lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Zazzakar zuma kan falalar daren Lailatul Kadri

Mukaddima

Mihwari na farko: Ahlil-baiti tare da iyakance lailatul kadri

1 ـ سئل أبوعبدالله الصادق  7 عن ليلة القدر فقال : (اطلبها في تسع عشرة وإحدى وعشرين وثلاث وعشرين)

An tambayi Abu Abdullah Sadik (as) dangane da daren lailatul kadri sai ya ce: ( ku neme shi cikin dararen 19-21-23)

shin Samahatus Sayyid daga wannan hadisi me ya fahimta shin daren lailatul kadri guda daya ko kuma yana da yawa?

2- wadanne gurabe ne akai tarayya cikin su da kuma wadanda akai sabani ciki cikin iyakance daren lailatul kadri tsakanin makarantar Ahlil-baiti da sauran makarantu?

3-shin daren lailatul kadari da Allah ya saukar da kur'ani cikinsa ya kare bayan kammala saukar kur'anin? Ko kuma yana maimaituwa a kowacce shekara? Wanne dalili muke da shi kan hakan?

4-falalar da aka ambata dangane da daren lailatul kadri ya hado da yininsa, ko kuma yana karewa da karewar wannan dare mai albarka? da dai za ku yi Karin bayani zuwa ga mai sauraron ku mai daraja.

5- a bayyane yake Samahatus Sayyid cewa akwai sabani dangane da daren lailatul kadri da yininsa a yankunan duniya, kamar yanda sau da yawa akan samu sabani kan gani watan muslunci, shin tare da faruwar hakan daren lailatul kadri da albarkokin da suke kunshe cikinsa zasu kasance ga wani yankin duniya ban da wani yanki, ko kuma zai mamaye da game sauran yankuna sa sasannin duniya?  Muna saran zaku yi mana Karin bayani dangane da wannan batu?

Mihwari na biyu: cikin hallarar suratul Kadri

1- Allah madaukaki ya ce: (Mala'iku suna sauka) sannan Kalmar Mala'iku a larabce ta zo da sigar jam'i wanda akai masa ado da alif da lamun, wanda hakan yana fa'idantar da gamewa, shin hakan na nufin dukkanin Mala'iku hatta makusanta daga cikinsu suna saukowa a daren lailatul kadri?

2 ـ (تَنَزَّلُ الْمَلاَئِكَةُ وَالرُّوحُ فِيهَا)

Mala'iku da ruhu suna sauka cikinsa.

Shin wurin wa suke sauka? Kuma saboda me suke saukowa?

3 ـ جاء في أصول الكافي عن الإمام الباقر  7 يا معشر الشيعة خاصموا
بسورة إنا أنزلناه تفلحوا..

Ya zo cikin Usulul Kafi daga Imam Bakir (as) yaku jama'ar shi'a ku kafa hujja ga abokan jayayyarku da suratu Inna anzalnahu zaku rabauta….

 Har dai zuwa karshen hadisin. Samahatu Sayyid  mene ne sasannin Akidu wadanda Imam yake nufin su daga wannan riwaya mai daraja?

4- da zamu koma ga kur'ani mai girma da mun samu wurare da dama da Kalmar Ruhu ta zo, hakika madaukaki yayin magana kan halin Maryam (as) ya ce: (sai muka aika mata da ruhinmu) wani wurin ya ce: (suna tambayarka gameda ruhu kace ruhu yana daga lamarin ubangijina, wannan shi ne abin da ya maimaitu cikin suratu Kadri cikin fadinsa madaukaki (Mala'iku suna sauka da ruhu cikinsa) to wai me ake nufi da ruhu cikin wannan aya mai albarka, yaya yake sauka?

5-daga jumlar darajojin lailatul kadri akwai abin da aya mai albarka ta bamu labari

(سَلاَمٌ هِيَ حَتَّى مَطْلَعِ الْفَجْرِ)

Shi daren lailatul kadri aminci har zuwa hudowar alfijir.

Me ake nufi da aminci anan? Daga wanne abu yake kasancewa?

6- hakika kur'ani ya kawo bayanin lailatul kadri da cewa dare da yafi watanni dubu alheri, me ake nufi watanni dubu? me ake nufi daga alheri anan, muna bukatar bayani kan haka.

Mihwari na uku: ayyukan daren lailatul kadri

1- mene ne hikima da falsafar himmatuwar shari'ar muslunci da al'amarin daren lailatul kadari cikin ba'arin wani lokuta koma bayan wasunsu?

2- muna saran Samahatu Sayyid zai yi magana dangane da tsare-tsaren ibada wanda shari'a ta zayyana su cikin wannan lokaci mai albarka ina nufin daren lailatul kadri da yininsa?

3- muna saran Samahatu Sayyid zai kawo mana falalar raya wannan dare mai albarka tareda kawo wasu riwayoyi cikin wannan fage.

4- cikin abin da yake yawo yake kai kawo cikin bakunan mutane shi ne cewa mafi falalar wannan ayyuka cikin wannan shi ne muzakarar karat, shin akwai wani nassi kan hakan? Shin muzakarar karatu ta fifita kenan kan kebantattun ayyukan ibada cikin wannan dare?

المحور الأوّل

أهل البيت  : وتحديد ليلة القدر

س 1 ـ «سئل أبوعبدالله الصادق  7 عن ليلة القدر فقال : اطلبها في تسع عشرة وإحدى وعشرين وثلاث وعشرين » سماحة السيد هل يفهم من ذلک أن ليلة القدر متعددة أم هي واحدة ؟

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittu Muhammad da iyalansa.

Ua ubangiji ka bude bakina da fadin shiriya ka kimsa mini tsoranka.

1-amsa: daga cikin mafi girman darare a wurin Allah kamar yanda kur'ani ya bamu labara shi ne daren lailatul kadri wanda yake mafi alheri da watanni dubu, Mala'iku da ruhu suna sauka cikinsa daga dukkanin lamari mai hikima cikin aminci har zuwa lokacin hudar alfijir, dare ne guda sai dai kuma sakamakon tsarkakarsa da girmamarsa Allah ya boye shi cikin darare saboda hikimarsa ta ubangijintaka da sirri, domin wanda bai kasance daga ahalin wannan dare ba kada ya samu damar riskarsa sabida wasu sirrika, kamar yanda ya boye sunansa mafi girma daga Asma'ul husna, kamar yanda ma'abota hikima ke aikatawa cikin tsadaddun hikimominsu da ilimummukansa da wallafe-wallafensu da tasnifansu, babu mai tsinkayarsu sai wanda ya kasance daga Ahalin tsadaddun sirrika da gwala-gwale da hikimomi masu isarwa.

Kamar yanda kowanne ma'aluli kadai yana samuwa ne da illarsa, sai dai cewa ita illa bayani kan samuwar hukuntau da kuma rashin ratsowar hanau da kuma tabbatuwa da samuwar dukkanin tanadi da sharudda, alal misali zafi duk da kasantuwarsa ma'lulin wuta ya samu da samuwarta, ya zama dole a samu abin da yake hukunta samuwar wutar kamar kirare, sannan kuma ya zama hanau bai ratso ba kamar misali kada kirare su kasance cikin danshi da jika, tabbatuwar sharudda kamar misalin samuwar sababin kamawar wuta, abin da yake tanadin kamawar tata kamar misalin tsinken ashana domin kunna kirare, ita illa duk da kasantuwar ta magana ce kan samuwar hukuntau da rashin ratsowar hanau sai dai kuma tare da haka daga lazimanta shi ne haduwar sharudda da tanadau suma suan daga ciki.

Daren lailatul kadri duk da kasantuwarsa dare ne guda daya sai dai cewa kuma Allah ya boye shi tsakankanin goman karshen watan Ramadan cikin kowacce shekara da kuma dare sh biyuar ga watan Sha'aban da kuma cikin sananne darare guda uku a mazhabar Ahil-baiti wato daren 19-21-23, da kuma 27 na karshen watan Ramadan, sai dai kuma tare da kafewar sahabban A'imma (as) cikin neman sanin daren lailatul kadri a kebance, sai da'irar buyansa ta ragu ta kuntatu tsakankanin darare biyun Ramadan 21-23, amma fi sanya rai sosai cikin daren 23 ya ma kusa ga kaiwa a karkare magana cikinsa da cewa shi ne kadai  daren lailatul kadri.

Sannan ya zo cikin madaukakan hadisai cewa dararen lailatul kadri uku ne bisa la’akari da cewa na farko da na biyu suna matsayin dararen shiri da tanadi don daren 23 wanda shi ne daren zartarwa da sa hannu, lallai cikin wannan dare ake rarrabe duk wani abu mai hikima, lallai cikinsa ake kaddara abin da yake cikin dukkanin kasantattu daga abubuwan da zasu faru a wannan shekara, kaddarawar ta kasance da umarnin Allah cikin Al’arhinsa, sannan da saukar da shi tare da Mala’iku daga cikinsu Ruhu wanda shi babban Mala’ika ne, ya zo cikin hadisi cewa shi yafi Jibrilu girmama, a wani fadin kuma ance Jibrilun ne Ruhu (as) sai Mala’iku su sauka da izinin ubangiji kan hujjar Allah waliyinsa mafi girma, wanda albarkacinsa ake azurta dukkanin al’umma, da samuwar sa ne kasa da sama suka zauna daram, ba da ban shi ba da kasa ta nutse da Ahalinta a abin da yake cikinta da abin da ya ratayu da taurari, sannan matafiyan duniyoyin taurari da adadinsu ya kai ga biliyan 250, cikin kowacce matafiya da hanya akwai taurari biliyan 30, kasar da ya zaba matsayar cibiyarsa shi ne kammalallen mutum wanda cikinsa Ismullahi A’azam yayi tajalli ya kasance mabayyana da madubi gareshi cikin dukkanin halittu wanda shi ne annabi mafi girma (s.a.w) farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne hasken sa da ruhin sa, ya kasance rahama ga dukkanin talikai, hakika muhammadiya ta gudana cikin baki dayan halittu, bayansa sai kammalallen mutum a kowanne zamani Imam Asri waz Zaman, ya zuwa wannan zamani namu har zuwa tashin kiyam, shi ne hujja na goma sha biyu daga A’imma Ma’asumai, Mala’iku da Ruhu suna sauka tareda al’amari mai hikima cikin dare lailatul kadri zuwa ga Sahibuz Zaman  (af) wanda shi ne kammalallen mutum mafi daukakar halittun Allah kai hatta Mala’iku makusanta.

Sannan gabanin karfafuwar al’amurra cikin lailalatul kadri, lallai yana daga hankali da jin kai kamar yanda yake sananne tsakanin mutane a ilmin injiniyanci dole ne a fara fitar da fasalin gini da tsara shi da surantashi gabanin dora harsahsin ginin, to haka lamarin yake gurin Allah madaukaki cikin tafiyar da al’amuran bayinsa, lallai shi yana fara kaddarawa     


(وكلّ شيء أنزلناه بقدر)

Kowanne abu mun saukar da shi gwargwado.

Kaddara al'amurra ya na kasancewa a daren 19, sannan ya tsara shi ya rubuta a cikin Lauhul Mahwu wal Isbat a daren 21, sannan ya san hannu ya zartar a daren 23 cikin uwar littafi cikin Lauhul Mahfuz.

Duk wanda ya raya darare biyu  na farko, zai iya samun canji da sauyi cikin abubuwan da Allah ya rigaya uyaa kaddara da yardarm Allah, idan har sadaka ta kasance tana tunkude bala'i yankakke, to fa haka lamarin yak e ga addu'a da ibada cikin dararen lailatul kadri, su dararen na shafewa da tabbatarwa, sai dai cewa cikin daren 23 lamarin na wanzuwa har zuwa hudowar alfijir, mumini da mumina zasu iya lamintar da lafiyarsu da aminciinsu daga cikin wadanda sukau riko da addu'a da munajati da ibad, daren aminci ne har zuwa hudowar alfijir, bayan nan sai ya hukunar al'amari, kai kace kamar a na rufe fayiloli da a mika su hannu Mala'iku domin su sauko don majibancin al'amari ya duba su, a jumlace ya tsinkayi abin da ya gudana cikin halittua tsawon wannan shekara, wannan yana daga cikin sunnar Allah da hikimarsa cikin halittunsa.

Daren lailaltu kadri dai guda daya ne sai dai cewa yaduwarsu cikin darare uku ya kasance sakamakon boye shi, da kuma stara kaddarori da hikima da gudanarwa ubangiji, lallai na da sha'ani cikin halittunsa, shi kowacce rana yana cikin sha'ani. 

 

2-Amsa: gabar da makarantu biyu suka yi tarayya da juna ma'ana makarantar Kulafa'u da makarantar Ahlil-baiti shi ne cewa cikin kowacce shekara akwai daren lailatul kadri, lallai yana da girma wurin Allah matsarkaki, lallai shi ya fi alheri daga watanni dubu, ya kamata a raya shi da ibada da addu'a, kamar yanda gabar tarayya ta buya cikin goman karshe Ramadan, kadai sabani yana makarantar Ahlil-baiti cikin daren 21da abin da ya biyo bayansa, da mai da hankali na musammam kan daren 23, sai dai kuma cewa wajen waninsu ya kasance ne tsakanin daren 27 kamar yanda hakan ya shahara wurin jamhur kamar kumar yanda yake a wannan zamanin namu, ko kuma dai daren 15 daga watan sha'aban.

Ya zo cikin hadaisin Ahlil-baiti: tsakiyar sha'aban kadai dai daren lailatul kadri na A'imma tsarkaka, daren 23 ga watan Ramadan kuma daren lailatul kadrin Allah ne da manzonsa (s.a.w).

 

 3-babu shakka lailatul kadri na maimatuwa a kowacce shekara, bari dai ya kasance tun sanda Allah ya halicci sammai da kasa, tun sanda adadin watanni ya kasance goma sha biyu, tun farawar watan Ramadan, kuma cikin kowanne watan Ramadan akwai lailatul kadri kuma Mala'iku suna sauka cikinsa da ruhu daga dukkanin al'amari zuwa ga waliyin Allah mafi girma daga Adam har zuwa cikamakin Annabawa da Manzann, ya kasance imamin zamaninsa, lallai A'imma.

Idan ya zamanto akwai imamai biyu a zamanin kamar misalin Hassan da Husaini (as) to dayan su shi ne take ke da wannan dayan kuma nan gaba, zai juyo gareshi a lokacin da babu dayan na farko, sabanin annabta su a iya samuwar annabtanka annabawa da yawa a mahallai daban-daban cikin zamani daya sabanin imamai da dole sdai babu daya na biyu kan zama imami.

Daren lailatul kadri ya kasancetun lokacin saukowar Adamu (as) har zuwa tashin kiyama, wannan bayani ya zo cikin ingantattun riwayoyi daga makarantar Ahlil-baiti (as) daga abin da kae shaida da bada dalili kan hakan.

4- yayin da falalar kwanakin da dararen ya kasance daga al'amuran gaib, babu wanda ke sanin iya sanin gaibu kai tsaye sai Allah madaukaki, idan hikimarsa ta hukunta da ya tsinkayar da wani mutum kan daga manzannin sa gaibu to hakika zai tsinkayar da shi, idan kuma ya kasance maslahar al'umma ta hukunta cewa ya tsinkayar da shi, sai ya umarce shi da labaruka, wannan duka ya kasance da ludufin Allah, sannan shi ludufi kamar yand aya zo cikin bayanin sa: shi ne dukkanin abin da zai kusanta bawa zuwa ga da`ar ubangiji ya kuma nesanta shi daga sabon sa, da wannan kaidin na karshe ne jabaru (tilashi) ke zamantowa ya fita daga ciki, domin babu jabaru babu kuma tafwizi (babu tilashi kuma babu sallamawa) sai dai cewa al'amari ne tsakanin al'amura guda biyu, kamar yanda yake a makarantar Ahlil-baiti.

A wannan lokaci zamu san falalar dararen da kwanaki da abin da yayi kama da haka ta hanyar hadisai da suka zo daga manzannin Allah da annabawan sa da wasiyyan su ma'asumai (as) su ma'abotan gida sune sune suka fi kowa sanin gida a dabi'ance da shari'anc, lallai sun bada labarin girman daren lailatul kadri da falalarsa da karamomin da suke cikin sa, suka ce yinin sa daidai yake da daren cikin falala da matsayi, ya kamata a kiyaye hakkokinsu su biyun ma'ana daren da yinin kamar yanda babban malamin hadisi Shaik Abbas Qummi yayi ishara cikin littafin Mafatihul jinan, bisa abin da ya zo daga iwayoyi da suke shiryarwa zuwa ga haka.

5-a nan akwai bahasosi masu yawa daga zawiyoyi daban-daban, wani lokacin daga zawiyar ilimin Hai'a da Falaki, wani kuma daga zawiyar Irfani, na uku daga zawiyar hadisai madaukaka da ayoyi masu daraja, da abin da ya zo daga tafsiri da tawil, da mikdarin abin da tsari da shirin zai iya dauka anyi ishara zuwa ga ba'arin wasu bahasosi a takaice da nusantarwa da fadakarw, sarai ya kasance gabar farawa ga wanda yake son zurfafawa cikin wannan fage. Abin da zan ambata yana kan hasken hankali da ilimin dabi'a da nakali ma'ama ayoyin kur'ani da hadisai madaukaka cikin addinin muslunci mai karkata zuwa ga shiriya na asali kuma cikin makarantar Ahlil-baiti.

Bisa haske da madogarar hankali da ilimin rayayyun dabi'a (physics) lallai ana hukunta cewa dole ne kowanne abu ya fara daga gaba kasantuwar ta saukakarta da dayantar ta, sannan tana kasancewa cibiyar dukkanin abubuw, lallai yand al'amarin yake bisa dogaro da ka'idar gudu daga cibiya ba da ban dangantaka tsakanin cibiya da waninta ba da ya lazimta gujewa abubuwa lamarin da ka iya jawo halaka da rushew, amma cibiya to ita ta tsayu da kankin kanta, lallai cikin samuwa tsantsa wato Allah rayayye tsayayye wanda yake tsayuwa kan komai da komai, sannan cikin koma bayansa, lallai daya ne, yana misaltuwa yana bayyana cikin sunayen sa da siffofin sa sai ya kasance mabayanna da madubi ga siffofin sa, wannan daya rak kenan bisa madogarar dalilin hankali da hujja nakali, shi kammalallen mutum wanda Allah ya halicce shi domin ya halifance shi cikin halittunsa, cikin cibiyar halittu wato doran kasa  

 (إِنِّي جَاعِلٌ فِي الأَرْضِ خَلِيفَةً)[3] .

Lallai ni mai sanya halifa ne a doran kasa.

Sannan mutum ya kasance mabayyanar sunan Allah mafi girma sunan girmama (Allahu) wand aya tattaro sunayen Allah da siffofin ubagijintaka, sannan Allah ya halicci abubuwa domin shi kamar yanda ya halicci mutum domin sa matsarkaki madaukaki ya zo cikin hadisi kudusi

«خلقت الأشياء من أجلک وخلقتک من أجلي » «عبدي أطعني حتّى أجعلک مَثلي ، أقول للشيء كن فيكون ، وتقول للشيء كن فيكون »

 Na halicci abubuwa saboda kai na kuma halicce ka saboda kaina, bawana kai mini biyayya har sai na sanya irina, ina cewa abu kasance take sai ya kasance, kai zaka cewa abu kasance take ya kasance.

Kammalallen mutum  a wannan lokaci ya kasance mihwari halittu kuma cibiyar su, dukkanin faila da kwarara daga Allah matsarkaki madaukaki kadai kaddara shi da zartar da shin a tabbatuwa ta hannun sa, shi ne tsanin failoli daga Allah zuwa bayinsa, kamar yanda hakan ya tabbata a mahallinsa, sakamakon kasantuwa shekara ga Ahlin doran kasa sannan ita shekara tana da farko, al'amura na gudana kan lissafin zamani, daga cikin sa: karni da gomomin shekara da shekara da watanni da kwana da awa  da minti da sakan da kiftawar ido, to haka al'amarin yake ga halittun sammai shekarar su cikin gudanar al'amura cikin isar da sakon su da sauke nauyin su wand aya ta'alalaka da tsara halittu da kaddarorin sa, sannan farkon shekarar su (lailatul kadri) kamar yanda ya zo daga hadisi mai daraja :

Sannan yayin da Allah ya kaddara al'amura ya hukunta su ya karfafa su cikin uwar littafi, da abin da ya rubuta cikin lauhul mahawu wal isbatu, lallai ya zama dole a hankalce da nakalce ya tsinkayar da waliyin sa mafi girma mabayyanar sunan sa mafi girm, shi ne kammalallen mutum wanda ake kira da Imamul Zaman cikin kowanne zamani da bigire, Mala'iku wakiltattu da saukar da kaddarori kan wannan waliyi wanda ya tabbatu a doran kasa, saboda ita wadda Allah ya zaba tsakankanin biliyoyin duniyoyin taurari cikin magudanar tabbatanatu, kamar yand aya zabi tabbanar sa (galaxy) tsakanin biliyoyin tabbana (galaxy). Su Mala'iku kaddarori halittu tare da Ruhu mafi girma suna sauka wurin waliyin Allah mafi girma, shi yana tare da a wannan yinin namu cikin daren lailatul kadri mai albarka shi ne Imami na goma sha biyu Hujjatu Mahadi Muntazar daga iyalan Muhammad Allah ya gaggauta bayyanar sa mai daraja, ya kuma lullube mu da tausayin sa da jin kansa da addu'ar sa da ludufan sa kebantattu lokaci bayan lokaci har zuwa haduwar mu da Allah matsarkaki yana mai yarda da mu, kuma mu kasance cikin darajar masoyan mu Imaman mu tsarkaka a mutsugunin gaskiya wurin sarki mai ikon yi.

Sannan wannan saukar Mala'iku da wannan girma haka da mas'uliya mafi girma da saukar ruhu da dukkanin al'amari mai hikima wurin waliyin Allah mafi girma (as) babu shakka kan misalin wannan sauka mai girma akwai albarkoki masu tarin yawa da girmama wadanda suka shallake tunanin mutum, kadai sun kebantu da daren lailatul kadri guda daya wanda shi ne daren da yake mafi alheriu daga watanni dubu.

A wannan lokaci tambaya na bijirar da kanta, tare da sassabawar sasannin da kasashe, bari tare da sabawar duniyar kasa cikin tafiyar rana  inda zaka samu daidai lokacin da a wannan yankin dae ya shiga a wancan kuma ran ace, da mutum zai riski lailatul kadari cikin rabin kwana daya sannan yayi tafiya cikin jirgin sama zuwa daya rabin ya kuma riski daren sa, shin zai zama kenan ya riski darare biyun na lailatul kadri, ko kuma dai dare guda daya da zai yi ayyukan daren lailatul kadri cikin garin na biyu d aya samu kansa, ko kuma mu ce dare na biyu ?


Tura tambaya