lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

ALLAH YANA GANI NA A KOWANNE WAJE

 

An hakito cewa wata rana wani tsoho yayi niyyar gwada kaifin basirar dalibansa, sai ya tafi wajen samari hudu ya baiwa kowannensu tuffa ya nemi su ci wannan tuffa a wurin da babu wanda zai gansu, bayan wani dan lokaci kankani sai wannan samari hudu suka zo, sai ya tambaye su: shin kun cinye wannan tuffa, sai suka ce: na’am mun cinye ta, sai yace musu a ina, sai daya daga cikinsu ya bashi amsa da cewa a cikin dakina, na biyu ya bashi amsa da: a cikin sahara, na uku ya bashi da cewa ya cinye ta sa a kan jirgin cikin teku, amma na hudunsu sai ya zamanto shi ya dawo da tuffarsa a hannunsa, sai tsohon ya tambaye shi, me ya sa kai baka ci taka tuffar ba?

Sai ya bashi da cewa: na tafi na duba wurare masu tarin yawa sai dia cewa ban sami wani wuri da babu wanda yake gani na ba, saboda Allah yana ko ina yana kuma gani na a ko ina.

Tura tambaya