lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ku kasance tareda masu gaskiya

 

Ba bakon al’amari bane kaga ana hujumi kan akidojin ubangiji ana kai musa bara da dukkanin kibiya da masu daga makiya, saboda dama dole ne su samu karo da nau’uka daban-daban daga mutane wadanda basu zama wuri guda da bukatunsu da alfanunsu da suka ginu kan zalunci da danniya sakamakon su akidojin ubangiji ka’idojinsu na kira zuwa ga gaskiya da karfafa adalci da yada rahama, wannan wani abu ne da kowa ya san shin a nesa da na kusa, bari dai hakan kamar wani jigo ne na rayuwa da sunnar samuwa da dukkanin litattafan sama sukai bayaninsu, lallai kur’ani na da wata babbar aya cikin bayanin asalinsu da sabubba da dalili da natija kai da dukkanin abinda ya lazimce su, mafita daya da za a iya kubuta daga wannan matsala.

Lamari ba abu ne mai saukin gaske ba da za a iya ketare shi da juzu’an halloli ba ko magancewa ta jeka nayika da fafutikar mutane na baya da na yanzu bari dai

 ( كل حزب بما لديهم فرحون ) .

Dukkanin wata kungiya na murna da abinda yake garesu.

Lokacin da akida ke kasanctuwa babu wasa babu wargi kadai zance ne na faifaicewa daga mafi gaskiyar masu Magana mafi hikimar masu aiki, a irin wannan lokaci ya zama dole faifaitaccen hukunci ya zo da abinda yake kaiwa zuwa ga bayyanuwa da tserata da bayyanannen lamari da yanayin da zai kasantu mabayyani mahaskaki kamar rana.

Haka dai lokacin da Allah ya kirayi annabinsa ya amsa sai yace:

( اني تركت فيكم الثقلين كتاب الله وعترتي اهل بيتي ما ان تمسكتم يهما لن تضلوا بعدي ابدا )

Hakika ni mai bar muku nauyaya biyu ne littafin Allah da tsatsona Ahlin gidana matukar ku kai riko da su ba zaku taba bata a bayana ba har abada.

Saboda dole ne hasken shiriyar da ya tabbatu cikamakin manzanni (s.a.w) ya zama dole ya kasance ya wanzu ya kuma cigaba, kuma dole mikakken layin da ya zayyana shi da shiriyar kur’ani ya zama dole ya wanzu mabayyani, kuma dole tunanin da ya zo da shi da gaskiya ya wanzu yana mai alfarma har zuw atashin kiyama, wannan bai kasantuwa face ga wand aya siffantu da haskensa shine Allah yake zaba ya sanya shi imami mai shiriya da shiryarwa, mai gaskiya mai gasgatawa, bai furuci da son rai, babu wani daga mutane da yake tsara da shi, wannan abin ya afku lokacin da Allah ya kaunaci al’umma da imaman shiriya, daga cikinsu zaka samu Sadik Ahlil-baiti (as) alfaharin muslunci kambunsa kuma alfaharin dukkanin dalibin ilimi, yayin da ya tsaya yana cewa:

 ( حدثني جعفر ابن محمد الصادق ..) .

Jafar bn Muhammad Sadik ya zantar dani.

Amincin Allah ya kara tabbata gareshi hakika ya kasance taskar ilimi annabawa , sannan madaukakan hadisansa sun kasance masdari tushe mashaya da shari’a, ya sanya abinda ya ke gareshi ga al’umma domin sauke sako daga hadisi na gaskiya da bayani mai nuduki, da hujjoji na yankan shakku da hikimomi masu alfanu, da nasihohi na shiriya, da dataccen tunani, da dukkanin abinda al’umma take bukatuwa zuwa gareshi.

Da kuma tunkude bata, rayuwarsa amincin Allah ya tabbata gareshi ta kasance rayuwa ga zukatan muminai, rayuwar muslunci madawwami, samuwarsa mai albarka samuwar al’umma  wacce ta samu da samuwar kakansa Mustafa Muhammad (s.a.w)


Tura tambaya