lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata

DA SUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN KAI


Masoyana, Salamu Alaikum. Zanso nayi ishara zuwa ga jumlah akan adduoi masu amfani akan soyayya tsakanin ma’aurata, sai dai kafin na shiga cikin ainihin maudu’in bahasina zan yi ishara izuwa ga nuqdodi muhimmai  guda biyu a cikin jumlah.

Nuqda ta farko: shi haduwa da rabuwa tsakanin ma’aurata baya wuce daya daga cikin abubuwa hudu idan akayi la’akari da da ruhin su da kuma jiki, domin shi mutum ya qunshi asullai ne guda biyu: ruhi da jiki.

Na farko:  daga sama inda Allah yake cewa ﴿ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي﴾.

Na biyu: daga qasa

﴿َمَثَلِ آدَمَ خَلَقَهُ مِنْ تُرَابٍ﴾ ﴿ أَكَفَرْتَ بِالَّذِي خَلَقَكَ مِنْ تُرَابٍ﴾ ﴿ فَإِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ تُرَابٍ ﴾ ﴿ خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَابٍ ﴾ .

Halaye Guda Hudu:

Na farko: Ya kasance tsakaninsu akwai wani alaqa na ruhi da kuma jiki a tare, Kaman ace suna son junansu a zuciya kuma suna rayuwa a qarqashin rumfa daya ba tare da saki ko rashin kula juna  har zuwa qarshen rayuwansu.

Na biyu: Ya kasance bayan auransu sun samu rabuwa na ruhi da jiki a tare Kaman yanda yake a sakin da namiji inda ya rabu da matarsa ba zai iya dawo da ita ba sai da sabon aure, basa son junan su kuma ba za su iya rayuwa ba a qarqashin rumfa daya.

Na uku: Ya kasance a tsakaninsu akwai kusanci na ruhi da kuma rabuwan jiki, kamar ya kasance suna son junansu a cikin zuciyoyinsu sai dai kuma akwai rabuwan jiki a tsakaninsu saboda wasu dalilai, sai su rabu ta jiki kamar yadda yake a sakin da zaka iya dawo da matar ba tare da sake jaddada aure ba, a wani yanayin kuma sukan haramta wa junansu, sai dai namiji yana da ikon dawo da matar a cikin kwanakin iddanta.

Na hudu: Ya kasance a tsakaninsu akwai rabuwan ruhi amma kuma suna buqatuwa zuwa ga juna, Kaman su kasance a qarqashin rumfa daya kuma  suna rayuwa kamar ma’aurata, sai dai kuma ba soyayyar ma’auarata a tsakaninsu, dukansu sun banbanta da juna ko kuma sun banbanta da juna a ruhi, suna rayuwa ne dan dole tare da tsana a tsakaninsu saboda wani dalili daga dayansu ko kuma dukansu.

Sai dai lallai shi saki  yana da maana kashi biyu

Na farko a luga: wanda ke zuwa a maanar bayarwa ko kuma budewa

Na biyu a cikin istilahi: cikin bahasin fiqihu na nufin karanta sigar saki tsakanin maaurata a sharian ce, wanda hakan zai janyo kasan tuwan su komawan gidan jiya wato kafin suyi aure.

Saki anan ya kasu gida uku, na farko raj’I (رجعي) na nufin idan mijin ya nemi sakin matar sa amma kuma zai iya komawa gareta a lokacin da take idda, na biyu khul’I (خُلعيّ) wa to idan matan ta nemi mijin ta ya sake ta, sai na uku kuma ba’in (بائن) wato sakin da ba komawa bayan rabuwa har sai da sabon aure. Dukkanin wanna rabe rabe suna da hukunce hukuncen su don ne man Karin bayani zaa iya duba littafan fiqihu kan bahasin saki (الطلاق).

Maanar saki a istilahin fiqihu shine fitan mace daga igiyar aure, kamar yadda Allah swt ke fadi

﴿ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ ﴾ ﴿ الطَّلاقُ مَرَّتَانِ﴾﴿ وَالْمُطَلَّقَاتُ يَتَرَبَّصْنَ بِأَنفُسِهِنَّ ﴾

Wannan ayoyin suna bayani ne kan dukkanin rabe rabe na saki wanda ya kunshi raj’iya da wanda ba raj’iyyaba.

﴿ وَبُعُولَتُهُنَّ أَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ ﴾  ita kuma wannna ayar tana Magana ne kawai kan sakin raj’iyya.

Sai dai saki da kuma aure bisa laakari da ruhi da jiki (na mace da namiji) yana haifar da halaye guda hudu kamar yadda ya gabata a farkon bahasin mu.

Idan kuma muka dubi abin ta fiskar dalilai na fitira da hankali ko kuma ta fiskar naqali wanda aka samo da ga littafi da sunna, cewa so tsakanin ma’aurta itace asalin jigo na rayuwar aure, wanda a cikin zuciya ake samu.

A wani maana so na nufin haduwan ruhi na maurata yan da ruhin mauaratan zai komai guda a jikin biyu, ta yanda duk rayuwan su zai koma cikin maamular su da kuma rayuwansu a fiska daya, Ko wannen su yana kokarin taimakon dan uwansa wannan shine ake kira da gushewan ruhi a cikin wani ruhi, wanda wannan irin mu’a mala da ake samu tsakanin su shike sa maurata su sami cikakkiyar rayuwa kwarai na duniya da kuma na lahira , Kowa zai ke kokarin kare hakkokin da ke tsakanin su na rayuwar aure sabida kowa na jin ba ban banci tsakanin juna, zasu ke kokarin biya wa juna bukatun su in dai ba ya kasance sabon Allah ba

Amma in ya kasance a tsakanin su akwai fada da gaba da rashin son juna ko da daya da ga cikin sune kejin haushin daya nanne kuma soyayyan da ke tsakanin su zai fara gushewa, sai maganar rabuwa na jiki ya fara nuna kansa sabida aukuwan rabuwan ruhi da ya faru a tsakanin su, wannan zai janyo matsaltsalu da dama a tsakanin su kamar fadace fadace da bacin rai.

Anan ne za’a samu wasu daga cikin abokanai ko yan uwa da zasu shiga tsakani don sulhu a tsakanin ma’aurata da bada shawarwari don neman zaman lafiya, sai dai wani abun da mutane ke gafala akai shine duk wannan matsaloli na farowa ne da shi kan sa dan adam din, wani lokaci kuskure ne da rashin sani, ko kuma rashin sanin ainihin illar da ta janyo irin wannan rarrabuwa, amma idan aka gano ainihin illa ko kuma matsala magance ta zai kasance me sauki ne, sai ansan ciwo ake sanin maganin da yafi dacewa

Ya kamata ga duk wanda zaiyi sulhu a tsakanin ma’auratan yasan ainihin illar da ta janyo rarrabuwa a tsakanin su, sabida ta wannan hanyar ne zai iya gano hanyar magance ita illar, idan kuma ba’a sami tsayyar matsala ba toh dole shi me sulhu ya bude wata hanya don qulla wata sabuwa alaqa tsakanin su masoyan, kowa ya karbi laifin sa sabida kowa ana hukunta shi ne bisa aiyukan da ya aikata وكلّ نفس بما كسبت رهينة

Duk da dai wasu illoli da matsaloli dake bijiriwa tsakanin ma aureta zai komane zuwa sanin Allah, wato ba wanda ke da masaniya akai sai Alllah (swt). Irin wadannan matsala Allah ne kawai da manzon sa da kuma imamai su suke da masaniya akan hanya da tafi dacewa wurin magance su, duk wanda ya yi amfani da wadannan hanyoyi da Allah da manzon sa suka gindaya wurin magance matsaltsalun da ke damun sa za’a irgo shi a matsayin shi’a

Domin Allah ma daukakin sarki ya baiwa dan adam hanyoyi ma su sauki na fita da ga duk wani matsala da ta shafeshi na duni da kuma na lahira, kamar neman sauki da dai sauran su, wannan hanya itace addu’a. me ake nufi da addu’a?

Da wannan tamabayan zamu shiga ban gare na biyu daga cikin bahasin mu.

Nuquda ta biyu: bayani kan addua, Allah madaukakin sarki ya bayyana ma’anar addu’a da kuma manufan halittan dan Adam cikin ayar sa da yake cewa ﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ kuma yazo a hadisi cewa

(الدّعاء مخ العبادة) wato addu’a jigon ne na ibada.

Wannan bayani na nuna cewa addu’a na daga cikin asalin usuli na falsafar halittar dan adam, domin Allah shine shugaba kuma ya halicci bawansa ne don ya bauta masa, sabida shi bawa da wannan ibadar ne zai isa ga sa’ada kuma ya kasance khalifan Allah a sunayen shi da kuma siffofin shi.

Addu’a ta na da kyau a ko wacce hali kuma shi dan Adam da abun da ya mallaka duk na Allah ne kuma shi dan adam baya isar wa kan sa da wani alheri ko sharri kuma baya kashewa kuma baya rayarwa, wannan shine nuni na cikkar Allah.

Akwai dalili da dama daga hadisai wanda suke nuni akan falaloli addu’a cikin rayuwar dan adam, dabadin addu’a da dan adam yakeyi ba da Allah be kula shi ba kamar yadda Allah ke fadi cikin littafin sa

﴿ قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاؤُكُمْ ﴾ addua na nufin neman biyan buqatu akan komai daga na sama da kai, yazo a hadisin qudsi cewa annabi musa yakan raki Allah komai har gishirin abincin sa ko kuma idan igiyar takalmin sa ya tsinke ya kan roqi Allah.

Ta hanyar Addu’o’I da tawassili ne ake samin sauki kan warware matsaloli na rayuwa da kuma taimako wurin saukaka wahalhalu da matsaltsalu, Allah na cewa cikin littafin sa

﴿ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَابْتَغُوا إِلَيْهِ الْوَسِيلَةَ وَجَاهِدُوا فِي سَبِيلِهِ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ ﴾

Sharidodin karban addu’a na farko shine imani, da kuma tsoron Allah a kawacce fuska a misdaqi ne ko na ma’ana, sharadi na biyu kuma shine shine jihadi a hanyar Allah ya shifi duka bangarorin jidadi

(بالأصغروالأوسط والأكبر) ita kuma matsakaiceciyar hanya itace tsakanin wanna sharidda biyu itace tawassili da neman kamun kafa zuga Allah ta duk wani hanyar da zai iya isar da kai izuwa gare shi kamar mutum yayi itirafin zunuban shi, da kuma tsai da sallah da yin azumi da sadaka da dai sauran su, abin da kuma yafi wadannan aiyuka falala a duniya da lahira shine tawassili da fiyayyen halitta Annabi Muhammad da iyalan gidan sa (بفاطمة الزهراء, وأبيها وبعلها وبنيها الأئمة الأحد عشر) sannna zaka iya yin tawassili da salihai da mumunai bayin Allah maza da mata rayayyu da kuma matattu domin su rayayyune a gun Allah kuma masu arzirtawa, Allah ya ba su izinin ceto da karban addu’o’I da kuma biyan bukatu, sabida su wata hanya ce ta neman biyan buqatu zuwa ga Allah da kuma hanyace da ta hada sama da kasa, kuma su fuskar Allah ce wanda waliyyan Allah ke fuskantar Allah da ita,

(فأذكر إسم ربك، وتبتّل إليه تبتيلاً في كمال إنقطاعك إليه، في إطاعة أمره، وكن من الذين يبتغون إلى ربهم الوسيلة)

Ana rokon Allah ne akan falalarsa baa akan adalcin sa ba

﴿ وَاسْأَلُوا اللَّهَ مِنْ فَضْلِهِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيماً ﴾. Sabida shine me mulkin sama da kasa, toh duk wanda ya kasance mamallakin komai kuma yana da masaniya akan komai shine za’a iya rokon falalarsa, sannan shi kuma zai amsa addu’ar maroki da masaniyarsa, shi kuma addu’r da be samu karbuwa akan lokaci ba shine

(لعلّ الذي أبطأ عني هو خير لي، لعلمك بعاقبة الأمور), sannan na kasance me godiya bisa samun damin rokon falalarsa da nayi da kuma kasancewa kunlum cikin masu rokon sa dare da  rana.

Falalar Aduu’a cikin Al’qur’ani

1 ـ ﴿ وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِي إِذَا دَعَانِي ﴾.

2 ـ ﴿ ادْعُوا رَبَّكُمْ تَضَرُّعاً وَخُفْيَةً إِنَّهُ لا يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ *وَلا تُفْسِدُوا فِي الأَرْضِ بَعْدَ إِصْلاحِهَا وَادْعُوهُ خَوْفاً وَطَمَعاً إِنَّ رَحْمَةَ اللَّهِ قَرِيبٌ مِنْ الْمُحْسِنِينَ ﴾.

3 ـ ﴿.. إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ الدُّعَاءِ ﴾.

4 ـ ﴿ قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاؤُكُمْ ﴾.

5 ـ ﴿ أَمَّنْ يُجِيبُ الْمُضطَرَّ إِذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ وَيَجْعَلُكُمْ خُلَفَاءَ الأَرْضِ أَئِلَهٌ مَعَ اللَّهِ قَلِيلاً مَا تَذَكَّرُونَ ﴾.

6 ـ ﴿ فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ ﴾.

7 ـ ﴿ وَقَالَ رَبُّكُمْ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ﴾ 

Amma yazo cikin hadisai da dama

1. Daga zurara ya ji daga abu ja’afara yana cewa Allah cikin littafin sa me girma nacewa ﴿إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ﴾ wannan shine addu’a kuma fiyayyen ibada shine addua, zurara yacce

﴿ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لأَوَّاهٌ حَلِيمٌ ﴾ sai yace abin da ake nufi da الأوّاه shine me yawan addu’a.

2. sudair ya tambayi ab ja’afar: wacce ce fiyayyar ibada? Imam yace ba abin da yafi agun Allah face ka tambaye shi biyan bukatun ka, kuma ba wani abin da Allah yafi tsana face mutum ya qi tambayar sa komai.

3. daga maisar bn abdulaziz ya daga wurin abi Abdullah cewa imam yace min ya maisar ka roka kar kace abu ya wuce, sabida a gun Allah akwai matsayi da sai an tambaya zaa samun amsa, inda ba wa zai rufe bakin sa ya qi tamabayar wani abu, ba za’a biya masa bukatun sa ba, idan ka tambaya za’a b aka, domin ba kofar da bawa zai kwankwasa face an bude masa ita.

4. abu ja’afar nacewa: duk wanda baya rokon falalar Allah to zai kasance faqiri.

5. An rawaito daga abi Abdullah: ce wa amiril muminin na cewa mafi soyiwan aiki cikin aiyuka a gun Allah shine Addua, kuma imam ya ce: amiril muminina ya kasance mutum me yawan addua ne.

6. Fiyayyen halitta na cewa: Addua makamin muminine, kuma jigon Addinine, kuma Hasken sama da kasa ne. 

7. An rawaito daga amiril muminin: Addua mabudin bukatu, kuma ma nunin hanya ne, adduar da yafi karbuwa shine adduar da yafito daga tsarkakkiyar zuciya, kuma shine me janyo ceto, idan aka nema da ikhilisi zai kasance khalis, duk wanda yake cikin matsala zai fi dacewa ya nemi mafita daga gun Allah.

8. an rawaito daga abi Abdallah: cewa bana muku nasiha da makamin da zai cece ku daga hannun makiyan ku ba, kuma zai isar da ku zuwa arzikin ku? Sai sukace eh, sai yace ku roki ubangijin ku dare da rana, sabida makamin mumini shine addua.

Sabida haka Addua makamin annabawa ne kuma makariyar muminai ne, yana rushe balai wanda zai sauko da kuma wanda be sauko ba, kuma magani ne na kowa ni ciwo, kusani cewa balai abu ne na dan lokaci kadan, duk wan da ke son adduar sa ya karbu to ya roka a lokacin da yake cikin wadata, idan mutum me yawan addua ne balai bata sauka masa, yin addua yafi karanta Alquani ﴿ قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاؤُكُمْ ﴾ kuma ba wani mumini da zai roki Allah ba tare da an biya masa bukatun sa ba, sai dai ko abiya masa anan duniyane kuma a biya masa a can lahira, kuma Allah ya canza masa da yafiyanh zunuban sa iya ka yawan addu’o’in sa, mutane sun kasance ajizai wurin yin addu’a, da addua ne dan adama zai iya kusan ta ga Allah.

فالدعاء: إبتهال إلى الله بالسؤال والرغبة بما عنده من الخير والإقبال والإنقطاع إليه، وقد يطلق الدعاء على الذّكر أيضاً، كما روى عن النبي’: (أفضل الدعاء الحمد لله) قيل: لأنه سؤال لطيف يدّق مسلكه...

Daga karshe: an rawaito daga hadisin arafa cewa annabin tsira na cewa: yawancin addua na da kuma adduar annabawa shi ne addua kafin arafa

(لا إله إلّا اله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كلّ شيء قدير) sabida shi kamar godiya da girmamawa da kuma yabo ne don neman samun karbuwan addu’o’I daga Allah madaukakin sarki.

والآن بعد بيان هاتين النقطتين، حان أن ندخل في صلب الموضوع، فهذه تحف وهدايا من كتابي (زبدة الأسرار في الختومات والأذكار) ولم يطبع، وعسى أن يطبع بعد موتي ورحلتي إلى ربي الكريم الحليم العظيم.

Bayan bayanai da mukayi akan wadannan kishiyoyi, yanzu kuma zamu shiga cikin asalin mauduin mu wanda muka dauko daga cikin littafina me suna (زبدة الأسرار في الختومات والأذكار) wanda baa sami daman buga shi ba, kuma ina fatan a bugashi bayan mutuwa na

وفدتُ على الكريم بغير زادٍ        من الحسنات والقلب السّليم

فحملُ الزاد أقبحُ كلّ شيء       إذا كان الوقودُ على الكريم

Don haka dole mu nemi biyan buqatu da ga gun Allah, sabida shi me karamci ne baya maida bawansa, baya kunyatar da duk wanda ya kwankwasa kofarsa.

(الحمد لله الأول قبل الإنشاء والإحياء، والآخر بعد فناء الأشياء، العليم الذي لا ينسى من ذكره، ولا ينقص من شكره، ولا يخيب من دعاه، ولا يقطع رجاء من رجاه)

 

Ga wasu addu’o’I da zikiri kan ma’aurata

1. SOYAYYA (ختم سورة الحمد للمحبّة)

Ma aurata masu halartacciyar soyayya, idan soyyarsu ta kasance tayi sanyi, to duk Wanda ya karanta suratul hamd (سورة الحمد) ta wannan hanyar Na tsawon kwanaki bakwai safe da yamma da ikon Allah zai Sami nasara Kan dawowar soyayyar su.

1. BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ka mallakamin wane ko wance (sai a kirayi sunan wanda ake so sunan sa/ta da sunan mahaifin sa/ta)

2. AL HAMDU LILLAHI RABBIL ALAMIN (يا رقيب سخّر لي قلبه أو قلبها) idan namijine sai ace قلبه idan kuma macace sai ace قلبها

3. ARRAHMANIR RAHIM (يا ودود سخّر لي) sai a ambaci suna Wanda ake so a mallaka

4. MALIKI YAU MIDDIN (يا رقيب سخّر لي قلبه أو قلبها) idan namijine sai ace قلبه idan kuma macace sai ace قلبها

5. IYYAKA NAA BUDU WA IYYAKA NASTAIN (يا ودود سخّر لي) sai a ambaci suna Wanda ake so a mallaka

6. IHDINAS SIRADAL MUSTAQIM (يا رقيب سخّر لي قلبه أو قلبها) idan namijine sai ace قلبه idan kuma macace sai ace قلبها

7. SIRADAL LAZINA ANAMTA ALAIHIM (يا رقيب سخّر لي قلبه أو قلبها) idan namijine sai ace قلبه idan kuma macace sai ace قلبها

8. GHAIRIL MAGHDUBI ALAIHIM (يا رقيب سخّر لي قلبه أو قلبها) idan namijine sai ace قلبه idan kuma macace sai ace قلبها

9.  WALAD DALIN (يا ودود سخّر لي) sai a ambaci suna Wanda ake so a mallaka

2.KAN SOYAYYAR MA’AURATA

. Zai Sami makwancin su sai ya rubuta wannan addu’a ya manna

(بسم الله الرحمن الرحيم إبراهيم خليل الله موسى كليم الله عيسى روح الله محمد حبيب الله ورسول الله، لو أنزلنا هذا القرآن على جبل لرأيته خاشعاً متصدعاً من خشية الله وتلك الأمثال نضربها للناس لعلّهم يتفكرون أَلَم نشرح لك صدرك ووضعنا عنك وزرك الذي إنقض ظهرك ورفعنا لك ذكرك فإنّ مع العسر يسراً إنّ مع العسر يسراً فإذا فرغت فانصب وإلى ربك فارغب)

3.DON MALLAKAR ZUCIYA

Zai Sami sunan wanda ya ke so ya malliki zuciyarsa ko nata sai ya jera haruffan sunan da wa dannan sunayen na Allah

ألف (الله) ب (رحمن) ج (رحيم) د (مالك) هـ (قدوّس) و(سلام)  ز(مُؤمن) ح (ميهمن) ط (عزيز) ي (جبّار) ك (متكبّر) ل (خالق) م (بارئ) ن (مصوّر) س (غفّار) ع (قهّار) ف (وهّاب) ص (رزّاق) ق (فتّاح) ر (عليم) ش (قابض) ت (باسط) ث (حافظ) خ (رافع) ذ (معزّ) ض (مذل) ظ (سميع) غ (بصير).

Misali in sunan Wanda ake so a mallaka Muhammad ne za’a dauki haruffan sunan sa wato م ح د sai a jera da sunan Allah da ke sama wanda yayi daidai da wannan harufa. Addu’ar zai kasance kamar haka kenan

(اللهم إني أسئلك يا بارئ يا مهيمن يا مالك أن تسخّر لي قلب محمّد) sai a ambaci sunan da sunan mahaifinsa da Na mahaifiyarsa tare da soyayya

Wannan addua yana karbuwa ne alokacin da soyayyar ya halasta ashara’ance amma idan na haramunne wato soyayyar da be dace ba adduar zai kasance akasin abinda ake nema, kamar yanda Alqur’ani me girma zai iya kasancewa ceto ne ga muminai فإنه شفاء ورحمة للمؤمنين wani lokaci kuma zai iya kancewa hasara ne ga azzalumai baya kara musu komai face hasara ولا يزيد الظالمين إلّا خساراً، فلا تغفل

4. SOYAYYA TSAKANIN MA’AURATA

Mutum zai iya rubuta wadannan sunaye sai ya sanya Akan makwancin mauaratan da suka tsani juna, sabida wannan addu’a Na canza tsana zuwa soyayya da izinin Allah. Ga sunayen

طسوم طسوم سوم سوم علوم علوم كلوم كلوم حيّوم حيّوم قيوّم قيّوم ديّوم ديَوم سبحان من بذكره تطمئن القلوب اطمئن قلب (sai a ambaci sunan mijin da na mahaifin sa ) بمحبّة (sai a ambaci sunan matar da na mahaifinta)

Sannan sai aci gaba

 اللّهم ألفّ بينهما كما أصلحت بين محمّد ’ وأنصاره، اللّهم يا من أدخل محبّة يوسف× في قلب زليخا، ويا من أدخل محبّة موسى × في قلب آسية بنت مزاحم، ويا من أدخل محبّة محمد ’  في قلب خديجة بنت خويلد، ادخل محبة (wane) في قلب (wance) (أو ادخل محبة فلانة في قلب فلان sai aka ambaci sunan ma’auranta) كما أدخلت الليل في النّهار، والنّهار في الليل.

 

Sai ka ci gaba da cewa

﴿لَوْ أَنفَقْتَ مَا فِي الأَرْضِ جَمِيعاً مَا أَلَّفْتَ بَيْنَ قُلُوبِهِمْ وَلَكِنَّ اللَّهَ أَلَّفَ بَيْنَهُمْ إِنَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٌ﴾ ولا حول ولا قوة إلا بالله العلي العظيم.

Za’a rubuta wannan adduar da zaafaran da ruwan warda (ماء الورد) a daidai goshin fitowar rana a ranar juma’a.

Tunasarwa Na muhimmi

Zai fi dacewa mutum in Yana da buqatu agun Allah ya ke yawaita addu’ar sa da sunayen Allah ko kuma kafin ya fara addu’a ya yawaita neman gafara daga zuniban sa sabida zunubai sukan sanya addu’a yaqi karbuwa, shi addu’a akwai kala daban daban duk wani buqatun da dan adam yake dashi akwai addu’a da zikiri da yafi dacewa

Sabida hakane muke kawo muku addu’o’I daban daban don samin nasara kan buqatun da ake dashi, samu yana daga me nema, kuma Allah baya kauda fuskarsa ga bawarsa donmin shi Allah yana son bawansa sosai yazo cikin hadisin manzo dake cewa

Wani lokaci dalilin da yasa Allah baya karban adduar bayin sa a kan lokaci sabida yana so yake yawan jin muryar bawansa ne ta hanyar Addu’o’I da kuma zikiri, kuma shine yake da masaniya akan halin da bawansa ke ciki da kuma abin da yafi dacewa da shi, sabida shi me karamci ne kuma me hikima ne kuma masani.

Allah subahanahu wata’ala Yana karban duk wani addu’a in har ya cika sharudan da ya kamata kuma mukayi tawakkuli da Allah.

(ولعلّ الذي أبطأ عنّي هو خير لي لعلمك بعاقبة الأمور، فلم أرَ مولىً كريماً أصبر على عبد لئيم منك عليّ....) 

Tura tambaya