lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU KARANTA A'UZUBILLLAHI KAFIN FARA KARATUN RAKA'AR FARKO

Wuri: birnin Qum mai tsarki-cibiyar Muntada Jabalul Amil islami- tare da Samahatus Assayid Adil-Alawi (H)

Lokaci: karfe 8 na safiya zuwa 9 na safiya.

Darasin fikhu (83) 21 ga watan Jimada Thani shekara ta 1441 Q.

Bahasi cikin mustahabbat din kira'a (karatun sallah):

sun dunkule cikin al'amura kamar haka: na farko: karanta A'uzubillah zuwa karshe kafin fara karatun raka'ar farko, shine mutum ya karanta :

 (أعوذ بالله من الشيطان الرجيم)

Ina neman tsarin Allah daga sharrin Shaidan jefaffe.

Ko kuma ya karanta:

 (أعوذ  بالله السميع العليم من الشيطان الرجيم)

Ina neman tsarin Allah mai ji masani daga sharrin Shaidan jefaffe.

Sannan ya kamata karantawarsa ta kasance a boye.

Ina cewa:  kamar yanda aka sani ya kasance cikin al'adar da Fakihai suka kasance kanta cikin Risalolinsu madaukaka cikin kowanne babi da take da maudu'i bayan amabaton hukunce-hukunce na wajibai shine suna riskar da su hukunce-hukuncen mustahabbi sai kuma daga baya su rufe da hukunce-hukunce makaruhai.

Daga cikin hikimar hukunce-hukuncen mustahabbai shine kasancewarsu masu kammala tawaye-tawayen farilloli da wajibai sakamakon abinda yake tare da su daga maslahohi  a jumlace dai shine basu kasance farilla kamar yanda wajibai suka kasance, sabida mu na neman haske da kyawu dfa kamala cikin wajibai, kamar yanda cikin makaruhai akwai barna da mafsada daga abinda yake tasiri cikin buyar haske da haskakar wajibai, kamar yanda yake cikin Alwala da Hadasul asgar  ko kuma kamar yanda cikin wankan janaba da Hadasul Akbar, hakika hadasi yana daga abinda yake jawo duhu da kazantuwa cikin Rai da ruhi, kamar yanda alwala ta kasance haske haka sabunta alwala kan alwala haske ne kan haske sai wannan haske ya zama ya kawar da datti da dukkanin duhu na badini (tabbas Allah yana son masu tsarkaka) lallai kamar yanda ya zo cikin hadisin Annabi (s.a.w) daga Sarki Allah madaukaki cikin wani hadisi Kudusi

من أحدث ولم يتوضأ فقد جفاني، ومن توضأ ولم يصل ركعتين فقد جفاني، ومن توضأ وصلى ولم يسألني ويدعوني فقد جفاني، ومن دعاني ولم أستجب له فقد جفوته، وما أنا بربّ جاف).

Duk wanda ya samu kansa cikin hadasi sannan yaki yin alwala hakika yayi mini jafa'I, duk wanda yayi alwala yayi sallah ya tashi bai rokeni komai ba hakika yayi mini jafa'I, duk wanda ya roke naki amsa masa tabbas nayi masa jafa'i, ni ban kasance ubangiji mai jafa'I ba.

Bayanin bayani kan hukunce-hukunce kira'a daga wajibai cikin mustahabban kira'a hakika Muhakkikul Hilli yayi ishara zuwa abubuwa guda goma:

Na farko: karanta neman tsari da Allah daga sharrin Shaidan gabanin fara kira'a, ita isti'aza wato neman tsari Kalmar ta kasance daga babin istif'al da suka samu kario daga haruffan ziyada guda uku (I,S,T) suna da ma'ana dalab nema, ita isti'aza ma'anarta neman tsari da mafaka ya zuwa karfafaffen shinge domin samun kariya daga sharri da cutuwa kamar misalin shiga cikin mafaka yayinda ake harbo muku makamai masu linzami.

Hakika Allah ta'ala cikin littafinsa mai girma hakama Annabi mafi girma da iyalansa tsarkaka cikin hadisansu masu daraja duka sun umarce mu da neman tsari daga saharrin Shaidan jefaffe , haka da neman tsari daga sharrunkan kawukanmu, lallai rai mai yawan umarni ce da mummuna kuma tana daga mafi tsananin kiyayyar makiya daga dalilan da yasa ake neman tsari daga sharrukanta da cutarwarta, na uku da kuma neman tsari daga sharrin Masharranta daga mutane da Aljanu, na hudu da neman tsari daga sharrin (makalaka)

Sannan ba zai zama mun wadatu da neman tsarin na fatar baki na lafazi ba kadai matukar dai bai cudanya da aiki ba, ta iya yiwuwa ya zama mara amfani idan ma bai kasance mai cutarwa ba tareda gafala.

Mustahabbi ne gabanin fara kira'ar fatiha cikin sallah a raka'ar farko, wannan shine ra'ayi da Mashhur suka tafi a kai kamar yanda Muhakkikul Hilli ya kasance kansa Allah ya tsarkake ruhinsa, bari dai an  nakalto daga Majma'ul Bayan kore sabani cikin wannan mas'ala, an nakalto daga Alkilaf  daga Kashaful Lisam: Ijma'I kan wannan ra'ayi, ya zo cikin Azzikra: ittifaki kansa, daga abinda zahirinsa yake nuni cewa wannan ra'ayi yana daga Ijma'ul Madraki babu banbanci Muhassal ne ko kuma Mankuli, kamar dai yanda kake gani.

Jigo cikin mukamin istidalal: shine riko da wani bangare daga ingantattun riwayoyi da ake riklo da su wanda suke shiryar kan mustahabbancin, daga cikin riwayoyin akwai :

صحيحة الحلبي محمد بن يعقوب عن علي بن إبراهيم عن أبيه عن ابن أبي عمير عن حمّاد عن الحلبي:

عن أبي عبد الله عليه السلام: قال عليه السلام: بعد ذكر دعاء التوجه بعد تكبيرة الاحرام: ثم تعوّذ بالله من الشيطان الرجيم ثمّ إقرء فاتحة الكتاب([1]). حمد بن الحسن بإسناده عن محمد بن يعقوب مثله.

Sahihatu Alhalabi Muhammad Ibn Yakubu daga Aliyu Ibn Ibrahim daga babansa daa Ibn AbI Umairu daga Hammad daga Halabi: daga Abu Abdullah (A.S) ya ce: bayan ambaton addu'a da fuskantar ubangiji bayan kabbarar harama: sai ka nemi tsarin Allah daga Shaidan jefaffe sai ka karanta Fatiha. Hammad Ibn Hassan ya rawaito misalin wannan hadisi da isnadinsa daga Muhammad Ibn Yakubu.

Dora umarnin da ya zo cikin riwayar cikin fadinsa (A.S) : (sannan ka nemi tsarin Allah) kan mustahabbanci koma bayan wajabci akwai sabani cikin hakan daga Abu Ali Shaik Dusi (K.S) sakamakon shi ya zabi dora jumlar kan wajabci kamar yanda ya hakaito shi daga Azzikra: J 3 sh 331, wannan bakuwar magana ce ba a riko da ita, bari dai ijma'I na raddin kansa kan sabani da aka hakaito gabaninsa da kuma bayansa, bari dai magana ta na gangara kansa.

Da farko: babu abinda yake hukunta zabar wajabci koma bayan mustahabbanci, hakika umarni da ya zo cikin jumlar bai bayyanuwa cikin wajabci a kankin kansa, domin ya cudanya da jumla daga mustahabbai kamar misalin daga hannu da shimfida shi da kawo kabbarar harama, da addu'o'i ciki da makamancin haka, bisa la'akari dayantuwar siyaki da nufar mustahabbi daga wasu wuraren daban, sai ya zama shima wannan  an dora  shi kan mustahabbanci. Bai nufi wajabci ba, ka lura sosai.

Na biyu: ko da ma ace ba ambaci wadannan karinoni na cikin gida  to lallai karorni da shaidu na waje suna shaida kan rashin nufin wajabci, sabida mas'alar mas'ala ce da ake yawan jarrabtuwa da ita, na uku: mas'ala ce take yawan kewaya kan Mukallafi a kowacce rana, na hudu: da ya kasance wajibi da ya bayyana karara sakamakon abinda ya afku cikinta daga sabani, na biyar: abinda Mashhur suka tafi akai daga rashin wajabci bari dai sun zabi mustahabbanci kamar yanda bayani ya gabata, na shida: abinda ya bayyana daga ba'arin wasu nassoshi duk da kasancewarsu masu raunin isnadi sai dai cewa aiki da rikon da Malamai suka yi da su yana daga abinda yake gyara raunanar isnadin, daga cikinsu akwai:

خبر الفرات ابن أحنن: محمد بن يعقوب عن محمد بن يحيى عن علي بن الحسن بن علي عن عباد (ابن يعقوب عن عمرو بن مصعب عن فرات بن أضف عن أبي جعفر عليه السلام: فإذا قرأت بسم الله الرحمن الرحيم فلا تبالي أن لا تستعيذ([2]).

Kabaru Furatu Ibn Ahnan: Muhammad Ibn Yakubu daga Muhammad Ibn Yahaya daga Aliyu Ibn Hassan Ibn Aliyu daga Ubbadu Ibn Yakubu daga Amru Ibn Mus'ab daga Furatu Ibn Adafu daga Abu Jafar amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: idan ka karanta bismillah kada ka damu idan bakai karanta isti'aza ba.

ومرسلة الفقيه: كان رسول  الله صلى الله عليه وآله أتمّ الناس صلاةً وأوجزهم، كان إذا دخل في صلاته قال: الله أكبر بسم الله الرحمن الرحيم([3]).

Mursalatu Fakihu: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mafi cika sallah daga dukkanin mutane ya kuma fisu takaita ta, idan ya shiga sallarsa yana cewa: Allahu Akbar bismillahi rahamanir Rahim.

Na bakwai bayan ambaton abinda Shaik Abu Ali Dusi (K.S) cikin Azzikra: ya ce: lallai wannan bakuwar magana ce sabida wannan umarni umarni ne na mustahabbi da ittifakin malamai,

`dansa cikin Alkilaf ya nakalto Ijma'I daga garemu.

Amma magana kan abinda ake neman tsari da shi cikin raka'ar farko, shine abinda adadin malamai suka yi bayaninsa karara kamar yanda ya kasance zahirin da wasu adadin suka bayyana daga manyan malamai, ana wani kaolin ana tsamo ijma'I daga kalmominsu, sabida dalili ya kebantu da shi, kamar yanda Siratul mutasharri'a ta kasance kansa.

Amma dangane da sigogin isti'aza: daga cikinsu akwai abinda Muhakkikul Hilli ya kawo,siga  ta farko dai: shine kace: (A'uzubillhi minal Shaidanir Rajim) kamar yanda Sira ta kasance kai, an samo daga Mashhur bari dai hatta daga Shahidul Sani: wannan siga anyi ittifaki kanta, kamar yanda ta zo cikin hadisin Annabi (s.a.w)4 daga Azzikra.

ta biyu: ya ce: (A'uzubillahi Assami'ul Alim Minash Shaidanir Rajim) kamar yand aya zo cikin Sahihatu Mu'awiyatu Ibn Ammar, haka cikin hadisul Ridawi da Kabaru Da'a'im.5

Ta uku: ya ce: (A'uzubillahi Assami'ul Alim minash Shaidanir Rajim wa'a'uzu billahi an yahadurun)6.

Ta hudu: ya zo cikin muwassakatu Samma'atu: (Asta'izu billahi minash Shaidanir Rajim annalaha huwas Sami'ul Alimi).

Amma boye karatunta wannan shine abinda yawanci malamai suka zaba, daga Shaik Dusi cikin Alkilaf anyi ijma'I kansa, daga Attazkiratu da wasu littafan: kan haka A'imma (A.S) sukai aiki da shi, kamar yanda Siratul mutashshari'atu ta kasance kai, sai dai cewaya zo cikin hadisin Hannanu Ibn Sudairu

 حنان بن سدير : (صليت خلف أبي عبد الله عليه السلام المغرب، فتعوذ بإجهار([7]).

Nayi sallar magariba a bayan Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi, sai ya bayyana karatun neman tsari.

Sannan ya bayyana bismillahi sai dai cewa malamai sun kauracewa aiki da wannan riwaya, sabida haka ta fadi daga la'akari da ita.

([1]).الوسائل: باب 57 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأوّل وفي الباب: 7 روايات

([2]).الوسائل: باب 58 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأول.

([3]).الوسائل: باب 58 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

([4]).الوسائل: باب 57 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث 6.

([5]).الوسائل: باب 57 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث 7.

([6]).الوسائل: باب 57 من أبواب القراءة الحديث 5.

([7]).الوسائل: باب 57 من أبواب  القراءة في الصلاة الحديث: 4.

 


Tura tambaya