lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

YAYA ZAN RUBUTAWA YARA KISSA

Hakika duk wani wayayyen Balarabe marubuci ya na fadake da cewa kissoshin da aka tarjama daga turawan yamma basu bada fa'ida mai kyawu da iayayen yara ke fata yaransu su yi tsinkayi kansu, yaro karami Balarabe yana bukatar kissoshi da suke magana kan duniyar da yake ciki da tafi kusanci da yanayin muhallin da yake rayuwa cik, wacce take magana da harshensa da al'ummarsa da addininsa , wacce take karfafar al'adun mutanensa, saboda haka bakin kissoshi da aka tarjama su basu amfanarwa a wadannan fagage ada muka ambata, duk da nasararsu cikin kwadaitar da yaro cikin yin lafiyayyen tasarrufi, godaddun halaye wasu alamu da akai tarayya cikinsu ga haduffan kissoshi ga kananan yara cikin kowanne yare.


Sinadaran rubuta kissoshin kananan yara:

Mafi muhimmancin sinadarin kissa sune jaruman da aka sanyawa cikin kissar, shi yaro karami a dabi'arsa yana bincike da neman jarumai da zai kwaikwaye su, ya zama dole a samar da wasu manyan mutane da sunayen da suka dace da muhallin rayuwar yaro, ya kuma kasance sun fifitu da siffofi nau'i-nau'i, daga cikin hikima shine samuwar yara da launin wankan tarwata da kuma farare , a samar da lafiyayyu da marasa lafiya, domin ta saba da karbar abubuwa mabanbanta, ya zama wajibi wadanda zasu taka rawa cikin kissa su daukaka daga kananan mutane zuwa jarumai, domin himmar mai bada kissa da kuma yaro da yake sauraro da tattaru kansu yayin rubutu da karatu, kamar yanda ya zama wajibi yaron ya zama ya fifitu dfa siffofi na musammam kamar yanda a galibi yake son ya ga ya kasance Jarumi, wajibi kan yaro ya siffantu da kyawawan dabi'u a dukkanin fagage, kamar yanda yara su kasance suna farin ciki yayinda ake basu labarin kissoshin dabbobi, saboda ba sharadi bane wanda wadanda zasu taka rawa cikin kissa su kasance yaro karami ko cikakken mutum, shi yaro bai muhimmanatar da nau'in jarumi yana muhimmantar ayyukansa da rawar da yake takawa ne cikin habaka.

Habaka: sune abubuwan da suke kunshe cikin kissa bawai ana nufin kulli ba da ita kamar yanda wasu suke zato, ma'ana dai ita ke tsara abubuwa da suke cikin kissa kan mahangar marubucin kissar; kamar yanda mai karatu ke karantawa.

Kissoshin yara suna bukatar sanya muhawara cikinsu da sardi, sannan ana fifita takaitawa cikinsu kan tsawaitawa, domin su kananan yara suna da saurin gajiya da kosawa, sanya muhawara yana taimakawa yaro fahimtar abubu da rayuwa tare da su.

 


Tura tambaya