lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Taskar Adduoi 3


Da sunan Allah me rahama me jin kai

Yan uwa masu bibiyna salamun alaikum

Muna farin cikin sake kawo muku wannan rubu don nemna biyan bukatun ku adduoi kasha na uku.

Yana da kyau mutum in zai yi addua ya kasance yayi shi da ikhlasi da kuma salatin annabi da istigfari kuma ake sanya ‘yan uwa, Allah yana gaggawan amsa adduar da mukeyi wa ‘yan uwan mu muminai.

A wannan rubutu muna dauke ne da addua don magance matsololi da tsanani

1. Don samin daman biyan bashi da kuma kubuta daga gidan yari da kuma matsalolin rayuwa irin su bakin ciki da damuwa. Zaa iya karanta wannan ayar da aka fi sani da zikirin annabi yunus

 (لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ * فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْغَمِّ وَكَذَلِكَ نُنجِي الْمُؤْمِنِينَ)

2. An rawai to daga imam Rida (as) cewa zaa iya karanta wannan aya sau 442

(لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنتُ مِنَ الظَّالِمِينَ * فَاسْتَجَبْنَا لَهُ وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْغَمِّ وَكَذَلِكَ نُنجِي الْمُؤْمِنِينَ)

Don biyan bashi.

3. Idan aka rubuta Bismillahirrah manirrahim  a kwano me tsarki da ruwan wardi da kuma zaafaran sannan aka wanke, duk wanda ya sha zai sami Karin fahimta, haka kuma idan aka rubuta shi kafa 19 a farar takarda mara rubutu akaba wa mace me matsalar haihuwa, ya kasance tare da ita da izinin Allah zaa sami biyan bukata, haka zalika idan aka daura wannan takarda akan bishiyar da bata ‘ya’ya, da ikon Allah zai bada ‘ya’ya.

Tura tambaya