lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 16 MUHARRAM 1441 H- YA HALASTA YIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA CIKIN ZABI MATUKAR BA AKAI GA KARANTA RABI INBANDA FATIHA DA IKLAS

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami-tareda Assayid Adil-Alawi (H).

Lokaci: karfe 8 na safe, fikhu 3.

Cigaba kan bahasin da ya gabata: Akaramakallahu (K) ya ce: ya halasta ayi uduli daga sura zuwa wata surar cikin zabi matukar bai kai ga karanta rabin surar farko ba face daga Fatiha da Iklas, baya halasta ayi uduli daga garesu ya zuwa wasunsu kai bari bari hatta zuwa daga daya daga cikinsu zuwa daya, da zarar an fara da daya daga cikinsu ko da kuwa da fara karatun bismilla ne, na'am yana halasta yin uduli daga garesu zuwa suratul Juma'atu da Munafikun a iyakacin ranar Juma'a ta yanda mustahabbi ne cikin Auzhur din ranar Juma'a da ya karanta suratul Juma'a cikin raka'ar farko a raka ta biyu kuma ya karanta suratu Munafikun, idna ya sha'afa ya manta ya karanta wasu surorin hatta Fatiha da Iklasi to a irin wannan yanayi ya halasta yayi uduli daga garesu zuwa suratu Juma'atu da Munafikun matukar dai bai kai rabin surar da ya fara da it aba, amma idan ya fara da Fatiha da gangan to baya halasta yayi uduli zuwa garesu a bisa ihtiyadi.

Ina cewa: magana tana faruwar cikin mukamai: na farko: cikin asalin halascin uduli, na biyu a cikin mahalli da wurin da yake halasta da rashin halasta, malamai sun samu sabani cikin kan ra'ayoyi kamar yanda bayani ya gabata.

Amma mukami na uku: cikin abubuwan da aka togace cikin halasci da rashinsa hakika manya-manyan malamai sun sassaba cikin mas’lar, mashhur da Almuhakkikul Hilli sun tafi kan halasci yin uduli matukar dai bai kai rabin sura da ya fara da ita face cikin Fatiha  da suratul Kafirun da Iklas, cikin wadannan surori baya halasta ayi uduli daga garesu zuwa wasunsu, wannan shi ne ra'ayin da muma muka zaba kamar yanda shi ne ra'ayin da mashhur daga malamai suka zaba kamar yanda aka nakalto daga garesu.

Yana shiryarwa kansa wasu fuskoki: na farko: da'awar ijma'I kamar yanda ya zo daga Majma'ul Burhan, sai dai kamar yanda kake gani ijma'I ne Almadaraki kamar yanda yake a zahiri.

Na biyu:nassoshi da suka zo cikin wannan babi kamar misalin Sahihatu Amru Ibn Abi Nasar Assakuni ya karbi da Shehunai: Muhammad Ibn Yakub da isnadinsa daga Ibn Abi Nasar:

قال: قلت لأبي عبد الله  عليه السلام: الرجل يقوم في الصلاة فيريد أن يقرأ سورة، فيقرء قل هو الله أحد، وقل يا أيها الكافرون، فقال: يرجع من كل سورة إلّا من قل هو الله أحد وقل يا أيها الكافرون[1].

Ya ce: na cewa Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: mutum ne yake tsayawa cikin sallah sai ya nufi karanta sura, sai ya karanta suratul Iklas, da suratul Kafirun, sai ya ce: zai iya uduli daga kowacce sura in banda suratul Iklas da suratul Kafirun.

Muhammad Ibn Hassan da isnadinsa daga Husaini Ibn Muhammad misalinsa dai, daga Muhammad Ibn Yakub misalinsa dai.

Fuskar kafa hujja: bayan ingancin isnadinsa lallai riwayar a bayyane take karara cikin rashin halascin uduli idan ya fara da karanta suratul Iklas ko Fatiha zuwa wasunsu

وصحيحة الحلبي عن الكليني بإسناده عن ابن مسكان عن الحلبي قال: قلت لأبي عبد الله عليه السلام: رجل قرأ في الغداة سورة قل هو الله أحد قال: لا بأس أو من افتتح سورة ثم بدا له أن يرجع في سورة غيرها فلا بأس، إلّا قل هو الله أحد، ولا يرجع منها إلى غيرها، وكذلك: قل يا أيها الكافرون[2].

Sahihatu Alhalabi daga Kulaini da isnadinsa daga Ibn Muskan daga Alhalabi ya ce: na cewa Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: mutum ne da asubahi ya fara karanta suratul Iklas sai ya ce: babu laifi ko kuma daga wand aya fara da sura sannan ya canja ra'ayi yayi uduli zuwa wata surar shima babu laifi, in banda suratul Iklas bai halasta yayi uduli daga gareta zuwa wata surar, haka ma suratul Kafirun.

 صحيحة علي بن جعفر: عن عبد الله بن جعفر في (قرب الإسناد) عن عبد الله بن الحسن عن علي بن جعفر عن أخيه عليه السلام قال: سألته عن الرجل أراد أن يقرء سورة فقرأ غيرها، هل يصلح له أن يقرء نصفها ثم يرجع إلى السورة التي أراد؟ قال: نعم ما لم تكن قل هو الله أحد أو قل يا أيها الكافرون[3].

Sahihatu Aliyu Ibn Jafar: daga Abdullahi Ibn Jafar cikin littafin Kurbul Isnad daga Abdullahi Ibn Hassan daga Aliyu Ibn Jafar  daga dan'uwansa amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce: na tambaye shi dangane da mutumin da yayi niyyar karanta wata sura amma kuma sai ya karanta wata daban, shin ya halasta ya karanta rabinta sannan ya janye ya dawo zuwa ga sura yayi niyyar karanta ta tun farko? Ya ce: na'am matukar dai bata kasance suratul Iklas da Kafirun ba.

Aliyu Ibn Jafar ya rawaici wannan hadisi cikin littafinsa, babban malaminmu Allama Hurrul Amili Allah ya tsarkake ruhinsa ya ce: ina cewa: abinda yake shiryarwa zuwa ga hakan zai zo daga baya.

Na uku: sakamakon misalta karatun sura bayan Fatiha na kasancewa cikin raka'o'in biyun farko sai ya zama tabbatu da zarar fara karanta sura idan sun kasance Iklas da Fatiha, a wannan lokaci baya halasta ayi uduli daga garesu zuwa wasu surorin, lallai yin hakan zai zama ya lazimta sauya wazifar da aka kallafa maka da wata wazifar da daban wannan wani abu ne da babu dalili a kansa, bari dai zai lazimta kokarin tabbatar da abind aya rigaya ya tabbata hakan mustahili ne a hankalce ko kuma muce yanada muni idan ya kasance an sanya hankali cikinsa, a wannan lokaci tareda kasancewa sura juzu'I ce wani yanki ce ya fara da ita wacce itace suratul Iklas ko Fatiha to sauran usrori za su zama sun fadi daga kasancewa juzu'I da yanki, kan haka: idan muka tafi kan wajabcin cika zai wajaba kansa ya cika idan kuma muka zabi halasci kan karkasa zai zama ya halasta ya takaitu kan iya inda ya karanta ya dauke hannu daga saura.

Wannan shi ne ra'ayin da mashhur suka zaba kamar yanda ya kasance ra'ayinmu, sai dai cewa an nakalto daga littafin Almuntaha da Biharul-Anwar da Azzakiratu kaikawo da kin zabar ra'ayi cikin mas'alar, sai dai kuma cewa tareda samuwar nassoshi da ijma'in da akai da'awarsa babu fagen da za a tsaya ana kai kawo da kin zabar matsaya, wannan magana magana ce mai rauni.

Almuhakkikul Hilli (K) cikin littafin Almu'utabar ya zabi karhanci, sai a dora hanin kan hani na tsarkaka bawai nna rashin halasci ba bisa riko da fadinsa madaukaki:

﴿فَاقْرَءُوا مَا تَيَسَّرَ مِنْ الْقُرْآنِ[4]،

Ku karanta abinda ya saukaka daga kur'ani.

Lallai idlakin kur'ani da idlakin karanta abinda ya sawwaka ya tattarowa dukkanin surori baki dayansu, sannan riwayar Assakuni bata samu karfin da zata iya yin taksisin ayar ba, maganarsa ta kare Allah ya daukaka matsayinsa, kamar yanda kake gani za ayi masa martani : da farko: hakika riwayoyin ingantattu ne a cikin mukamin  kamar yanda ya gabata zasu iya taksis din idlakin ayar mai daraja kamar yanda yake gudana cikin taksis idlakin ayoyin kur'ani mai girma da riwayoyi ingantattu, kan haka ne malamai su kai aiki babu banbanci cikin abinda ya ta'allaka da wannan mukami ta fuskar karatun sallah ko waninta.

Na biyu: idlakin ayar bai da alaka da bahasinmu na batun rashin halasicn uduli daga suratul Iklas da Fatiha zuwa wasu surorin, lallai zai lazimta kaidi da taksis  mara kyawu abin kyama, kamar cikin fadinmu: na cinye dukkanin Ruman din da yake cikin wannan lambu sannan cikin lambu akwai Ruman 100 sai kuma daga bayan ka dawo kayi taksisi kace na cinye baki dayansu amma banda guda 99 ma'ana dai kwaya daya rak ka ci, misalin wannan taksis abin kyama a wurin ma'abota hankali, to haka lamarin yake cikin bahasinmu, wannan shi ne abinda Assayidul Hakim yayi ishara zuwa gareshi cikin Almustamsakihi juz 6 sh 189.

Sai dai zai a iya ishkali a kai a tafi kan mudlakin halasci hatta cikin surorin Fatiha da Iklas ko kuma da mafi d acewa hani daga wanda ya zabi rashin halasci cikinsu da cewa: ta kaka za a zabi wajabcin kammala karanta su idan ya zama an fara da su baya halasta ayi uduli daga garesu zuwa wasu surorin, tareda cewa bayani ya zo kamar yanda zamu gangara kansa- halascin uduli daga garesu zuwa surorin Juma'a da Munafikun a ranar Juma'a tareda mustahabbancin karanta su cikin ranar juma'a, da kammala karatunsa wajibi ne da ba a halasta uduli daga garesu saboda wani aiki na mustahabbi, kamar yanda ake cewa: ta kaka za a kyale wajibi a sadaukar da shi saboda aikin mustahabbi, abar abinda yake cikinsa daga cikakkiyar maslaha a jumlance ya zuwa wata tauyayyar maslaha, wannan ketare iyake ce wanda yake zalunci ne sai ya zama yayi kar da hankali da hikima, ita hikima shi ne ajiye abu a mahallinsa, an bada amsa wannan ishkali : ita wannan mas'alar tana daga ta'abuddiyat wacce ubangijinmu ya buatar da mu da ita babu mulazama a shari'ance tsakaninsu, kamar yanda yake bayyana a wanin wannan muhalli daga halascin yanke farilla ga wanin wajibi tareda rashin halascin yanke wajibi a kankin kansa, ka lura.

Sannan abinda idlakin ke hukunci da shi yana da nassoshi cikin wannan babi na rashin halascin uduli mudlakan ko da kuwa ya fara karanta farkon ayar ko da kuwa mikdarin bismillar surar da ya ayyana karantawa ce, a  al'adance za a ce ya fara karanta suratul Iklas ko Fatiha da zarar ya fara da bismillarta , a wannan lokaci babu banbanci ciki kasancewar ya kai ga karanta rabin surar ko bai kai ba.

Kamar yanda hukuncin idlaki shi ne rashin halascin uduli daga kowacce daya daga garesu zuwa wasu surorin kai hatta tsakankanin junansu sakamakon cin gashin kan kowacce daya daga cikinsu.


[1] الوسائل: باب 35 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأول.

[2] الوسائل: باب 35 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

[3] الوسائل: باب 35 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثالث.

[4] المزمل: 20.

 

Tura tambaya