lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

SIRRIN SALATI

 

An rawaito daga wani mutum cewa ya fada cikin matsancin talauci ta yanda ta kai bashin da yake wuyansa ya kai dinare dari biyar ya kuma gaza biya gashi kuma masu kudin sun matsa masa sai ya biya su.

Sai ya tafi wurin wani dan kasuwa ya ci bashi daga hannunsa da sharadin cewa zai biya shi a ayyanannen lokacin da su ka yi yarjejeniya, da ya karba sai ya tafi ya biya bashi da wadancan mutane suka matsa masa kan ya biya su  bashin d ayaci daga hannunsu, baya an kwana biyu sai yanayinsa ya kara munana da kuntata har ta kai ga lokacin da suka yi yarjejeniya zai biya bashin da ya ci daga wancan dan kasuwa ya zama ya yi gashi kuma bai da ko da dirhami ko dinare daya bari mai dai bashin da yake kansa ya kara tsananta, wannan dan kasuwa ya zo domin karbar kudaden da ya ranta daga hannunsa amma sai ya zama bai samu wannan kudade da yake binsa ba, sai ya tafi ya kai kara wurin Alkali sai Alkali ya yanke hukunci kan tura wannan wand ayaci bashi gidan fursun ba zai fito ba har sai ya biya wannan bashi, sai wanann mutumi ya cewa da Alkali: ya shugabana ka dan jinkirta mini ka bani lokaci zuwa gobe domin in samu damar gayawa matata in kwantar da hankalin iyalina don kada su shiga damuwa kan rashin ganina, sai Alkali ya ce menene zai lamintar damu cewa zaka je ka dawo ba zaka gudu ba?

Sai mutumin ya ce lamini na shi ne Manzon Allah (s.a.w) idan har ban dawo to kai shaida kaina lallai ni ba na daga al’ummar Muhammad (s.a.w) wannan Alkali ya kasance mutukin kirki sai ya mutunta wannan laminci na mutumin ya karba ya barshi ya tafi wajen iyalinsa.

Sa’ilin da ya dawo gidansa ya baiawa matarsa labarin halin d aya tsinci kansa ciki wannan matar tasa Saliha sai tace masa tun dai Manzon Allah (s.a.w) shi ne lamininka a wurin Alkali to zo mu mu yi salati ga Manzon Allah (s.a.w) saranmu Allah zai kawo dauki ya yaye mana damuwar da muke ciki albarkacin salati sai shi da matarsa suka zauna suka dinga salati ga Muhammad da iyalansa har bacci ya dauke su sai yayi mafarkin Manzon Allah (s.a.w) ya ganshi yana ce masa idan Allah ya kaimu gobe gari yaw aye kaje wajen mai gari k ace ina gaishe shi ka gaya masa Manzon Allah (s.a.w) ya bukaci ka biya bashin da ake bina, idan ya tambayeka wata alama da take gasgata haka? Kace masa akwai alamomi guda biyu? Ta farko itace cewa mai gari ya kasance yana salatin Annabi a kowacce dare kafa dubu bai taba yankewa ba.

Alama ta biyu: shi ne cewa a daren jiya yayi kuskure cikin kidaya adadin salatin ka gaya masa cewa salatinsa ya kammala ya cika kafa dubu.

Yayin da da ya farka daga barcisai yayi gaggawa ya tafi wajen mai gari yayi sallama ya shiga wurinsa sannan ya ce masa Manzon Allah (s.a.w) yana gaisheka ya na kuma bukatar ka biya mini bashi sai ya ce: nawa ne bashin naka ? sai ya ce: dinare dari biyar sai mai gari ya ce: wacce alama ma ce zata gasgata zancenka? Sai mutumin ya ce: akwai alamomi biyu , ta farko itace kullum kana yin salati kafa dubu, sai mai gari ya ce gaskiya ne ya kuma rushe da kuka, sannan mutumin ya ce alama ta biyu kuma shi ne jiya da daddare kayi kuskuren cikin kidaitawa Manzon Allah (s.a.w) ya ce inyi maka bushara da cewa adadin ya cika, sai mai gari ya ce: gaskiya ne ya kara rushewa da kuka sannan ya ce a bashi dinare dari biyar  daga Baitul mali, sannan ya kara bada umarni a bashi dubu biyu da dari biyar  daga aljihunsa na kansa ya ce: wannan karramawa ce da kuma sakamakon isar da sakon gaisuwar Manzon Allah (s.a.w) da kayi, sa mutumin ya fito yana gaggawa zuwa wajen Alkali domin biyan  bashin ya kuma cika alkawarin da ya dauka, lokacin da ya shiga wajen Alkali sai ya samu Alkalin yana zaune yana jiransaa hannunsa ga wata `dan karamin kulli cike da kudi Alkalin ya ce masa: ni ne zan biya maka bashin wannan dinare dari biyar ne daga aljihuna saboda na yi ido biyu da Manzon Allah (s.a.w) albarkacinka da sababinka ya ce mini idan na biya maka bashin da yake wuyanka ranar lahira nima zai sauke mini wanda yake wuyana.

Sai kwatsam ga dan kasuwar nan da yake binsa bashi shima ya shigo yana cewa Alkali ya shugabana hakika na yafe masa bashin da nake binsa ga kuma dinare dari biyar nan hadaya gareshi, saboda naga Manzon Allah (s.a.w) albarkacinsa ta dalilinsa ya ce mini idan ka yi masa afuwa daga bashin mu ma zamu yi maka afuwa ranar lahira.

Sai mutumin ya fito daga wajen Alkali cike da murna da farin ciki yana ta gaggawa zuwa komawa gida ya je ya baiwa matarsa labarin abin da ya faru shi da ake neman ya biya bashin dinare dari biyar amma gashi yanzu ya dawo gida dauke da dinare dubu hudu, hakan ya faru ne albarkacin falala da salatin shugabanmu Muhammad tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi da iyalansa tsarkaka

Tura tambaya