lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

ME YASA YAN SHIA SUKE KIRAN SUNAN YAYAN SU DA ABDU ALI KO ABDU ZAHRA……..?

DA SUNAN Allah me rahamna me jin kai

 

Allah ne kawai ya halasta a bauta masa, Allah nacewa acikin Alqur’ani

﴿ بَلْ اللَّهَ فَاعْبُدْ ﴾, amma me yasa yan shia suke san ya wa yayan su suna irin abu Ali  ko  Abuzzahra ko kuma Abdul imam? Amma kuma in muka duba zamu ga cewa su imamai da yan shia ke takama dasu basu taba sanya irin wanna sunayen wa yayan su ba. Kuma idan aka ce Abul husai ana nufin hadimin (خادم الحسين) Husain ne bayan kasantuwan imam Husain yayi shahad, kuma mutum zai iyayi kasncewa hadimin imam ko da bayan shahadarsa ne?

Amsar mu akan wanna tambayan itace:

Na farko: Ba makawa kan cewa ba wanda ya cancan ta a bauta masa sai ubangijin talikai wato Allah madaukakin sarkim, kuma duk wanda ya yi shirika ga Allah ya tabbata aikinsa zata kasance bacacciya, dalililai na hankali da kuma na naqli da aka same su cikin littafi da sunnah da kuma bayanan imamai sun tabbatar da hakan

Sai dai shi kalma na Abu idan muka duba asalin littattafai na luga zamuga na da maanoni da ban daban wanda zamuyi bayanin su daya bayan daya.

Na biyu: mun tabbata cewa a farkon musulunci anyi yaki da dama wanda an kama bayi maza da mata, mujahidai sukan raba mazajen a tsakanin su su kasance musu bayi, matan kuma akan saidasu a matsayin ma’aikata, sai dai musulunci yaba wa wanda aka kama dama da cewa in suka koyarda wani abun da suka iya zasu kasance ‘yantattu, ko kuma duk wanda ya karya azumi da gangan in ya tashi yin kaffara zai iya ‘yanta wasu daga bayin da suke wurin sa, irin wannan hanyoyin ‘yanta bayi yazo da dama acikin addinin musulunci.

Abin da yasa muka kawo wannan maudui na bayi shine abin nufi da Abd (عبد) anan wurin shine maanar mu na karshe wato bayi masu hidima kuma a ke saya da sayarwa da su, kamar kalma ta Abdullah mutane sune Abd wato bayin Allah masu bauta masa, shi kuma Allah shine maula kuma shugaba abin bautawa, amma acikin lugah akwai ban banci tsakanin Abdullah da kuma bawa na mutane, idan muka duba abd a maanar bawan Allah zamu ga ana Magana ne akan ibada amma idan kuma abd na bayin mutane ne maanar sa zai kasance akan kan bauta ne kamar mutum ya bautar da wani.

Yazo cikin littafin Almufradat na raghib Al-Esfahani cewa: abd yana nufin bauta da kuma nuna kaskanci shi kuma ibada abune me fadi da ya kunshi duka maanoni biyu na ABD, sabida shi ibada yana nufin nuna asalin kaskanci ne kuma be cancanta a yi ma wani hakan ba sai wanda yafi kowa wanda shin Allah madaukakin sarki, shiyisa yake ce wa

﴿الّا تعبدوا إلّا إياه﴾.

Ibada a wata fuska ta kasu kashi biyu, nafarko ibada a aikace kamar sujada na biyu kuma ibada ta Magana kamar irin su addua

(اعبدوا ربكم، واعبدوا الله)

ABD ya kasu kasha hudu:

1. Abd wato bawan da ke mulkar bayi wanda ya cancanci a masa bai’a (العبد بالعبد) wannan bawan bashida iko akan komai.

2. Abd wato bawa a ta fannin halitta, shi kuma wannan ya kebanta ga Allah madaukakin sarki ne (إن كل من في السموات والأرض الا آني الرحمن عبدا)

3. Abd ata fannin bauta da hidima a kan wannan bayani mutane sun kasu kashi biyu ne, na farko abd wanda ke ikhlasi da Allah an tabbatar da hakan a cikin Alqur’ani:

﴿وَاذْكُرْ عَبْدَنَا أَيُّوبَ﴾ ﴿إِنَّهُ كَانَ عَبْداً شَكُوراً ﴾ ﴿ نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَى عَبْدِهِ﴾ ﴿عَلَى عَبْدِهِ الْكِتَابَةة﴾ ﴿لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ﴾﴿فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلاً﴾ ﴿فَوَجَدَا عَبْداً مِنْ عِبَادِنَا ﴾

Sai kuma Abd na duniya wanda yake hidima ma wasu mutane irin wanna yazo a fadin mazo da ke cewa (تَعسَ عبد الدرهم تعس عبد الدينار). A wannan bayanin ne zamu gane cewa ba kowa bane kenan zaa kira shi da Abdullah sabida kalma na abd yana da maana da dama anan kuma na nufin bauta, in mukayi amfani da kalma adb akan haka zai kasance kowa ne ke nan ke bautawa Allah, har abubwan da basu da raima zaa iya basu wannan sunar. Don haka suk sanda aka dauki Kalmar abd aka manna ta da sunan Allah zai kunshi maana me yawa kamar in da akace a qurani (وما أنا بظلّام للعبيد) kuma duk wanda ya kauce wa Allah yayi shirka.

Abin da muke so mu tabbatar shine: kalma ta abd a maanar ta na gama gari ana nufin nuna kaskanci tare da biyayyah, idan har anan nufin nuna kaskanci da kuma biyayya ba tare da wata qaidi ba toh irin wannan Abd ga Allah ne kawai ta ko wani hanya a hankali ko kuma naqali, amma idan kuma ana nufin kawai kaskanci zai iya kasancewa ga annabawa ne ko wasiyyay na Allah irin mutanen da ke biyya wa annabawa ko wasiyyay zaa a iya kiran su suma da Abdu wane, kamar masu kai ziyar kabar buran imamai zaa iya kiran su abd na su imaman sabida suna nuna kaskancin sune agabannin imamai, kamar yadda ake cewa yaro bawane ga mahaifin sa, ko kuma dalibi bawane ga malamin sa, idan muka riqe wannan bayanin yazo acikin hadisi an rawaito daga imam Ali cewa: من علّمني حرفاً فقد صيّرني عبداً wanda ya koyarda ni koda harafi dayane ya ‘yantar dani.

Wannan na nuna mahimmanci da kuma girman koya da koyarwa cikin musulunci, sabida yasanya matsayin malaimai daidai na maula da shuwagabanni, shi kuma dalibi an sa matsayinsa daidai da na bawan da bai da komai sabida shi bawa komai nashi na uban gidan sa ne, kamar yadda yazo cikin tarihi.

Toh in muka dubi annabi Muhammad (saw) da fatima azzahara (as) da kuma sauran a’imma (as) zamuga cewa su malamaine wanda suke koyar wa mutane abubuwa da dama da kuma masu taimakawa wurin shiryar da su (ويزكيهم ويعلّمهم الكتاب والحكمة) wannan ayar ta kunshi har wasiyyay sabida suma suna koyar da mutane don haka suma sun kasance malamai na gaskiya, su kuma mutane sun kasance daliban su, dalibai kuma matsayin bayi suke da shi.

Da wannan bayanai na mu zamu gane cewa ba wani matsala mutum ya ke sanya suna irin su abdur rasul ga dansa da nufin cewa shi dan amatsayin dalibin annabi ne, ko kuma yake kiran sa da abdu Ali ko Abdu Husain amatsayin dalibin su, wani lokaci irin wadannan suna sukan taimaka mutane suke tuna da asalin hadafin da kuma koyarwa na annabawa da kuma wasiyai, shin akwai matsala wani yayi hakan?

Na uku: me yasa kuke bata asalin maanar Kalmar sabida abun a bayyane yake in akace abdu wane ba wai yana bauta masa kamar yadda yake bauta wa Allah bane, misali yanzu in aka ce wa annabi

(سيدي يا رسول الله) ko kuma ace (سيدنا الحبيب المصطفى) ga dukkan musulmi ta ko wacce mazhaba in suka yi  amfani da kalma na sayyid yana nyufin hadimi, shin dole wanda kake masa hidimar ya kasance a raye ? to meye laifin ace wa abdul Husain hadimin Husain bayan mutuwar imam husai.?Ahankalce dole sai mutum yaba ma wani ruwan alola ko kuma dole sai ya bashi abinci da abin shane kafin aki rashi hadimin wane? Mun san cewa hankali baza ta dauki hakan ba amma in mutum ya watsa tunanin wani da kuma koyarwar sa cikin duniya ako wacce zamani da kuma wuri zai kasance hadimin sa, kamar mutum yake raya zaman makokin imam Husain, mun san hankali ta yarda da hakan, sabida hidima ba kawai ba da abinci ko kuma abinsha bane ake kira hidima.

Na hudu: acikin makarantar ahlul bait da kuma koyarwar su kamar yadda yazo acikin littafin ziyarar su misali acikin ziyarar imam Ali na nemar izinin shiga haramin sa akan karanta wannan addu’ar

(عبدك وإبن عبدك وإبن أمتك جاءك زائراً) wannan bashi bane yake nuna cewa muna bautawa imam Ali bane kamar yadda muka bauta wa Allah, sai dai abd anan na nufin maanar ta biyu alugance, Inda zaka ga wani dan shia ka masa wannan tambayar cewa shin ka yarda da Allahntakar imam Ali, kuma shin kana bauta masa ne kamar yadda kake bauta wa Allah? Na tabbata amsar sa zai kasance AA ne ko da sau nawa zaka tambayeshi haka amsarsa zata kasance, ko shi imam Ali yana cewa أنا عبد من عبيد محمّد wato ni bawane da ga cikin bayin annabi Muhammad, to haka muma in mukace mu adb ne na imam Ali muna nufin abd da nufin hadimai ba wai abd na bauta ba, kamar yadda mukayi bayani abaya kan Kalmar Abd da maanoninta da tazo cikin littafin raghil alesfahani. Ya kamata muke bada wa ko wacce kalma asalin maanarta da kuma maanar da me firta Kalmar yayi niyya, sabida wasu kalmomi suna da maana da dama kamar a misali kalma ta ain (العين) wanda tana da maanoni sunkai guda sabain, sabida ita kalma akan gane asalin maanar tane ta hanyar qarina haliyya (القرائن الحالية) ko maqamiyyah (المقامية) ko kuma lafziyyah (اللفظيّة), don haka in mutum yace shi abd husaine ba wai yana nufin yana bauta masa bane sai dai yana nufin shi abd ne na Husain wato hadimin Husain. Hidimar mu ga ahlulbaiti shine biyayya gare su da kuma bin su sannan watsa ilimin su da kuma manufar su a tsakanin jama’a, ba kuma ko wani musulmi bane za’a iya kiransa da abd Husain ba ko da kuma yana kiran kansa da hakan.

Na biyar: yazo daga Ahlul bait cewa (نحن صنائع الله والخلق صنايعنا) malamasn hadisi suna bayyana cewa akwai maanoni da dama kan bayanin wannar hadisin, suna cewa mamanar hadisin shine mu ahlul baiti Allah ne ya tarbiyyanta mu, tarbiyyan sauran mutane kuma na hanin mu, sabida sune mahadi na Allah da halittarsa, haka hankali take tabbatarwa da kuma naqali wanda akaji daga littafi da sunnan.

Idan mutum yazo gun Allah cikin kaskantar da kai zai kasance Abd ne ba a matsayin hidima ﴿ أَطِيعُوا اللَّهَ وَأَطِيعُوا الرَّسُولَ وَأُوْلِي الأَمْرِ مِنْكُمْ ﴾

Toh anan Abd na nufin me biyayyah ga Allah wato bawar sa, sannan kuma shi bawan a tsawon biyayya da yake yi wallahi zai kasance me biyayya ga manzon Allah don haka zai kasance abd ga manzo don haka za’a iya kiransa da abdu rasulillah kuma bawa na Allah, sai kuma biyya ga majibantan al’amura yana daga cikin biyya ga manzo, wannan irin biyyan ya kebanta kawai ga imamai ne ma’asu mai ne, idan da kuma biyya din zai kasance ga wanda ba ma’asumi bane to be dace ba a bauta wa mahluqi ba wurin saba wa Allah. Wanda ya cancanci amasa biyayya ta haqiya sai ya kasance ma’asumi, don haka duk wanda ya ke biyayya wa majibantar al’amura kamar yana biyya wa Allah da manzon sa ne, duk wanda ya kasance abd ne ga Ali ko Fatima ko hasan ko Husain da kuma sauran ahlul bait, zai kasance shima abd ne ga Annabin tsira wato abd da maanar hadimi domin banbanci tsakanin ma’anar abd da ma’anar ibada da kuma abd da ma’anar biyayya da hidima kamar nisa tsakanin sama da kasane.

Da wannan bayanai da mukayi zai kasance ba wani matsala mutum ya sanya wa dansa suna abd Rasulillah ko abdu Ali ……., don haka duk wanda yake da tunin cewa irin wadannan suna ana sa sune da ma’ana bauta toh yana kuskure kuma baya ba wa kalma hakkinta wurin banbance tsakanin ma’anoni da Kalmar ta kunsa, don akan sami kalma daya da ma’anoni da dama.

 

وآخر دعوانا أن الحمد لله ربّ العالمین.

Tura tambaya