lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kafar sadarwa da wakilci

Imam Jawad (a.s) tare da dukkanin takunkumi da yake ciki daga hana shi nasabta Wakilai amma kuma tareda wannan hali dangantakarsa da kafar sadarwarsa da `yan shi'a bata yanke ba, cikin fadin garuruwan da Sarkin Abbasiyawa yake mulki cikinsu Imam (a.s) ya kasance yana aika wakilai da sakonni domin kiyaye hadin kan `yan shi'a, hakika wakilan da yan sakon Imam sun samu damar fadada aiki da isar da sakonsa cikin garuruwa misalin  Ahwaz, Hamdan,Sistan, Bustu rayyu, Basara, wasid, Bagdaza, da cibiyoyin sunna da shi'a daga Qum da Kufa.

Cikin bahasin tsufan Imam Jawad (a.s) mun rubuta cewa lokacin da Aliyu Ibn Asbad ya gana da Imam ya tsaya a tsanake yayi masa kallon kwakwaf domin kamanninsa sun shiga kwakalwarsa don samun damar yiwa mabiyansa na kasar Masar bayani siffofinsa wanda hakan yake nuna cewa Imam yana da masoya a wannan kasa.

Makarantar ilimi ta Imam Jawad (a.s)

Mun san cewa daya daga manya manyan sasannin rayuwar A'imma shine yada tarbiya da sakafa, wadannan manyan bayin Allah kowanne daya cikinsu cikin rayuwarsa ya kasance yana da wata rawa da ya taka cikin yada tarbiya da sakafa, ya kasance yana tarbiyantar da Almajiransa tareda koyar da su ilimi domin su yada shi cikin al'umma, sai dai cewa tareda haka kowanne daya cikinsu zamaninsa yana banbanta da wadanda suka gabata daga yanayin siyasa da zamantakewa, Alal misali a zamanin Imam Bakir da Imam Assadik (a.s) sun samu kyawuntar yanayin siyasa da suka amfana da shi wajan yada ilimi da tarbiyantar da manya-manyan malaman riwaya da adadinsu yakai dubu hudu, amma daga zamanin Imam Jawad zuwa Imam Hassan Askari (a.s) sakamakon matsi da takunkumin siyasa ayyukansu na yada ilimi da sakafa ya kasance iyakantacce hakan ya sanya ba zakat aba hada su da wadanda suka gabace daga Imamai ba cikin adadin marawaitan hadisai da suka tarbiyantar gaba daya Almajiran Imam  Jawad (a.s) basu wuce mutum 110.[1] sannan gaba daya hadisai 250[2] suka rawaita daga gareshi babu mamaki cikin faruwar hakan sakamakon Imam (a.s) ya kasance matsanancin takunkumi dukkanin maotsinsa yana kan idon hukuma sannan kuma da wuri yayi shahada kamar yanda Malamai suka fada hakika yayi shahada yana dan shekara 25 a duniya, tareda ya kamata mu lura da wani abu guda tareda karancin Almajiransa sai dai cewa yay aye fitattun malamai daga cikinsu misalin Aliyu Ibn Mahziyar da Ahmad Ibn Muhammad Bazandi, Zakariyya Ibn Adam, Muhammad Ibn Isma'il Ibn Bazi, Husaini Ibn Sa'id Ahwazi, Ahmad Ibn Kalid Barki kowanne daga cikinsu ya kasance tauraro a fagen ilimi da fikhu, wasu cikinsu suna wallafe-wallafe masu tarin yawa, sannan a gefe guda Almajiran Imam Jawad (a.s) su kadai ne Marawaitan basu takaita iya da'irar yan shi'a ba, bari dai zaka samu marawaitan Ahlus-sunna suna nakalta daga wajensa da kwasar ilimin muslunci, babban misali cikinsu shine Kadibul Bagdadi ya kasance ya nakalci hadisai na isnadinsa daga Imam Jawad (a.s)

Tura tambaya