lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Gwagwarmaya tsakanin hankali da wahami

.

Ya Allah ka fitar da ni daga duhhan wahami, ka karrama ni da hasken fahimta, ya Allah ka bude mana kofofin rahamar ka, ka rarraba mana taskokin ilumummukanka da rahamarka ya mafi jinkan masu jin kai.

Ka sani shi dauki ba dadi tsakanin hankali da wahami daga karshe tana iya tukewa da karkarewa ga galabar wahami da samun ikonsa kan hankali, wannan yana daga cikin mafi hatsari da halaka, lallai yanda lamarin yake mutum zai zama yana daukar abin da ba ilimi ba a matsayin ilimi, wanda hakan na biye da kufaifayen ilimi, ya tsammaci cewa shi yana kyautata aiki.

Ta yiwu wanda yake da ba’arin wasu daga ilimummuka daga mushahada ya jarrabtu da wahami da hiyali da kurafat da karairayi, sababin hakan yana komawa zuwa ga kasantuwar mutum bai yi amfani da karfin hankalinsa ba da mustawar da ya dace ya yi amfani da shi, har wahami ya wayi gari yana mai galaba kan hankalinsa, bai buya ba mabiya wahami duk da kasantuwarsu cikin surar mutane a ganagar jikinsu sai suna da tanadin riskar ayarin cikakkun mutane da zukata masu furuci masu riskar gundarin abubuwa, tare da haka su basu tsallake madaukakan tsanuka ba cikin martabobinrai da nafsun dan Adam, da kuma kaiwa ga tsololuwar kamala tare da wahamai.

Bayanin haka: shi ne cewa shi mutum cikin zirinsa na zahiri da tsarin hallittarsa a zahirinsa da badini yana dauke da gundarin girma, yana sassabawa a siffance da cikin zatinsa daga sauran halittu ma’abota jikkuna, sakamakon wannan tsarkakken jauhari da ya kasance cikinsa ya fifitu daga halittu marasa bakin magana da furuci da tsirrai da daskararrun abubuwa. Dama sauran halittu ma’abota jiki ya fifitu da karamci da falala da daraja, hakika Allah ya karrama dan Adam da karamomi, daga cikin mafi girmansu da kyawunsu shi ne hankali, shi hankali shi fitilace mai haskaka cikin maslakai da hanyoyin rayuwar mutum.

Wannan itace marainiyar zinariya kwaya daya rak ma’ana nafsu din mutum da ta sauko daga daukaka daga madaukaka, hakika ta fifita daga waninta cikin kausin nuzuli da su’udi da abubuwa guda biyu:

1- hankalta da riska mafahim da ma’anoni mujarradai da kulliyat, da riskar hakikanin abubauwa kamar yanda suke a hakikaninsu.

2-Kubutuwa da fitar da iradar hankali daga datti da shubuha cikin janyo abubuwan da suka dace da kuma abubuwan da suke dadadawa nafsu, ana kiran wadannan da sha’awa, kamar yanda cikinsu munazorori suka afku. Su kuma ana kiransu da fushi, dan Adam cikin zubinsa Allah ya bashi hankali, bisa la’akarin da kasantuwarsa mutum, kuma ya bashi nafsu mai Magana da karfi na fushi da sha’awa bisa la’akari da janibin dabbantakarsa, lallai a ilimin mandik anyi ta’arifinsa da cewa shi dabbace mai Magana duk da cewa anyi ta’arifinsa a irfani da rayayye mai jin radadi.

Kebantaccen jauhari da yake cikin mutum wanda ake ta’arifinsa cikin isdilahin addinai a matsayin ruhi. Sannan akai ta’arifinsa a falsafa da nafsul nadika, wacce take mallakar karfin idrakil kulli. Ita tana daga tabbatattun abubuwa, da kuma idrakat na juzu’iyya wanda su suna iya canjawa, mutum yana iya kaiwa ga nafsul insaniyya ba ta hanyar tsanukan waje ba, sai dai cewa ta biyu samun yana kasancewa ta hanyar tsanukan da kayan aiki na waje da karfin jiki.      

Cikin wannan siyaki wasu ba'arin malaman falsafa suke cewa: ita nafsu tana iya riskar kulliyat da zatinta sannan tana riskar juzu'iyat da kayan aikinta. Sannan shi mutum yana da janibin bukatuwa da tsirrai daga karfinsa na cimaka da girmau da haifau  janibin da yayi tarayya da sauran dabbobi, sakamakon kasantuwarsa jiki mai girma mai motsi da iradarsa, hakama yana tattare da janibinsa na mutum kamar misalin riskar kulliyat da juzu'iyat , shi jiki ne mai girma yana motsi da irada kuma mai magana, sai ya zamanto ya tattaro janibin bukatuwarsa da tsirrai sakamakon cimakau da girmau da kuma dabbantaka da `yan Adamtaka, kai hatta madawwamiyar rayuwa.

 (أحياء عند ربهم يرزقون)

Su rayayyu ne suna azurtuwa daga ubangijinsu.

Rayuwar ubangiji tana tajalli cikinsa kamar yanda sunayensa da siffofinsa girmansa ya girmama suke tajalli cikinsa, daga nan mutum ya zamanto rayayye mai imani da Allah, rayuwar Allah kadai dai shi ne iliminsa da kudurarsa, lallai shi masanin komai ne kuma mai iko ne kan komai ne, sannan dukkanin wanda ya kasance kwatankwacinsa to ya kasance rayayye cikin zatinsa da siffarsa da ayyukansa.

Sannan asalan tsirrai karfi guda uku ne: cimakau girmau haifau, ita cimakau tana da abubuwa guda hudu da ta kebantu da su: jawau turau kamau nikau, sannan haifau tana da karfi guda biyu: samau rarrabau, abin da ake nufi da na farko shi ne tana sanya yankunan abinci su zamanto masu ikon karbar surar kwayar halitta, sannan ta biyu tana sanya su masu iko kan karbar wata surar daban.

Amma janibin rayuwar dabbanci, lallai ita tana tarayya da mutum cikin karfi goma sannanu, daga cikinsu akwai na zahiri, sune ganau jiyau kamsau dandanau tabau, biyar daga cikinsu kuma na badini sune: na farko shi ne hissi mushtarak wanda ake kira da (bindasiyya) wanda yake riskar surori na zahiri domin ya dauko ya kaisu zuwa mataskatar hiyali da karfi na hiyali, hiyali wanda yake taskace surori da gadinsu shi ne mataskatar hissi mushtarak , sai kuma karfi na wahami wanda yake kiyaye hissi na juzu'i, sai na biyar wato karfi mai tasarrufi wanda yake tattara dukkanin ababen da aka riska aka taskace su, sannan ya sadarsu da sashensu tare da sashe domin fitar da hukunci daga gare su, idan tushen hukunci ya kasance daga wahami, sai a kira shi da hiyali, idan kuma ya kasance daga karfi na hankali sai a kira shi da tunani,

Gudummawar tunani cikin rayuwar mutum:

Sannan ka sani shi hankaltar mafhumai kulli da riskar tabbatattun abubuwa wanda yake tajalli cikin nafsul nadik, kadai dai yana samuwa ne daga hanyar datacaccen tunani da ingantaccen ra'ayi, sannan shi datacaccen tunani yana kasantuwa cikin ilimi mai amfani, shi ilimi bai kasantuwa sai da da samuwar lafiyayyen hankali, bawai cikin sauki ake keta hijaban wahami da suke hana gano tabbatattun abubuwa da gasgatattun ilimummuka da fannoni masu kyawu ba, sai da hankali da ilimi da ma'arifa, lallai karfi na wahamai suma suna riskar abubuwa na zahiri da wanda bana zahiri ba, wadanda suka kasance cikin na zahiri, hukunci juzu'i na gangarowa daga gare su, sai dai cewa kawai wani lokaci a mukamin dauki ba dadi da fafatawa da hankali sai ka samu ya yi galaba kansa ya zauna kan karagar ilimi ya karbe ragamar tafiyar da lamurra a hannunsa, sai ya rattaba kufaifayin ilimi kan hukuncinsa, sai ya dinga sawwalawa da kayatar da karya da rigar gaskiya, wannan duka na daga sawwale-sawwalen nafsu cikin mutum, shi wahami yana amfanarwa cikin dabbobi domin tseratar da akuya daga farmaki da harin Kura, amma cikin mutum yana cutar da shi musammam ma lokacin jidalinsa da dauki ba dadi tare da hankali da abubuwa na hankali, sakamakon su wahamai gangar jiki ne na samuwa, suna daga karfi na badini cikin mutum kamar yanda bayani ya gabata, idan suka karbi ragamar mulki sai su kasance sun mamaye ko ina sun hana hankali sakat da taka rawa, shi wahami bai imani da hankali ba, bai sallama mishi ba, bai mika wuya ga hukuncinsa ta ko ina, kai hatta a ba'arin muhallai wahami kan kasancewa shugaba hatta tare da samuwar jahilci da wauta da gabunta, daga cikin abin da yake gajiyar da hankali da yin galaba kan hukunce-hukuncensa, kamar misalin mutum da yake tsoran kwana tare da gawa ciki daki daya, adaidai lokacin da yana da yakini da hankalinsa cewa gawa bata cutarwa ba kuma ta amfanarwa, gawar bata bakin komai sai da daskararren abu daga sauran daskararrun abubuwa kamar misalin bangon da yake kishingide jikinsa ko kuma misalin tabarmar da yake zaune kanta, sai dai cewa tare da hakan yana jin tsoro sakamakon ya ajiye aiki da hankali ya mika wuya ga wahami.

Misalin wannan shi ne abin da muke gani cewa kowa da kowa ya sancewa shi mutum matalauci ne  cikin zatinsa, bai da amfanawar ballantana cutarwa, bai da karfi babu dabara sai da da Allah madaukaki, sai dai cewa sakamakon wahami sai muke neman biyan bukatarmu daga gare shi, ko kuma mu sanya shi a mahallin ubangijintaka da Allantaka sakamakon wahaminmu mu fitar shi daga haddinsa na mutum da dabba, hakan kuskure ne matukar bai kasance shingagge da shingen Allah ba da iliminsa daga ubangiji mai hikima ba.

Wahami wani lokacin kan sanya mutum cikin fursun dinsa a daddaure da sasarinsa shi ne abin da ake kira da Shaidan mai tsaurin kai, kadai dai zaka iya saninsa daga kufaifayinsa da waswasinsa da sawwale-sawwalensa.

Wazifofin da suka hau kan hankali:

Daga cikin wazifofin hankali shi ne ma'abocin hankali ya ciratu daga riskarsa ga juzu'an abubuwa na zahiri ya zuwa mafhumai kulli, daga nan ne zai fara kaiwa ga kamsasar kamshim hakika, kamar misalin wanda yake hango kyalkyalin haske daga nesa, Kamar misalin dambar farawa da hattamawa da karshe, shi ilimi shi ne jarin hankali.

Sannan ka sani tsakanin nukdodi biyu daga bangarori biyu wato farawa da hattamawa shi ne samun ma'arifa, hanya daya rak wanda kuma itace tsani shi ne kaiwa ga ma'arifa, lallai ita ma'arifa ita ce misalin karfaffar igiya da zata sadar tsakanin mai ilimi da ilimi da abin da ake son a sani, babu banbanci cikin kasantuwa a nukdar farawa ne ko hattamawa, duk sa'ailin da muka taka gaba zuwa ga abin da muke son sani a dunkule shima sai ya karo gaban kadan gare mu a dunkule, lallai zamu kara cika da ma'arifa da shi, mu san shi cikin kebantattunsa da juzu'ansa, to hakama idan muka nesantu daga nukda ma'arifarmu sai ta karantu iliminmu ya zama kamar misalin digo ne kan littafi ko kamar digon ruwa cikin kogi, daga cikin abubuwa da suke banbanta ilimi da ma'arifa shi ne cewa shi ilimi shi ne riskar kulliyat shi kuma ma'arifa riskar juzu'iyat.

Nukda daya ce kawai ta yawaitu ne sakamakon jahiltar da jahilai sukai kanta da neman sanin su da tambayoyinsu kan hakikaninta da mahiyarta da abubuwan da suka kasantar da ita da juzu'anta

Tura tambaya