayar da yayi yace: wane ne yaci wannan tufar?

Xaya daga cikinsu ya xora hannunsa kan qirjinsa yace: ya shugabana ina neamn uzurinka. Amma nine na ci wannan tufar, Imam (a.s) ya tashi daga inda yake ya miqe tsaye ya waiwaye shi yace: me yasa kake almubazzaranci. Me yasa baka girmama ni'imar ubangijinka kake ko unkula da ita?shin baka san cewa ubangiji yana tsananta azabarsa kan almubazzarai ba?

Sai wannan mutumi ya qara xora hannunsa kan qirji ya qara nemana uzuri daga wurin Imam.

Imam ya dawo xaki tareda baqinsa, lokacin da kowa ya zauna a wurin da yake, sai Imam (a.s) ya waiwaye su yace: abokaina duk lokacin da baku da buqatuwa da abu, ka da ku lalata shi ba tare da wani kwakkwaran dalili baidan baku da buqatarsa ko baiwa waxanda suke da buqata.

Tura tambaya