lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Malamai magada Annabawa_ kashi na 3 tarihin Shaik Abbas Qummi


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Shine Shaik Abbas bn Muhammad bn Abu KAsim Qummi, an haife shi a shekara 1294 hijra Qamariya a birnin Qum mai tsarki ta yand aya taso cikin ta, ya fara karatun fikihu a birnin Qum tun yana karamin yaro, a shekara ta 1316 ya tafi birnin Najaful Ashraf domin cigaba da yin karatun Hauza a wannan lokacin yafi maida hankali kan karatun hadisi hakan ne ma ya sanya shi ya lazimci bibiyar Allama Muhaddis Shaik Husaini Nuri Dabarasi, sannan ya dawo birnin Qum a dan wani takaitaccen lokaci a shekara ta 1331 hijri Shaik Qummi ya nufi birnin Mashad ya zauna kusa da hubbaren Imam Rida (As) Shaik Abbbas Qummi ya sadaukar da dukkanin kokarin sa cikin fagage da dama musammam ma fagen koyarwa lamarin da yakai ga adadin dalibansa sun kai daruruwa koma ace dubunnai a wannan zama da yayi a mashada na tsahon shekaru goma sha biyu, daga baya sai ya amsa kiran malaman Qum don yaje can ya bada tasa gudummawar cikin gida Hauza ilimiyya da kuma koyarwa cikin ta.

Shaik Abbas Qummi ya shahara da zuhudu da tsantseni da kyawawan dabi’u da yawan ibada da tsananin kaunar ilimi hadisi, an rawaito cewa yayin da wasu ba’ari suka zarge shi kan shagaltuwa da tattara hadisai maimakon shagaltuwa da wallafa fikihu da sauran fagaen sa, sai ya basu amsa da lallai shi zai sadaukar da ladan abinda ya wallafa zuwa ga Fatima Zahara (as) da haka ne wadannan litattfai nasa za su samu wanzuwa, kamar yanda ya kasance tsananin tawali’unsa ya lullube shi ya kasance baya zama gaban majalisi, bayan ya karkare tailfin Mafatihul Jinan ya kara wallafa wasu adadin litattafan daban daga cikin su akwai littafin Manazilul Akira, da Safinatul Bihar, da Madinatul Hikam, da Sa’arul Muntahal Amal fi Tarikul Nabiyi, da Wa’al Nafsul Mahmum fi Musibatul Sayyidna Husaini Mazlum, da Fawa’idul Ridawiyya fi Tarajimul Ulama’ul Jafariya, da Baitul Ahzan fi Masa’ibul Sayyidatul Niswan, da Muktasarul Abwab fi Sunani Wal Adab, rayuwar Shaik Abbas Qummi ta hattama dawafin ta a birnin Najaful Ashraf ya bar duniya a shekara 1359 hijiri wanda yayi daidai da 1940 miladi cikin shekaru 65, an binne shi cikin Hubbaren Imam Ali (as) domin girmama shi (ks).

Da yawan musulmi masu bibiya suna ganin sirrinsa ya buya cikin iklasin da yake da shi da kin yarda da samuwar kansa da kauracewa neman wani abu daga daukakar duniya cikin ilimin da Allah ya bashi, koda kuwa wasu na ganin ya takaita to ga abinda shi yake fada da bakinsa: babana ya kasamce yana zuwa masallaci da yake kusa da gidan sa anan yake sallah ya saurari huduba ko lacca wacce ake yi bayan idar da sallah, ya kasance akwai wani tsoho yana karanta kissoshi daga littafin Manazilul Akira dana wallafa sai dai cewa bai san cewa wannan littafi ni na wallafa shi ba, ya kasance duk sanda ya dawo gida sai yace mini ina ma ace zaka rubuta littafi misalin littafin wancan tsoho yake karantawa ka kasance misalinsa da yake zantar da mu yayin da naji haka daga gareshi na kusa in bayyana masa cewa nawa ne, sai dai a cikin zuciya nace bai da wani muhimmanci ya san cewa ni na wallafa, abu mafi muhimmanci shine Allah ya karbi wannan aiki daga gareni, sai nayi shiru naki cewa komai, duk sanda ya maimaita mini wannan Magana sai in roke shi da ya sanya ni cikin addu’ar sa da Allah yda datar da ni da irin siffofin sa da dabi’unsa.

Ya kasance yana himmatuwa kan rubutu da talifi da tarjama, mutane da daman gaske sun nakalto wannan himmatuwa da yake da ita, babban dansa cikin ta’alikin mahaifinsa kan rubuta yana cewa: lokacin da nake karamin yaro na kasance ina ganin mahaifin ya shagaltu da rubutu tun daga asubahi har zuwa yammaci ba tareda wani abu ya sanya shi ya ajiye ba, hatta lokacin da muka kasance cikin halin safara tafiye-tafiye zuwa wajen gari, ya kasance yana damuwa da lamarin abokansa da himmatuwar da ba za a iya siffanta ta ba, ya kasance yayin da yake musu rakiya cikin tafiye-tafiye ya na himmatuwa da su matukar himmatuwa yana kuma girmama su yana yi musu mu’amala da mafi kyawun mu’amala, ya kasance mutum mai gudun duniya da nesanatr kayace-kayacen cikin ta Masu gushewa, an nakalti kissoshi masu tarin yawa kan zuhudun sa, zamu kawo daya daga ciki matsayin samfuri, a wani lokaci wasu mata guda biyu daga birnin Mumbai na kasar Indiya sun zo wurin sa, sun bayyana masu bukatar su ta bashi albashin wata wanda ya kai Rubai 75 daga kudin kasar Indiya, sai yaki karba, sai daya daga cikin `ya`yan ya nuna bai yarda da abinda yayi ba, cikin fushi sai ya bashi amsa yana mai cewa: yi min shiru, kudaden da na kashe a baya har yanzu bai san yaya zan yiwa Allah bayanin su, hakama wurin Imamul Hujja (Af) saboda haka naki yarda in karbi wannan kudade don gudun kada in kai kaina da daukar nauyi.

Shaik Abbas ya kasance yana yin tawali’u ga kowa da kowa musammam ma malamai, ya kasance yana zantar da su hadisan Ahlil-Baiti (as) yana kuma ta’ammuli da su da kyawawan dabi’um A’imma (as) dabi’ar sa ta kasance yana zauna a gefan majalisi.

Hudubobin sa da kalaman sa suna da tasiri cikin zukatan masu sauraran sa, saboda yayin da yake kiran mutane ya zuwa lazimat daya daga cikin ibadoji  ko kuma kyawawan halaye daga halayen A’imma (as) to zaka same shi shine kan gaba cikin riko da su, ya kasance yana sanya wannan aya mai girma gaban gidonsa:  

كَبُرَ مَقْتًا عِندَ اللهِ أَن تَقُولُوا مَا لاَ تَفْعَلُونَ

Ya girmama kasancewa fushi ace kun kasance kuna fadin abinda bakwa aikata.

 

Ya kasance yana mai riko da ibadojin nafila, kamar nafiloli kowacce rana da karatun kur’ani d addu’o’i da suka zo daga A’imma (as) hakama raya dare da ibada da yin sallar dare, babban `dansa yana cewa: bana iya tunawa cewa akwai wani dare da ya Makara daga tashi yin ibada hatta cikin halin safara.

Daga cikin maganganun malamai kansa: ya zo cikin Ma’ariful Rijal: Ayatullahi Shaik Abbas Qummi ya kasance masani mai aiki da ilimin sa Adali Sika, Shaik Muhammad Hirzul dini yana cewa: shi Shaik Abbas Qummi ya kasance mai dandake ilimi mai yawan bahasi da bincike a zamanin sa amintacce mai tarbiya zahidi mai yawan ibada, kuma ma’abocin talife-talife masu fa’idantarwa.

Ya zo cikin littafin Raihanatul Adab: yana daga cikin mafifitan zamanin mu, ya kuma kasance masani mai daraja.

Shaik Muhammad Ali Tabrizi Kiyabani yana cewa: ya kasance mutum kamili masanin hadisi mai dandakewa kwararre.

1ـ قال الشيخ محمّد حرز الدين& في معارف الرجال: «كان آية الله الشيخ عباس القمّي عالماً عاملاً، وثقة عدلاً متتبعاً، وبحّاثة عصره، أميناً مهذّباً زاهداً عابداً، صاحب المؤلّفات المفيدة».

2ـ قال الشيخ محمّد علي التبريزي الخياباني& في ريحانة الأدب: «من أفاضل علماء عصرنا الحاضر، كان عالماً فاضلاً كاملاً محدّثاً متتبّعاً ماهراً».

 

Tura tambaya