lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

WANENE YA FI HATSARI TSAKANIN NAFSUL AMMARA DA SHAIDAN?

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Dukkanin godita tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Bayan haka: ta yiwu wannan tambaya ya zamanto ya fada cikin tunanin wasu ba’ari daga matasa sakamakon tarin sanin da suke da shi ko kuma bisa amsa bukatar halittarsu ta son neman tsinkaya kan abin da ya faku daga garesu, ko kuma sakamakon shiga sharar da ba shanu, ko kuma ya kasance daga babin barkwanci wannan tambaya mai hatsari ta fado tunaninsu cewa babu shakka Shaidan jefaffe ya sabawa ubangijinsa ya kuma halaka ya bata, amma to shi wanene Shaidaninsa da ya zama dalilin halakarsa? Lokacin da mutum ya sabawa ubangijinsa sai aka tambaye shi me yasa ka sabawa masa, lallai zai ce: Shaidan ya ribace ni, tun farkon al’amari dama Shaidan ya rantse cewa zai yi kiyayya da da mutum kuma sai ya halakar da shi face wanda ya kasance daga katangaggun bayin Allah wadanda ya shinge su domin kansa bayan sun kasance sun katange kawukansu daga saba masa da kuma tsarkake ayyukansu dominsa, ko da yaushe suna tuna lahirarsu cikin ayyukansa na gargaru.

Tambaya shi wai wannan Shaidan din wanene ya kasance Shaidaninsa sababin halakarsa?

Amsa: hakika Allah ya halicci Nafsul Ammara cikin mutane da aljanu shi kuma Shaidan ya kasance daga aljanu tsiyatarsa da Nafsul Ammararsa suka yi galaba kansa, sai ya sabawa ubangijinsa, ita dama Nafsul Ammara ta kasance cikin mutane da aljanu  kuma sune wadanda Allah ya kallafa ibada a kansu (ban halicci aljanu da mutane face domin bauta mini) hakika ubangiji ya baiwa mutum da Aljani cikakken yanci da zabi, basu kasance misalin Mala’iku ba cikin bauta masa, lallai su Mala’iku sun kasance an halicce su kan bauta da tasbihi basa sabawa umarnin ubangiji.

Ita Kalmar Nafsu kalma ce mai matukar hatsari musammam ma cikin mutum m lallai nafsunsa wacce take cikin tsakankanin geffansa biyu itace mafi tsananin kiyayya da shi, cikin Kur’ani mai girma an ambaceta cikin ayoyi masu da misdakai da yawa, kamar yanda ya gabata babu kaifi mu kawo jumla daga cikinsu, hakika matsarkaki cikin suratu Kafu ya ce: ( hakika mun halicci mutum mun san abin da yake zuciyarsa take masa wasiwasi da shi kuma mu ne mafi kusanci da shi daga jijiyar wuyansa) , kamar yanda Ubangi shi ne yake (shiga tsakanin mutum da zuciyarsa)  duk wanda ya kasance mumini yayi Imani da Allah Azza wa Jala zaka same shi yana tunawa da shi yana yin sallah da azumi yana kuma karanta Kur’ani yana ciyarwa yana aikata ayyukan alheri , sai dai cewa tareda haka wani lokacin yana cudanya aiki mai kyawu da mugunya sai ya afaka cikin aikata zunubi,

Abin ban mamakin shi ne ta kaka mutum zai ce yayi Imani amma kuma yana aikata sabo?

Amsa: dalili da sababin hakan shi ne mun yi sakaci da babban Makiyi na asali na hakika wanda makaminsa ya kasance mafi kaifin makamai, sai muka karkata wurin raunannan Makiyi muka dora dukkanin laifukanmu kan wuyansa, bamu tuhumi kawukanmu ba, lallai kaidin Shaidan kan Mumini ya kasance mai rauni  (hakika kaidin Shaidan ya kasance raunanna) duk wanda mijinginarsa da madogararsa ta Allah mabuwayi karfaffa ta kaka Shaidan zai yi tasiri a kansa.

Kadai babban Makiyi na asali shi ne zuciya Nafsinmu, lallai ita kamar misalin nakiya da aka `dana kan iyakakken lokaci d atake cikin zuciyar mutum, Allah matsarkakin Sarki yana cewa: ( ka karanta littafinka ya isar ya zama mai hisabi a kanka) haka zalika ya ce (yau za a sakawa dukkanin rai bisa abin da ta aikata yau babu zalunci lallai Allah mai saurin hisabi ne), girmansa ya girmama ya ce: ( kowacce rai tana jingine da abin da ta aikata).

Fadinsa ta’ala cikin suratu Annazi’atu: (amma wanda ya ji tsoran gamuwa da ubangijinsa ya hana ransa abin da ta ke so daga sabo lallai aljanna ce mafakarsa) haka kuma wanda ambatonsa ya daukaka ya ce: (rai ta san abin da ta hallarar).

Da wasu ayoyin da suka zo da batun nafsu, yayin muka kalli wadannan ayoyi da ambatonsu ya gabata zamu same su suna kai kawo a da’ira guda daya shi ne Kalmar nafsu, wai mene ne wannan nafsu din da take cikin mutum  kamar yanda akwaita cikin aljani, sakamakon samuwarta ne Allah ya kallafawa mutane da aljanu bauta masa, domin sukai ga samun lada su azurta duniya da lahira, Allah mabuwayi yana cewa: (ban halicci aljanu da mutane sai don su bauta mini) daga abu mai kyawu da za iya fada cikin wannan babi, bari dai yana daga hikima da amfani da hankali da lura da fadaka shi ne cewa iyayen gijin da aka kasance ana bauta musu a zamanin jahiliya koma bayan Allah misalin (Allatu da Uza da Manatu da Suwa’u da Wudda da Yagusa da Ya’uka da Nasara) dukkanin wadannan gumaka da suka kasance a zamanin Jahiliya a yanzu babu su babu labarinsu duk an rushes u babu abin da ya rage sai Kissoshinsu kan takardun tarihi da kuma isharar da Kur’ani yayi kansu.

Bautar gumaka ta gushe babu abin da ya rage sau bautar jabun ubangiji wanda shi ne biyewa son rai, Allah yana cewa: (ashe baka ga wanda ya riki son ransa matsayin ubangijinsa ba) ma’ana shi ne shi biyewa son rai mai yawan umarni da mummuna idna yayi galaba kan mutum sai ya hau kansa kamar yanda SHaidan daga aljannu da mutane suke hawa kans, lallai zaka same shi yana kafircewa ayoyin Allah na sasanni da na kawuka da rubutattu cikin litattafan da suka zo daga sama da Kur’ani  mai girma (sannan karshen wadanda suka munana miyagun ayyuka zai kasance suna karyata ayoyin Allah)

Saboda haka ne zaka same mai biyewa son rai yana aikata dukkanin abin da ron sa take sha’awa ko da kuwa yayi baran-baran da hankali da masu hankali da shari’a tsarkakka, sai ya zama kamar misalin dabbobi cikin mu’amalarsa bari dai yafi su batan hanya.

Ya zama tilas a yaki son rai a saba masa domin son rai shi ne mafi hatsarin makiyi shi ne makiyi na boye shi kuma Iblis na bayyane wanda sojoji daga mutane da aljannu suke tallafa masa, ashe Kabila bai kashe `dan’uwansa Habila ba lokacin da ransa ya sawwala masa ya kayata masa yin hakan ( sai ransa ya kayata masa kashe `dan’uwansa sai ya kashe shi)

Ka tambayi duk wanda ka so? Ka tambaye shi lokacin da yake aikata zunubi da sabo sannan daga baya ya tuba yayi nadama, wanne abu wanene ya kirayeka zuw aga aikata zunubi da sabawa Allah matsarkaki? Da sannu zai ce maka Shaidan ya halakar dani ya rudar dani, wannan na nufin Shaidan shien sababi na fari a bayan dukkanin zunubi da ake aikatawa, shi ko mutum wankakke ne kubutacce ne, idan haka ne to me yasa ake yiwa mutum da zarginsa kan laifin da yake gangarowa daga gare shi?

Alal hakika shi kaidin Shaidan yana da rauni, sai dai cewa idan mutum ya zama yafi raunana daga Shaidan, lallai zaka samu Shaidan yayi galaba kansa a fagen daga, hakan na biye da raunin mutum cikin imaninsa da aikinsa na gari daga cikin zuciyarsa, saboda mafi kiyayyar daga makiyanka itace zuciyarka da take tsakankanin geffanka, itace take umartarka da aikata miyagun ayyukada alfasha da munkarai, ya zama wajibi kanka ka yaketa kayi jihadi kanta da mafi girman jihadi. Ka d aka mika ragamar lamarinka gareta lallai zata jaka zuwa ga aikata sabo, sannan daga waje Shaidan zai taimaka mata kan aikata sabon, saboda haka wanda za a fara tambaya da farko kan sabo shi ne kai kuma kai ne wanda kafi cancanta da ayi azaba da ukuba a kanka, saboda ai zuciyarka ce ta kayata maka aikata kisa da zina da cin gulma cin naman mumini  wacce ta kasance mafi tsananin laifin daga zina, wa’ayazubillahi.

Duk da cewa Shaidan ya kasance makiyi mabayyani kuma dole ayi taka tsantsan da shi dole mu san makamansa masu hatsari, da wanne makami ne zai zai kawo mana hari da zamu tunkude shi da addu’a da neman tsarin Allah domin shi ne mai taimako da tallafawa, kuma mu daura damara da makamin Annabawa Addu’a kamar yanda ta kasance makamin Muminai mazanasu da mata, babu makawa Shaidan makiyi ne mai hatsarin gaske, sai dai cewa zuciya tafi shi hatsari ta fishi zama barazana da tsananin kiyayya da kafirci, hatta shi kansa Shaidan zai barranta daga zuciyar `dan Adam ranar lahira, zai ce shi fa yana tsoran Allah kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukaki: (kamar misalin Shaidan yayin da ya cewa da mutum ka kafirce bayan mutum ya kafirce sai Shaidan ya ce lallai ni ina barranta daga gareka lallai ni ina jin tsoran Allah ubangijin talikai*sai karshensu su biyun ya kasance cikin wuta suna masu dawwama cikinta wadancananka shi ne sakamakon Azzalumai). Babu laifi muyi Ishara ya zuw aga jumla daga makaman Shaidan kamar yanda ya zo cikin wannan addu’a mai daraja addu’a ta farkon yinin watan Ramadan mai Albarka wacce ta zo cikin littafin (Almafatihul Jinan) wallafar Shaik Abbas Qummi Allah yayi masa Rahama, da farko zaka fara yin salati ga Annabi (s.a.w) da iyalansa kamar yanda muke hattama addu’o’inmu da da salati kamar yanda aka yi mana alkawari da cewa idan muka kewaye addu’ar da salati daga farkon ta zuwa karshe za a karbe ta ba za ayi wurgi da it aba, a cikin wannan gutsire daga addu’a anyi ishara zuwa ga makamai dai-dai har guda 22 daga makaman Shaidan: (ya Allah ka yi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad ka bani kariya cikinsa cikin watan Ramadan daga Shaidan jefaffe daga kifcensa da yaficensa da hurinsa da kumburawarsa da wasiwasinsa da jinkirtawarsa da damkarsa da kaidinsa da makircinsa da tarayyarsa da masoyansa da yaudararsa da burace-buracensa da rudarwarsa da fitinarsa da raminsa da kungiyarsa da mabiyansa da shi’arsa da waliyyansa da abokanan tarayyarsa da dukkanin makirce-makircensa Allah kayi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad).

Babu kokwanto cewa wannan makamai nasa masu hatsari ne cikin kowacce gaba akwai bukatar dogon sharhi da ta’aliki da Karin bayani, alal misali (tarayyarsa) lallai ishara ce zuwa ga ayar mai girma cikin Kur’ani mai girma kamar yand aya zo cikin tafsirinnta da tawili kaka Shaidan yake tarayya da mutum cikin samar da zuriya yayin kusantar iyali yayi tarayya da shi cikin kwayar halittar yaron  idan mutum bai yi bismillah bai ambaci Allah gabanin kusantar iyali, Allah matsarkaki yana cewa (yayin da muka cewa Mala’iku ku yi sujjada ga Adamu sai suka yi face Iblis ya ce yanzu zan yi sujjada ga wand aka halicce shi daga yunbu tabo* ya ce  ka ganka ko! Wannan da ka karrama shi a kaina da zaka jinkirta mini zuwa ranar lahira lallai zan karkatar da zuriyarsa illa kadan daga cikinsu* ya ce ka je duk wanda ya bi ka daga cikinsu lallai Jahannam ace sakamakonku sakamako cikakke* kuma ka rikitar da wanda ka samu daga garesu da sautinka ka kuma yi hari kansu da dawakinka da dakarunka ka yi tarayya da su cikin dukiya da da `ya`ya ka yi musu alkawari alhali Shaidan ba ya yi musa alkawari da komai face rudu* lallai bayina baka iko kansu ubangijinka ya isar ya zama Wakili).

Daga cikin muhimman mashigar Shaidan da yake samun iko da dama kan bayin Allah ya halakar da su ya batar da su ya riskar da su cikin kungiyarsa da Kabilarsa da abokanan tarayyarsa shi ne mahsigarsa ta mantuwa, lallai yana mantar da kai tunawa da zuciyarka nafsunka ta mutuntaka da Malukutiyya wacce take tareda kai cikin ayyukan alheri sai ya dinga tunatar da kai da nafsul ammara  wacce take tunkuda ga miyagun ayyuka, duk wanda ya manta da nafsunsa ta mutuntaka za a jarrabe shi da nafsul haiwaniyya ta dabbanci, lallai zai manta da Allah matsarkaki (yaku wadnada sukayi Imani ku ji tsoran Allah rai ta tuna da abin da ta yi domin gobe ku ji tsoran Allah lallai Allah masanin abin da kuke aikatawa ne* kada ku zama kamar wadanda suka manta da Allah sai ya mantar da su kawukansu wadancananka sune Fasikai* `yan wuta ba zasu taba daidaituwa da `yan aljanna ba su `yan aljannu sune rabautattu).

Kamar yanda yake mantar da kai lahira da ladanta da ukubarta, sai dai cewa dalili da sababi na farko itace nafsu ranka zuciyarka mai umarni da miyagun ayyuka itace ke sharewa Iblis hanya da yi masa shimfida domin ya samu damar iko da salladuwa a kanka (bana iya barrantuwa da kubuta daga kaina, lallai ne rai mai yawan umarni ce da miyagun ayyuka face dai abin da ubangijina yayi rahama)

Ya zama dole ayi addu’a da magiya da Kankan da kai ga ubangiji da kuka domin ubangiji ya kubutar da mu daka sharrukan kawukanmu da sharrukan Shaidan da Ashararai daga mutane da aljannu, daga cikin addu’o’I cikin wannan babi : ( ya Allah lallai ni na zalunci kaina da yawa, kuma babu mai gafarta zunubai face kai, ka gafarta mini da gafara daga gareka, ka yi mini rahama lallai kai mai gafara da jin kai ne)

Babu shakka cewa kadai dai mutum yana samun dacewa cikin tsarkake kansa da taimakon Allah matsarkaki (kai kadai muke bautawa kuma daga gareka kadai muke neman taimako) an karbo daga shugabanmu Sarkin Muminai Ali (a.s) cikin Nahjul Balaga ya ce: (yaku bayin Allah lallai daga mafi soyayyar bayin Allah zuwa gare shi shi ne bawan Allah da Allah ya bashi taimako a kan ransa)  

Tura tambaya