lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

FIKHU 13 GA WATAN SAFAR 1441 WAJIBI MAZAJE SU BAYYANA KARATU CIKIN SALLARA ASUBAHI

Qum mai tsarki dandalin mahallin Jabalul Amil Islami tareda-Samahatus Assayid Adil-Alawi (H) karfe takwas na safiya
 

Mas’ala 20- wajibi ne kan maza su bayyanar da karatun sallar a sallar Asubahi da raka’o’i biyu na fari daga sallolin Magariba da Isha’i, sannan wajibi su boye karatun cikin sallolin Azuhur da La’asar in banda sallar Juma’a ita cikinta mustahabbi ne bayyanar da karatu, bari dai hatta cikin Azuhur bisa Magana mafi karfi

Ina cewa: mawallafin ya bijira kan ma’alar boye karatu da bayyanarwa cikin sallolin farilla Magana cikinsu a wani lokacin na fadawa cikin ma’anarsu a luggance da isdilahance kamar yanda bayani zai zo kai nan gaba, a wani lokacin kuma bayani na afkawa kan hukuncinsu kan maza da mata kamar yanda zai bayyana, a karo na uku kuma Magana na tsayuwa kan mahallansu da inda suke fadawa, na hudu: lallai yana daga sharadi na Ilmi da Zikri.

Mawallafi sai ya tafi kan abinda ya kasance ya shahara tsakanin malamai kamar yanda ya zo daga jama’a daga manyan malamai daga wadanda suka gabata da wadanda suka jinkirta, bari dia ya zo daga Shaik Dusi (k) cikin littafin Alkilaf da’awar Ijma’I kan wajabcin bayyanar da karatu kan maza cikin sallar Asubahi da raka’o’i biyu na farko-farko daga Magariba da Isha’i da kuma wajabcin boye karatu cikin raka’o’in biyun farko Azuhur da La’asar da raka’ar karshe cikin magariba da kuma cikin dukkanin raka’o’in biyun karshen kowacce sallah mai raka’a hudu.

Assayid Murtada Alamul Huda ya sabawa haka kamar yanda aka hakaito cikin littafin Almu’utabar juz 2 sh 176, haka ma Ibn Junaidu Al’iskafi kamar yanda aka hakaito maganarsa cikin littafin Almuktalaf juz 2 sh 170 Allah ya tsarkake ruhinsu duk su biyun, su sun tafi kan mustahabbanci bayyanar da karatu da kuma rashin wajabcinsa, an hakaito daga Assayid Murtada cewa yayi bayani karara kan karfafa mustahabbancin bisa riko da abinda ya zo cikin ba’arin wasu hadisai bisa maimaita karatu da zai manta bayyanarwa,  daga cikin malaman da suka zo bayansu mai littafin Almadarik ya zabi wannan ra’ayi cikin littafin nasa juz 3 sh 358 haka Assayid Sabzawari ya biye masa kan wannan ra’ayi cikin littafin Azzakiratu 247, ba’arin malamanmu na wannan zamani sun karkata zuwa gareshi daga cikinsu akwai babban malaminmu Assayid Ku’i (ks) cikin littafinsa Sharhu Urwa juz 4 sh 371.

Hakika Mashhur sun kafa dalili da fuskoki masu yawa wasu fuskokin suna karbar munakasha.

Fuska ta farko: Ijma’I kamar yanda kake gani zai iya zama daga Ijma’I madaraki kamar yanda hakan shi ne galibi cikin ijma’in Shaik Dusi (k.s).

Fuska ta biyu: Sira mutasharri’a, lallai tana gudana kan kiyaye bayyanarwa cikin wuraren da muka ambata, da sira kahkara’iya tana hadewa da zamanin Ma’asumai amincin Allah ya kara tabbata a garesu, ya zama wajibi mu yi koyi da su.

An gangarar da ishkali  kan wannan Magana: hakika kololuwar abinda yake kunshe cikin sira kamar misalin aikin Ma’sumi kadai tana shiryarwa zuwa ga rinjayar aiki ba tareda shiryarwarsa ba zuwa ga wajabci lallai shi rinjaya ya fadadu daga wajabci wanda baya halasta barin aikata shi daga mustahabbi da yake halasta aikata shi da barinsa.

Fuska ta uku: bisa riko da riwayar Almufaddal Ibn Shazan kamar yanda ya zo cikin littafin Ilalul Shara’i da riwayar nan da ta gangaro kan illar da sababin bayyanar da karatu cikin sallar Asubahi da cewa ita tana cikin lokutan duhu sai ake bayyanar da karatu domin mai wucewa da giftawa ta gefan wajen ya samn cewa akwai mutane a wajen.

An rawaito daga Muhammad Ibn Aliyu Ibn Husaini da isnadinsa daga Fadalu Ibn Shazan daga Arrida amincin Allah ya kara tabbata a gareshi cikin wani hadisi ya ambaci illar da ta sanya ake bayyanar da karatun cikin ba’arin salloli koma bayan wasu ba’arin, lallai sallolin da ake bayyanar da karatu cikinsu sun kasance lokutan duhu, sai ya zama wajibi a bayyanar domin masu wucewa su san akwai mutane, idan suna son su yi sallah sai su tsaya su yi sallah, domin cewa idan basu ga mutanen ba zai ya fahimtar hakan ta fuskanin jin sautinsu, an rawaici wannan riwaya cikin Ilalu Shara’I da Uyunul Akbar da wannan isnadi da zai zo: daga Muhammad Ibn Aliyu Ibn Husaini da isnadinsa daga Fadalu Ibn Shazan daga Imam Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin wani hadisi da ya ambaci dalili da Illar aka sanya bayyanar da karatu cikin wasu ba’arin salloli da cewa cikin lokutan duhu ne, sai ya zama wajibi mai sallah ya bayyanar domin mai wucewa ya san cewa akwai mutane, idan yana son yin sallah sai ya yi sallah, sabida idan ma bai ga jama’ar ba zai fahimta daga jin sauti, sallolin da ba a bayyanar da karatu cikinsu kadai sun kasance lokaci hasken rana cikin yini su sun kasance ta fuskanin gani da ido ba bukatar jiyar da sauti, ya rawaito shi cikin Ilalu da Uyunul Akbar da wadannan isnadai da zasu zo da makamancinsu.

Anyi Ishkali kai: da farko ambaton hakan ya kasance ne daga hikima bawai daga dalili da illa da sababi ba, na biyu ba a mahallin bayanin hukuncin bayyanarwa bane ba tareda wajabci ko mustahabbanci ba da ma’anar isdilahin da ake bahasi kansa cikin Fikhu ba da mukamin da muke ciki ba.

Fuska ta hudu: bisa riko da riwayar Yahaya Ibn Aksaram Alkazi: cewa ya tambayi baban Hassan Imam Musa Alkazim amincin Allah ya kara tabbata a gareshi dangane da sallar Asubahiba baya bayyanar da karatu cikinta ita tana daga sallolin cikin yinin rana, kadai dai ana bayyanar da karatu cikin sallolin dare? Sai Imam (a.s) ya ce: saboda Annabi (s.a.w) ya kasance yana sallatarta lokacin duhu ai ya kusanta ta daga dare.1

An yi ishkali kansa: hakika wannan aikin na Annabi (s.a.w) duk da kasancewarsa hujja kuma daga sunna sai dia cewa baya shiryarwa kan wajabci, bari dai yana da ma’ana da tafi fadada daga wajabci daga mustahabbanci sakamakon tarayyarsu cikin rinjayar aiki cikin kankin kansa

Fuska ta biyar: bisa riko da ingantacciyar riwayar  Abdur-Rahman Ibn Hajjaju daga kira’ bayan Imam? Sai Imam (a.s) ya ce: amma sallah wacce ake bayyanar da karatu kadai dai anyi umarni ne da bayyanar da karatu domin wanda yake bayansa ya saurara.2

    Abinda ya zo cikin hadisin Muhammad Ibn Himran ko Imran daga Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: kan illar hakan da cewa lokacin da Annabi (s.a.w) ya tafi Isra’i farkon sallar da Allah ya farlanta a kansa itace sallar Azuhur din ranar Juma’a, sai Allah ya jingina Mala’iku da su yi sallah a bayansa sannan ya umarci Annabinsa (s.a.w) da ya bayyanar da karatunta domin bayyana musu falalarsa.3

An yi ishkali kansa: lafazin wajabci da umarni basu kasance a bayanne ba cikin wajabcin da kai isdilahim da yake hana barin karantawa, bari dai mafi fadada daga gareshi rinjayarwa da ma’ana mafi fadada sai ya zama shima mustahabbanci ya tsayu a mukamin

Idan wani ya ce: kadai ana fadin haka cikinsu da wajabcin isdilahi bisa riko da idlakinsu, sai mu bashi amsa da cewa babu idlaki a wannan mukami sakamakon rashin korowar Magana ga shari’a ma’ana shar’antar da hukuncin wajabci, kadai abinda yake a mukamin shi ne bayanin hikimar bayyana karatu bawai hukuncinsa ba, sai a lura.

Na biyu idna ma mun mika wuya mun sallama kan cewa akwai idlaki, lallai ambaton hikima da harshen illa bai iya tabbatar da wajabci.

Na uku: hadisan guda biyu basu tattaro wanin Imam ba, mai tambaya ta’abbuditan da wa taukifan da tankihul manad ya zama tilas kansa ya zama akwai dalili ya zuwa gareshi, rashin dalili kai dalili ne rashi.

 na shida: kafa hujja da riwayoyi ya kunshi cewa hakika salloli daga cikinsu akwai wadanda ake bayyanar da karatu akwai kuma wadanda ake biyewa.

Haka yake kamar yanda kake gani baya shiryarwa zuwa ga wajabcin bayyanawa na isdilahi bari dai ya kunshi mafi fadada daga gareshi.

Na bakwai: wanda shi ne jigo a wannan babi bisa riko da ingantattun riwayoyin Zuraratu Allah ya kara masa yarda:

Ta farko: daga Abu Jafar amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: cikin mutumin da ya bayyana a wurin da bai dace a bayyana karatu haka ya boye a wurin da ba a boyewa, sai Imam (a.s) ya ce: idan ya aikata hakan da gangan hakika sallarsa ta baci kuma wajibi ya maimaita sallah, idan kuma yayi ne bisa mantuwa ko rafkana bai sani ba to babu komai a kansa sallar ta inganta.

Hadisi na biyu: daga gareshi amincin Allah ya tabbata a gareshi: n ace masa mutum ne ya bayyanar da karatu a wurin da ba bayyanarwa, ko kuma ya boye a wurin da ba a boyewa, ya bar karatu a wurin da bai kamata a bari ba, ya karanta a wurin da ba a karantawa, sai Imam (a.s) ya ce: idan yayi hakan bisa mantuwa da rafkana babu komai a kansa.

Zamu cigaba kan wannan hadisi da yardar Allah


([1]).الوسائل: باب 27 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثالث.

([2]).الوسائل: باب 31 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

([3]).الوسائل: باب 35 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

 

Tura tambaya