lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar

Da sunan Allah me rahama me jin kai 

Abu na farko shi ne ba shakka ko makawa cewa imam ali shi ne khalifa bayan manzon Allah daga Allah kuma tare da nassi, da dukkan abun da ke nuna ma’anan khalifacni da imamanci,Kaman yadda muka fada imamanci nada ma’anoni kasha uku

·       Na farko shine imama acikin tasarrufi (الإمامة التكوينية)- wato Allah ne ya turo su don su shuwagabanci mutane kamar irin su annabawa da kuma wasiyai

·       Sai nabiyu kuma imama cikin sharia (الإمامة التشريعية) shine taimakawa wurin isar da sakon da annabi ya zo dashi da kuma yin bayanin sa ga mutane

·       Na uku kuma shine imama da ya shafi alamuran duniya (الإمامة الدنيويّة)- wato shugabanci irin su mulki da hukumanci da kuma kula da alamuran mutane na yau da kunlum, wanda zai rike wannan matsayi yana bukatan shikan wasu sharuda daga cikin su akwai, yardan mutane kan cewa zai iya sauke wannan nauyi da ya dauru akan sa,  

Wannan shine abinda imaman mu basu samu ba musamman imam Ali (as) kasan tuwan masa kwace da wasu sukayi na wasu shekaru da kuma dan sa imam Hassan (as), wanda mutane suka guje su zuwa ga muawiya sabida son duniya.

Haka suka rike wannan mulki acikin kabilar su daga karshe kuma ya koma hanun bani Abbas, fadawar mulkin zuwa hannaye daban daban ya jawo rabe rabe tsakanin aluma, daga bisani hakan ya jawo rarrabuwan kasashen musulunci, wannan rarrabuwan bai amfanar da musulunci da komai ba sai dai ci baya da kuma rubgumar aladun turawan yamma kamar  yanda muke gani a wannan zamani namu.

Sai dai Allah ya yi alqawarin zai gadar da kasa ga Mahdi da kuma salihan bayin sa wanda zasu cika kasa da adalci da daidaito baya ta cika da zalumci .kuma Allah baya saba alqawarin sa .

Na biyu cewa wai imam ali yayi mubaya’a ga khalifofi guda uku wannan Magana karya ne da qazafi,ba zai yiwu a ce yayi musu mubaya’a ba bayan irin bayan haka kuma akwai nassoshi masu inganci sabo da haka wannan baa bun yarda bane Kaman yadda allama sayid sharafuddin amuli ya kawo a littafin sa(المراجعات)

Na uku abun da imam ali yay ba kashi bane ko hai’inci,yayi haka ne dan bin umarnin Allah da manzon Allah cewa yayi hakuri bayan wasiya a lokacin da ya kasan ce babu mai temaka masa,tabbas mutane sun qi shi sun kwace masa haqqin sa da muqaminsa da mulkin sa .

Kuma cewa don mutum na da ikon aikata abu sai bai aikataba ba shine hainci  ba, amma shi amirul mumini yana aikine da wasiyan manzo tsira kuma ba zai iya saba masa ba ko min kashin sa, Allama sayyid sharafuddin Alamuli ya bayyana hakan a littafin sa me suna:

(النص والإجتهاد:ص20) kar kashin bayanan da yayi kan taron da abubuwan da suka auku a saqifa.

(cewa imam ya na da masaniya kan magudin da mutane suke shiryawa) kuma in da imam ya nemi tashin hankali da suma sun ta da hankali, in da ya yake su da suma sun yake shi, kuma yin hakan baa bin da zai haifar face rudani cikin addini da tayar da hankular Al’uma shiyisa ya imam ya zabi zaman lafiya sabida zaman lafiya da hadin kan Al’uma.

Duk wannan bayanan sayyid ya ambato su cikin littafin sa me suna (فلسفة الميثاق والولاية) ko kuma zaa iya samun a littafin Almurajaat

Eh hakane imam ba wai ya zauna haka kawai  bane batare da ya nuna rashin yardar sa ba, sai dai sun zo sun fidda shi da karfi kamar yar da ya zo cikin littafin Aljauhari me suna(السقيفة )  kuma shaabi ya rawaito hakan a cikin wani littafi me suna (شرح النهج الحديدي) jildi na 2 shafi na 19, cewa lokacin da imam ke kafa wa Abubakar hujja da cewa:

فإن كنت بالقربى حججت خصيمهم

فغيرك أولى بالنبي وأقرب

وإن كنت بالشورى ملكت أمورهم

فكيف بهذا والمشيرون غُيّب

Imam ali yana cewa mafi soyuwan abu a garemu shi ne kar a taba lafiyan musulunci haka kuma daga wani fuskar imam yana dubi ga abubuwan da suka faru da kuma juyin mulkin da a kayi  a bayan manzon tsira ,da kuma kwacewar bai’an su kuskure ne Allah na kare musulmai daga duk sharri Kaman yadda suke da’awa (Abubakar yana cewa  bai’an da akamin kuskure ne ,Allah zai kare duk wani sharri da mummunan abu)  (شرح نهج البلاغة لإبن أبي الحديد: 1: 132)

sai dai kuma wannan hani din ya kasance a hanun imam ne da hakurin sa akan cutar da shi da akayi ,ya zuba musu ido daga nesa ,da kuma sadaukar da hakkin sad an kare musulumci da raya ta Allah ya saka masa akan waddanan abubuwa .

TAMBAYA:

Lokacin da imam ya dawo khalifa bai canza wani abu daga khalifofin da suka gabace shi ba, be kawo wani Alqur’ani da ban ba, har yakan yawaita fada akan mimbarin sa cewa:

 (خير هذه الأمة بعد نبيها أبو بكر وعمر) wato mafi Alherin mutum ga wannan Al’uman bayan annbi Muhammad Abu-Bakr da Umar ne, kuma be halasta auren mutu’a ba, kuma bai mai da gonar fadak ba, kuma bai wajabta mutu’a a hajji ba, kuma bai bukaci mutane suke cewa

(حي على خير العمل) cikin kiran sallah ba, kuma bai hana ake ce (الصلاة خير من النوم) ba,

Toh idan kunce Abubakar da Umar sunyi masa kwace ne me yasa duk bai mai da abubuwa yan da suke tun farko kamar yadda annabi ya koyar ba? kuma ga mulki a hanun sa. -Da abin da yafi dacewa kuce shine ya ha’inci Al’uma sabida bai bayyana musu abin da ya kamata su sani ba.

AMSA:

 1. kafin muyi Magana ya kamaya muke sanin abin da ya kama muke cewa sabida Maganan ka kan Abubakar da umar sune mafi alherin mutane bayan annabi ga wannan aluma hankali ba zai dauka ba kuma muna da masaniya cewa akwai hadisai na kage dayawa wanda bani umaiya suka kirkira don yabon wadannan sahabbai wanda in kadubi hadisan zakaga hankali bazai dauka ba.

2. munsan cewa imama ya nuna rashin yardansa tun lokacin suna raye toh me zai hana bayan mutuwan su ma ya nuna rashin yardarm sa ? lokacin da aka fidda wadan da zauyi khalafa akwai  Abdurrahman bin auf a cikin su imam ya bukace shi da yayi adalci da kuma koyi da koyarwa littafin Allah da sunnan manzo da kuma sunnan Abubakar da Umar a wani bayani kuma sai akace yabi koyarwar littafin Allah da sunnan annabi da kuma raayin sa, sai yayi amfani da hakan ya ba Usman kuria amma don samin cikakken amsa za ka iya duba الخطبة الشقشقية

3. fadin ka na cewa ka kan Abubakar da umar sune mafi alherin mutane bayan annabi ga wannan aluma, wannan karyace kawai wadda aka laqa masa, idan da sune mafi alheri ga wannan aluma bayan annabi me yasa be musu baia ba da ga farko, kuma har yake nuna rashin goyan bayan shi gare su a cikin خطبته الشقشقية.

Yaya zaayi suka sance mafiya Alherin mutane bayan sun zaunar dashi har na tsawon shekra 25 a gida ko sun riga shiga musulunci ne? ko sunfishi ilimi ne? ko sunfishi zuhudu ne? ko sunfishi sanin Alqurani ne? bayan muna da shaida Abubakr da kansa yakance :

 (.........ولست خيركم وفيكم أبو الحسن) wato yaya zan kasance mafi Alherin ku bayan ga Abu hasan (Imam Ali) a cikin mu.

4. shi kuma magana kan auren mutua kowa yasan cewa Allah ne da manzon sa suka halasta kuma ya kasance ana wannan auren har a zamanin khalifancin Abubakar da umar daga bayane umar ya haramta sabanin halarcin da Allah da manzon sa, mutual na hajima bayanin sa hakane lokacin umar ne aka haramta, umar na cewa : (متعتان كانتا في زمن رسول الله وأنا أحرّمهما وأعاقب عليهما) mutual guda biyu sun kasance halal a zamin annabi amma ni zan haramta su kuma zan hukunta duk wanda ya aikata, kuma umar ya aikata irin wannan abubuwa kan gonar fadak kuma ya kara wasu jumloli a cikin kiran Sallah irin su (الصلاة خير من النوم) don neman karin bayani zaa iya duba littafin (النص والإجتهاد) na sayyid sharafuddin Alamuli

5. cewa sunyi kwace wa imam ba kawai kage bane da ga gun shia ba, sai dai tarihi ya bayyana hakan kuma kowa ya tabbatar da ga ko wacce bangare na sunna da shia, hudu ta shaqshaqiyya ta bayyana hakan.

Wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuh

Tura tambaya