lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MA’ANAR ABOTA

 

Munana zato tsakanin abokan juna, a wani lokaci mu kan canja yanayin mu’amalar mu da abokan mu ba tare da wani kwakkwaran dalili ba sananna sai daga bayan idan mun yi bincike kan sababi sai mu samu babu abinda ya jawo haka sai munana zato da rare-rayen da muka kirkira muka gasgata su su ka wayi gari hakika muka zama muna gasgata su muna biye musu, sakamakon haka muka zamanto muna bin wani ayyanannen suluki da uslubi cikin mu’amalar mu ba tareda Ankara ba, alakokin da suke tsakanin mu suka munana matuka, shi aboki mutum ne kamar kowa yana kuskure yana kuma yin daidai, yana iya zamantow aya keta wani yanayi da ba zai iya bayyana abinda abinda yake cikin zuciyarsa gareka ba ko ga waninka, ta yiwu nan gaba ya fada maka dalilin canjawarsa, saboda haka ka tausasa masa ka bashi uzuri sau saba’in duk sanda ka ga ya aikata kuskure ko duk sanda kaga wani abu da zai iya bata alakarku ya faru, cikin wannan fage wata kissa daga cikin kissoshi ta burgeni cikin mu’amala tareda aboki da bayanin ma’adanin mutum  bayan sauyawar yanayi da halaye, san naji ina kaunar in nakalto muku wannan kissa.

A zamani da ya wuce anyi wani matashi mai girma mai tarin dukiya ma, babansa yana aikin sayar da gwalagwakai da duwatsu masu daraja, ya kasance mutum mai karamci tareda abokansa suna girmama shi shima yana girmama su, kwanaki suka luluka suka shuda, yanayi da hali ya canja, sai baban wannan matashi yam utu danginsu suka talauce talauci mai tsanani! Sai wannan matashi ya tafi yana neman tsofaffin abokansa , sai kwatsam ya tuna da wani abokinsa da ya kasance mafi mutunci da kirki mafi kusancin soyayya da shi daga sauran abokan, ya samu labarin cewa ya zama mai kudi sai take ya nufi wurinsa yana mai fatan saun aiki ko wata hanya don gyara halin da yake ciki, sai masu gadin fada suka tare shi sai ya basu labarin karfaffar dangantakarsa da mai wannan fada da abokantakar da take tsakaninsu, sai suka je suka gayawa mai fadar sai ya bude taga ya leko ya hango shi sai ya ga wani mutum cikin halin ban tausayi sanye da tsumma, sai ya cewa masu gadinsa ku je ku ce masa mai wannan fad aba zai iya ganawa da kowa ba a yanzu, sai ya fito yana ban mamaki daga mu’amalar da tsohon abokinsa yayi masa, yana tafiya zuciyarsa na ta konana yana mamakin yanda kima da mutunci da halasci da karamci suka mutu?! Sai ya koma gida bai san me zai yi ba, bai san idan zai je ba, daidai lokacin da yake kan hanya sai ya ga muatne uku gabansa cikin firgici sun fuskanto shi kai kace suna neman wani abu ne sai ya ce musu: me ya faru daku? Sai dayansu ya ce masa: muna neman wani mutum ne sai suka ambani sunan mahaifinsa sai ya basu amsa da cewa wannan mutumi da kuke nema mahaifina neya mutu kwanakin baya! Sai suka ce mahaifinsa ya kasance mutumin kirki suka nuna jimami da bakin ciki kan mutuwarsa, suka ce masa babanka ya kasance yana sayar da gwalagwalai da duwatsu masu daraja, yana bin mu bashin wani murjani mai daraja wacce ya barta wurinmu matsayin amana to yau mun dawo da wannan amana gareka, sai suka fito da wata yar jaka cike da murjani suka bashi suka juya suka tafi!! Sai mamaki ya mamaye wannan matashi ya kasa gasgata abinda ya gani, ya tsaya yayi tunani kan yanda zai sayar da wannan murjani, baki dayan garinsu babu wanda yake da kudin da zai iya sayen murjani daya daga wannan murjani da yake hannunsa yaya kuma jaka guda ta murjani, bayan wani lokaci sai ya hadu da wata mace tsohuwa mai kudi, ta zo ta neman mai sayar da kayayyakin ado daga gawl da duwatsu masu daraja, sai ya sayar mata sannan tayi alkawarin zata je ta dawo ta sayi sauran, a haka kasuwancinsa ya dawo yana habbaka kowacce rana har ya dawo kamar yanda ya kasanci a da zamanin da wuce kai ma ya habbaka fiye da zamanin baya, wata rana sai ya tuna da wancan abokin nasa da yayi masa wulakanci, sai ya rubuta wasika zuwa gareshi ya baiwa wani abokinsa don ya kai masa, a cikin wasikar yana cewa:

 

Na yi abota da mutanen banza da basu da cika alkawari da nuna halasci,* cikin mutane su sun shahara da makirci da yaudara* sun kasance a da suna girmama ni lokacin ina cikin wadata* amma lokacin da na karye sai suka kini suka gujeni sabida jahilci.

 

 Lokacin da ya karanta wannan wasika sai ya dauki takarda ya rubuta baituka uku matsayin martani da raddi yana mai cewa:

 

Amma mutane uku da ka hadu da suka baka murjani nine na turo su wajenka* babu wata hanya sai amfani da dabara* amma wannan tsohuwa da ta sayi murjani to lallai mahaifiyata ce* ka sani kai dan’uwana ne bari dai kai karshen burina ne* ban koreka saboda row aba* sai dai kawai ina jin yin kunyar gaba da gaba da kai cikin wannan hali.

Tura tambaya