b Kashe-kashen ma'arifa
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kashe-kashen ma'arifa

 

Akwai dangantaka karfaffa tsakanin ma'arifa da aiki dayansu na shiryarwa zuwa ga dayan daga babun dilalar ilimul ijmali kan ilimul tafsili haka ma akasi kamar am da khas.

وفي الحديث الشريف النّاس كلُهم هلكى ، إلّا العلماءء، والعلماء كلّهم هلكى، إلّا العاملون، والعاملون كلّهم هلكى، إلّا المخلصون، والمخلصون على خطر عظيم.

Ya zo cikin madaukakin hadisi cewa dukkanin mutane sun halaka face malamai, haka dukkanin malamai sun halaka face masu aiki, sannan dukkanin masu aiki sun halaka face masu tsarkake niyya, sannan su kuma masu tsarkake niyya suna kan babban hatsari.

Shi ne hatsarin riya lallai ita riya kamar misalin daddafar tururuwa ce akan dutsen da bai da tsiro cikin duhun dare, wane ke jin karar sawun tafiyar waccan tururuwa? Bana barrantar zuciyata lallai zuciya mai yawan umarni da mummuna ce face dai abin da ubangijina ya yi rahama. Lallai shaidan makiyin mutum yana madagata tun ranar farko ya yi rantsuwa da izzar Allah sai halakar da bil adama baki dayansu face bayin Allah tsarkakakku wadanda Allah ya tsarkake su don kansa da ranar lahira.

وقال أمير المؤمنين علي علیه السلام لكميل صاحب سرّه: يا كميل ما من حركة إلّا وأنت محتاج فيها إلى معرفة[2].

Sarkin muminai Ali (as) ya cewa kumailu abokin sirrinsa: ya kumailu babu wani motsi face kai kana bukatuwa zuwa ga ma'arifa cikinsa.

Sanin Allah da manzonsa da limamin zamaninka wajibi ne kan kowanne musulmi mace da namiji mumini da mumina. Dukkanin wanda bai san Allah ba bai san manzon Allah, bai san limamin zamaninsa bay a mutu a wannan hali da yanayi to fa ya yi mutuwar jahilya mutuwar kafirci da munafunci da bata. Karshensa azaba da wuta.

 (اللّهم عرفني نفسك فإنّك إن لم تعرفني نفسك لم أعرف نبيّك، اللهم عرفني رسولك، فإنّك إن لم تعرفني رسولك لم أعرف حُجتك اللّهم عرفني حُجتك، فإنّك إن لم تعرفني حجتك ضللتُ عن ديني اللّهم لا تمتني ميتة الجاهلية) [3].

Ya Allah ka sanar dani kanka lallai idan kai baka sanar dani kanka ba ba zan san annabinka ba ya Allah ka sanar dani annabinka lallai idan bakla sanar dani annabinka bazan san hujjarka ba ya Allah ka sanar dani hujjarka lallai idan baka sanar dani hujjarka ba na bata daga barin addinina.

Kashe-kashen ma'arifa da nau'o'inta:

sannan duk da kasantuwa ita ma'rifa tana da matsayin jinsi, kuma kowanne jinsi yana da nau'uka, kamar yadda nau'I yake da sinfofi, sannan sinfi yana da daidaiku da misdakai (abubuwan da yake gasgatuwa kansu) manya-manyan malamai sunyi ishara zuwa ga jumulla daga nau'ukan ma'arifa da kashe-kashenta cikin bahasinmu zaka tsinkayi mustawowin ma'arifofi wajen mutane da mustawan malamai, da sassabawar hanyoyi da tsarin ma'arifa da nau'inta, cikin kowanne nau'I arifi zai iya sanin tauhidi da annabta da imamanci, bari dai kowanne tabbataccen abu daga tabbatattun abubuwa, kowanne abu daga abubuwa, kamar yadda shi karkashin abubuwan da suka ratayu da ma'arifa ma'arifa ke kasuwa take nau'antuwa ya zuwa nau'o'i da kashe-kashe, ya yin da ta kasance kan ma'arifar imamanci kan hasken addini muslunci da mazhabar ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu, kamar yadda idan ka nufi sanin shugaban shahidai imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare shi, lallai kai zaka iya saninsa amincin Allah ya kara tabbata gare shi mu ma zamu iya saninsa gwargwadon ikonmu cikin kammiya da yanayinmu da fadin tanadinmu da iliminmu da wayewarmu ta hanyar ma'arifa mai zuwa nan gaba:

1-ma'arifa ta hankali: tana kasantuwa da kafa dalilin ilimi da hujjar mandiki na hankali daga kiyasi da jera mukaddima  daga sugriyat da kubriyat da lafiyayyun natijoji bisa sharuddan da aka ambata cikin ilimin mandik da falsafa.

2-ma'arifa shuhudiyya ta kashafin irfani: it ace tsaftatacciyar zuciya tsarkakka kamar misali madubi garai-garai da take kasantuwa daga kashuffan zuciya ta Allah gasgatatta.

3- ma'arifa fidriyya: tana kasancewa ga al'amurra da batutuwa sanyayyu cikin asalin halittar mutum da halittar mutum wadda aka kirata cikin hadisai da badinin mutum, hakika manyan malumma sun samu sabani cikin ma'ana da bayani kan fidra(halitta) musammam ma cikin fadinsa madaukaki:

 ﴿فِطْرَةَ اللَّهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا﴾ [4].

Halittar Allah da ya halicci mutane kanta.

Dalilin fidra yana daga dalilai ma'asumai kamar dalilin hankali da kur'ani da ingantaccen hadisi, ance ma'anarsa: shi ne alkawalin da aka karba a duniyar kwayar zarra bisa kudurcewa da shi, an kuma ce: ita ce hakika wacce Allah madaukaki ya yi halicci mutane kanta, shi ne karbar gaskiyarsu da tauhidi da manzanci da imamanci da za bar mutum da kansa ba tare da tasirantuwa da inda yake rayuwa ba, an kuma ce: ma'anarta shi ne dukkanin wani abun haihuwa ana haifar kan sanin Allah da kaunar kamala mudlaka da kywun alheri, ya zo daga ahlil baiti (as) cewa fidra: da ma'anar tsayuwa kan hanyar gaskiya babu karkata cikin fadinsa madaukaki:

﴿حُنَفَاءَ لِلَّهِ غَيْرَ مُشْرِكِينَ﴾،

Kuma masu tsayuwa kan gaskiya ba masu shirk aba.

Da ma'anar wilaya da kuma lallai cewa ita ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah muhammdu manzon Allah amincin Allah ya kara tabbata gare shi da iyalansa sarkin muminai Ali (as) da tauhidi da muslunci da ma'arifa da wasunsu, kamar yadda cikin ilimin mandik cikin tsanuka kiyasan hujja.

Cikin shakalin farko da kayayyakinsa daga awwaliyat daga cikinsu: nazariyat, babu shakka lallai ma'arifofin Allah da asraran tauhidi boyayyyu taskatattu ne cikin halittar mutum tun adamu har zuwa ranar kiyama kamar yadda hakan ya tabbata a mahallinsa sananne a wajen ahlinsa.

4- ma'arifa nakaliyya; tana kasantuwa da dalilan nakali cikin littafin Allah mai girma da sunna tsakakka daga cikinsu a'imma ma'asumai amincin Allah ya kara tabbatuwa garesu ma'ana da abin da ya zo cikin hadisai ingantattu wanda ake la'akari da su daga manzon Allah amincin Allah ya kara tabbata gare shi da iyalansa, zababben ra'ayi cikin karbar hadaisai ta fuska gamammiya shi ne lallai cikin hukunce-hukuncen shari'a da taklifi kadai dai muna karba hadisin amintaccen mai riwaya ta fuskanin isnadi a waninsa kuma daga akida da kyawawan halaye kadai dai muna karbar amintacce daga gares, dilala kuwa ta fuskanin tabbatatarwarta cikin akidu da hujjoji na hankali, cikin halaye da dalilai na tsarin halitta, Allah mai katangewa abin neman taimako, wannan ma'arifa tana komawa ga jijiyo uku wadanda aka halicce su kan kaunar kamala mudlaka ma'ana tana fuskantar Allah matsarkaki ita ce son kamala da son kyawu da son alheri.

5- ma'arifa tarikiyya: abin da kae nufi daga gareta shi ne ta kasance karkashin bibiyar litattafan tarihi da masana tarihi bayan banbance aya da tsakuwa da cire algus daga kosashshe.

6- ma'arifa jamaliyya: abin da ake nufi daga gare ta sanin abu daga gundarinsa da badininsa.

Tura tambaya