lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 21 RABIU AWWAL SHEKARA 1441 H TA’ARIFIN IJTIHADI A LUGGANCE DA ISDILAHI

Wuri: Qum Mukaddasa cibiyar Jabalu Amil Islami tareda- Smahatus Assayid Adil-Alawi

Lokaci: karfe 9 na safiya.

Cigaba kan abinda ya gabata cikin ta’rifin Ijtihadi a luggance da isdilahi, lallai bayan tsinkaya kan ma’anarsa ta lugga a jumlace maganarmu zata kasance cikin bayanin ma’anarsa ta isdilahi a wurin masana fihku wato Fakihai da abinda ya zo cikin harsunan riwayoyi da zantukan malamai daga bangaren Sunna da Shi’a, a zamani fakuwar nassi kamar yanda yake wurin Ahlus-sunna bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) sun bijira zuwa ga tsamo hukunci wato ijtihadin Sahabbai ko kuma abinda ake kira da kishiyar nassi a zamanin A’imma tsarkaka da lokacin fakuwar Hujjatul Ibn Hassan (a.s) a farko-farkon Gaibatul Kubra da tafiya kan ijtihadi.

Gabanin shiga cikin ta’arifin ijtihadi a isdilahance babu laifi mu yi ishara ya zuwa ga wani mai muhimmanci kamar yanda manyan malamai suka yi ishara shi ne: maudu’in kufaifayin shari’a cikin dalilai, kamar misalin halascin yin fatawa cikin mukamin bada fatawa kamar Mujtahidi ko kuma zartar da hukunci a mukamin yanke hukunci kamar misalin Alkali ba shi ne unwanin mujtahidi ba bari dai abinda ya zo cikin dalilai kuma kufaifayi suka rattabu kansa shi ne Malami ko Fakihi masanin hukunce-hukunce da dai makamancin haka, sai yafi dacewa bisa biyayya ga nassoshi da suka cikin wannan mukami na ta’arifin (Fakahatu da Fakihi) a wannnan lokaci bisa la’akari da rattabuwar kufaifayin hukunce-hukunce a kansa da kanta koma bayan koma bayan unwanin Mujtahidi da ijtihadi.

Wasu sunce: sakamakon kasancewa hadafi kowa da kowa abu ne guda daya kuma kamar yanda da sannu za a san cewa ijtihadi ko fakihanci shi ne tsamo hukuncin shari’a daga dalilanta na filla-filla ko kuma ace mayar da furu’a ya zuwa asali da makamancin haka daga ta’arifi da aka ambata a mukamin sai ijtihadi ya kasamce yana da ma’ana guda daya da fakihanci (fakahatu).

Kadai dai daya daga abubuwa biyu ya janye daga gareta:

Na farko: hakika sanin hukunce-hukuncen shari’a na rassan fikihu tsayayyu ne dagatattu ne-kamar yanda bayani zai zo-da farko dai sun dogara kan samuwar zurfaffar malaka cikin rai da ta hanyar ta Fakihi zai samu damar tsamo hukunci ko kuma mayar da rassa zuwa ga asali.

Na biyu: sun dogara kan motsa wannan malaka wacce ita wata kudura ce tareda duba zuwa ga dalilan fikhu  kamar misalin hujjantakar kabar da zahirin kur’ani, babu kokwanto Kalmar ijtihadi  tareda ma’anarta ta lugga da ta isdilahin fikhu tana shiryarwa zuwa ga wadannan abubuwa guda biyu.

Bayani: ance akasarin riwayoyin sun shiryar zuwa ga la’akari da ijtihadi cikin wanda zai kasance Alkali ma’ana dole ya kasance mujtahidi domin alkalanci ya halasta a gareshi hukuncinsa ya kasance zartacce dogaro da riwayar Makbulatu Umar Ibn Hanzalatu- bayaninta ya gabata cikin mabahisul ta’adul wal tarajihu_ cikin fadinsa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:  

وذلك في قوله× : (ينظر إلى من كان منكم ممّن قد روى حديثنا، ونظر في حلالنا وحرامنا، وعرف أحكامنا، فيرضوا به حكماً).

A cikinku ya duba wanda ya rawaito hadisanmu yayi duba cikin halalinmu da haramin dinmu, ya kuma san hukunce-hukuncenmu sai ya yarda da shi matsayin Alkali.

Imam tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi yayi la’akari da abubuwa uku cikin Alkali karkashin jumloli uku: 1- (wanda ya kasance ya rawaici hadisanmu daga cikinku) sai dai cewa wannan baya wadatarwa cikin riko da alkalancinsa cikin raba husuma da warware koke-koke.

2- (wanda yayi duba cikin halalinmu da haramin dinmu) abinda ake nufi da duba bawai shi ne kallo na idanu ba, kadai dai ana nufin kallo na sanya basira da tsamo hukunci.

3- sanin hukunce-hukunce kamar yanda (a.s) ya fada: (ya san hukunce-hukuncenmu) shi kuma sani da daban ilimi daban, kadai dai mafi kebantuwa daga gareshi shi ne ilmul bil kulliyat da sanin juzu’iyyat kamar yanda ya ke ilmu bil kiyasi a Falsafa haka zalika ilmu bil juzi’iyyat da falafa bil kulliyat.

Wadannan unwanoni da al’amura uku basu kasance masu kusanci ma’ana daya ba, bari dai yafi kebantuwa daga na farko kamar yanda hakan yake a bayyane, hakika alkali da cikinsa za ai la’akari da rwaitar hadisi a wannan lokaci tsuran riwaya ba zata wadatar ba cikin fifitarsa daga ba’amme domin shima ba’ame yana rawaito riwaya, galibin wadanda suka rawaito riwaya basu kasance daga Fakihai ba (na wane daga wadanda suke dauke da fikhu amma kuma ba su kasance Fakihai ba, na wane daga wanda ya dauko fikhu zuwa ga wanda ya fishi sanin fikhu) 1

Sai ya zamanto cikin Alkali kari kan nakalto riwaya dole ne ya kasance masanin halal da haram abinda ake nufi daga haka shi ne lura da zurfafa tuna da tadabburi cikin halal da haram wannan duba da zurafafa tunani ya doru kan karfi da iko da kudura da zai samu damar assasa Asalai.

Zamu cigaba da yardar Allah.


 

Tura tambaya