lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)

An karbo daga Abdul-A’ala d`aya daga cikin `yan shi’a da ya kasance yana zaune a garin Kufa ya ce: wasu ba’arin Sahabban Imam Sadik (A.S) sun rubuta wasika zuwa ga Imam wacce cikin ta su ka yi tambayar wasu ba’arin tambayoyi daga abin da suke bukatuwa zuwa gareshi, sannan sun dora mini nauyin in tambayar musu Imam baki da baki dangane da hakkin musulmi kan dan’uwansa musulmi, ya ce: sa’ilin da shiga birnin Madina na je wajen Imam (A.S) sai na mika masa wannan wasika da suka bani, kuma na tambaye shi kan hakkin musulmi kan dan’uwansa musulmi? Sai Imam (A.S) ya bada amsa wasikar da suka aiko a rubuce yaki bani amsar tambayar da na yi masa baki da baki, yayin da na da daura damarar komawa garin Kufa sai naje wajen sa don muyi bankwana mu yi sallama, sai na ce masa: na tambayeka gameda hakkin musulmi kan dan’uwansa musulmi amma baka bani amsa ba.

Sai ya ce: bana kaunar bada amsa akai.

Sai nace: me yasa ya `dan Manzon Allah?

Sai ya ce: saboda naji tsoran kada in fada muku gaskiya kuki aiki da ita sai ku zama Kafirai.

Sannam ya ce: ka sani cewa mafi wahala da muhimmancin wajiban Allah kan halittunsa abubuwa ne guda uku.

Na farko: ka yiwa mutane adalci daga kanka ta yanda ba zaka so wa waninka abinda baka sowa kanka ba.

2- kada ka yi wa mutane rowar dukiyar ka.

3-ambaton Allah a kowanne irin hali bana nufin ambaton da zikirin (subhanallahi walhamdulillahi)  ma’ana dai mutum ya tuna da Allah idan ya himmatu kan aikata zunubi

 

Tura tambaya