lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

BEGEN SHUGABAN SHAHIDAI YA ZAUTAR DA NI

BEGEN SHUGABAN SHAHIDAI YA ZAUTAR DA NI

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin  yabo da godiya sun tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa zababbu tsarkaka.

Bayan haka:

Allah girmansa ya girmama, haka na kasantuwa cikin tattakin  ma’arifa ta hakika ya zuwa haramin gaibu boyayye wanda haskensa ya bayyana cikin kawazazzabon `dafufi cikin ranar Ashura ranar shahada, wajen soyayyar Allah wacce ta yi tajalli cikin duniyoyin mala'ikantaka da malakutiyya  cikin Kausul nuzuli da Su’ud, hakika maganganu da ra’ayoyin Arifai da masu wusuli sun sassaba cikin tsanukan sadarwa da taguwa wadanda da su mutum zai nade dukkanin masaukan Ahlin ma’arifa da sairi da suluki, cikinsu akwai wanda ya tafi kan hikima, cikinsu akwai wanda ya tafi kan ibada kamar salla azumi, ance: sune azkaru da tsoran Allah wasu kuma da tunani kan girman mahalicci da halitta, da tafiya daga halitta ya zuwa ubangiji gaskiya da gaskiya, daga gaskiya kan halitta da gaskiya, ance har ta kai ga kwakwale suna gigita cikin mamaki da rudewa, zukatan da suke cikin kiraje sun kekkece daga tsinkaya da afkuwa kan hanya madaidaiciya da siradi mikakke da tafarki na hakika da kaiwa ya zuwa hakika tabbatattun abubuwa  da gaibun gaibobi.

Sai dai cewa hasken zuciyar mumini wanda shi daga shimfidadden hasken Allah da yake cikinsa yake yana shiryar da shi zuwa ga cewa lallai dukkanin hanyoyi zuwa ga Allah matsarkaki da sairin mausakan masu tafiya zuwa ga Allah mai girma da daukaka da dukkanin abin da ake ambato daga guzuri da taguwa daga abin da zai sadar da bawa zuwa ga ganawa da maulansa masoyinsa  lallai suna daga cikin hanyoyi zuwa ga Allah lallai su hanyoyin zuwa ga Allah sun haura adadin numfashin halittu sai dai cewa mafi kusancin hanyoyi zuwa ga Allah mafi alherin guzuri  da tsanin falalar farko da karshe, haske mafi cika hanya mafi daidaita ga nade masaukai, kadai yana bayyanuwa cikin soyayya ga shugaban shahidai Husaini da Imam Ali ibn Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare su, lallai soyayyarsa da kaunarsa  kadai dai sun kasance madarar soyayyar Allah da soyayyar manzonsa   

 (حسين منّي وأنا من الحسين)

Husaini daga gare ni yake ni ma daga Husaini na ke.

Shi ne mafificiyar ibada, mafificin wurudi da zikiri da aiki don kaiwa ga samuwa mai hukuntawa da cire hijabai masu katangewa zuwa ga kaiwa ga Allah matsarkaki madaukaki, shi taimakon Allah ne ga wanda ya bi hanyar hakikanin gaskiya cikin shari’a da darika, hujja ne ta hankali, hasken zuciya ne, lallai da soyayyar Husaini hannun gaibun Allah da taimakonsa ke mikuwa da taimakon ubangiji madaukaki, da ludufinsa da jalabinsa boyayye hanyoyi ke haskaka zuwa ga ubagijin talikai.

duk mai son alherin duniya da na lahira da farin cikin duniya da na lahira da sairi da suluki da wusuli ya zuwa ga Allah matsarkaki tsakanin zira’i ko mafi kusa da haka cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai iko, sai ya haskaku da fitilar shiriya Husaini, sai yayi maza ya hau jirgin tsira na Husaini, lallai an rubuta kan al’arshin Allah da koren launi wanda shi ne launin ma’arifa    

 (الحسين مصباح هدىً وسفينة النجاة)،

Husaini fitilar shiriya ne jirgin tsira ne.

Saboda haka ya rataya da direban jirgi a ruhance da jikance wanda shi ne Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare shi, duk wanda yake so ya kasance yantacce cikin farin ciki duniya da lahira to ya yi riko da baban `yantattu abin koyi ga rabautattu, shugaban mafiya alheri.

Ya zama dole da farko gabanin komai ya fara dandanar kaunar Husaini, lallai kauna ita ce zurfafawa soyayya banda wuce gona cikin soyayya irin wacce ta sabawa shari'a, haka kuma  da tsanantawa wanda yake shi karkatar zuciya ne zuwa ga masoya daddadan abu mai dadi, ma’ana mai dadi mafi dadada daga hakikar Husaini wacce tayi tajalli ranar Ashura cikin ziyarar Ashura, duk sanda dadi yafi karfafa da cika cikin dadada sai soyayya da karkata su zama mafi girmama da girma har ya kai ga haddin wuce gona da iri, sai a kira shi da kauna ta hakika idan abin da ya ratayu da shi ya kasance daga Allah girmansa ya girmama, da abin da sunan Allah ya kasance kansa.

 (اللّهم ارزقني حبّك وحبّ من يحبّك وحبّ كل عمل يوصلني إلى قربك)([1]).

Ya Allah ka azurta ni soyayyarka da soyayyar wanda yake sonka da son dukkanin wani aiki da zai sadar da ni zuwa kusantarka.

 Waken kauna daga bakin suhagaban shahidai cikin kaunar Allah, ashe ba shi ne wanda ya fadi abin da aka danganta shi zuwa gare shi ranar ashura ba:

 

 


na bar halittu baki daya saboda soyayyarka na maraitar da iyalina don son ganinka da za su daddatsani gunduwa gunduwa da har abada zuciyata ba zata taba karkata zuwa ga waninka ba.


Kauna da soyayya na wuce gona da iri idan abin da ya ratayu da shi wanin Allah ne to zai zama abin zargi. Kamar yadda Imam Sadik amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya fada cikin soyayya da bata hakika ba

 (قلوب خَلَت عن حبّ الله فأذاقها الله حبّ غيره)

Zuciyoyi sun wofinta ga barin son Allah sai Allah ya dandana musu son waninsa.

Amma cikin soyayyar hakika da ratyuwar zuciya da Allah to babu wani batun wuce gona da iri, saboda abin da soyayyar ta ratayu da shi shi ne samuwa mudlaka cikin zatinsa da siffarsa da ayyukansa, shi ne kamala da kyawu tsantsa, babu karshe ga soyayyarsa hatta ma taken wuce gona da iri ya bijiro, duk wanda ya yi riko da igiyar shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata gare shi cikin tafiyarsa da sulukinsa, ya dandani soyayya da ma’arifa boyayya da ma’anoninta da misdakanta cikin zuciyarsa da samuwarsa , ya jikkanta ta cikin hakikarsa ta waje  cikin rayuwarsa to hakika ya shiga mafi kusancin hanyoyi, mafi falalar guzuri zuwa ga Allah matsarkaki maduakaki. Saboda Imam Husaini cikin zabinsa ga shahada da musiba mafi girma cikin ranar ashura cikin kasar karbala, ya zabi hanya wacce Allah ya zanata ya ayyana masa cikin shafin samuwa cikin duniyar mulk da malakutiyya da gaibu da bayyane, karkashin soyayyarsa da fana’insa cikin Allah da wanzuwa tare da shi, shi ya cika cikin soyayya, kamar yadda ya zo cikin ziyara jami’a kabira

 (والتّاميّن في محبّة اله)

Da cikakku cikin soyayya Allah.

Domin lallai ita soyayya  tana daga mafhumin kulli mushakkak ma’abocin martabobi  duliya da ardiyya, daga abin da bai kidaituwa basu iyakantuwa, cikin cancanta da tsanani da rauni da gabata da jinkirta, sai dai lallai shugaban shahidai Imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya jikkanta ma’ana ta hakika ga soyayyar Allah cikin waki’ar daffi mai radadi ranar ashura goma ga watan muharram mai alfarma shekara 61 bayan hijra annabi, ta yadda sirrikan hakika da hakikani abubuwa da hakikanin asraru suka bayyanu ranar ashura a filin karbala, wannan yana daga cikin ma’anonin madaukakin  hadisin annabi:

 (إنّ لقتل الحسين في قلوب المؤمنين حرارة لن تُبرد أبداً) وكذلك (إنّ للحسين في بواطن المؤمنين معرفة مكتومة) ([2]).

(Lallai cikin kasha Husaini akwai wani zafafa cikin zukatan mumini da ba zai taba sanyaya ba har abada) haka ma (lallai Husaini yana da wata boyayyar ma’arifa cikin badinan muminai)

Farin ciki ga wana ya kasance ya sanni ya kaunace ni duk wana ya kaunace ni nima zan kaunace shi , sannan shi mai kauna yana dayanta cikin abin da yake kauna cikin ganin kyawunsa cikin idon zuciyarsa, sai ya ga masoyi abin kauna a halarce wajensa cikin zuciyarsa da badininsa, zuciya tafi tsananta riska daga basira da ido da gabban zahiri, daga nan ne kuma ma’anoni ke kewayawa wacce zuciya ta riske su kamar asraran ashura da salladuwar haske kan ziyara da zuciya yafi girma daga kyawun dukkanin surorin zahiri wadanda ake riska, yafi dadada daga dukkanin dadin gaibu da bayyana, wannan ma’arifa  boyayya wacce ta bayyanu cikin soyayya da kaunar Husaini, da son Husaini zaka kai ga son Allah ka ganshi da zuciyarka da tabbatattun imani ya gana da kai cikin sirrinka  da hankalinka, ka sani ka fahimta da cewa mafi girma da daukaka dadi da mukamai., tukewar masaukai da sairi da suluki  cikin sanin Allah shi ne soyayyarsa da son haduwa da shi da kallon tsarkin fuskarsa mai karamci. Duk wanda ya ga girmansa da girmamarsa da kyawunsa da haskensa da tajallinsa cikin littafinsa da halittarsa, da girman jabarutinsa da malakutinsa cikin wadanda suka nufi zuwa gare shi da arifai, zai risketa cikin zurfin samuwarsa da zuciyarsa da hankalinsa, zai gansu da hasken idanun zuciya da halitta, a wannan lokaci zai watsi dadade-dadade da suke hana shi isuwa ga Allah

 (واستتغفرك من كل لذة ليس فيه إسمك)([3]).

Ina neman gafararka daga dukkanin dadi da babu sunanka cikinsa.

Bai kusa ya yi tasiri kan wannan dadi ba wani dadin daban, sai dai cewa idan ya haramtu da ita da soyayyar duhu ko ta haske kamar hijabi mafi girma shi ne ilimin da bai cudanya da aiki, ya kasance daga haramtattu  daga dadin son Allah da son wanda suke sonsa muhammadu da iyalansa amincin Allah ya kara tabbata gare su da soyayyar shugaban shahidai amincin Allah ya kara tabbata gare shi.

Soyayyar Allah ita ce magaryar tukewa da karkarewa mafi girma da arifai da makusanta, itace tsololuwa daukaka da salikai da masu tafiya zuwa ga Allah madaukaki, abin da ake ambata daga mukamai bayan soyayyar Allah kadai dai shi riba ce daga ribarsa kamar misalin shauki da debe haso, abin da zuciyarsa ke Ambato kadai dai shimfida ce daga shimfidu kamar zuhudu da hakuri, da soyayya samuwa ta bayyanu aka bayyanar da samamme, da soyayya mai ibada ya banbantu daga abin bauta, lallai shi ne tushen kowanne abu da rukunansa da hakikarsa kamar yadda ya zo cikin hadisi kudusi daga Allah matsarkaki wanda ya shahara cikn fadinsa:     

 (كنت كنزاً مخفيّاً فأحببتُ أن أُعرف فخلقت الخلق لكي أُعرف).

Na kasance taska boyayya sai na kaunaci da a sanni sai na halicci halitta domin a sanni.

Zukata da rayuka da tsarin halittarsu  lafiyayya, soyayyar kyawu da kamala mudlaka na jijiyantuwa cikinsu, dukkanin zuciya an halicce ta kan son mani’imcinta, mafi alherin abin da zai sadar damu zuwa ga soyayyar Allah mai ni’imtawa  shi ne son Husaini son Husaini shi ne ya haukata ni…zahirinsa hauka badininsa tsantsar hankali…dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin talikai.

 

 


Tura tambaya