lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Tuba da tubabbu kan hasken kur’ani da sunna

Tuba hakikaninsa bayani ne kan ma’anar da ke tsaruwa cikin abubuwa guda uku. Na farko shine ilimi, na biyu yanayi da hali. Na uku aiki. Na farko yana jawo na biyu, na biyu na jawo na uku na 

Abinda ake nufi da ilimi a nan shine sanin cutarwa da zunubai keyi, lallai su guba ne masu halakarwa da raba mutum da rayuwa ta madawwamiya. Masu katange bawanie daga ladabi. Sannan daga wannan ilimi ya samu wani yanayi da hali shine ya tashi ya yunkuram zuciyarsa ta yi radadi saboda subucewa abinda aka hijabance daga barinsa, lallai zuciya duk yadda takai da jin kunan rashin hijabantacce  da radadinsa wannan radadi zai bubbugar da wani yanayi daban ga zuciya, ana kiran wannan yanayi nufar masoyi zuwa ga rayuwa karshen rayuwa da nufin yin aiki domin masoyi yana ta’allaka da yanayin ne, da barin aikata zunnubin da ya kasance a da ya cudanyu da aikata shi, da azamtuwa da fuskanta barin zunubi da yake nesanta shi da masoyinsa, da wannan zai gyara abubuwan da suka subuce masa a baya idan sun kasance daga abubuwan da suke karba gyara, ya sanya ilimi kamar gabata ne da mukaddima. Sannan barin aikata zunubi kamar riba ce da kuma abinda zai biyo baya, sabaoda wannan annabi (s.a.w) yace: (nadama tuba ce) domin ita nadama bata wofinta daga ilimi da ya wajabta masa barin zunubi ya kuma bashi riba daga wata azama da yake bi da bibiya.  

 

قال العلامة في شرح التجرید: «التوبة هي النّدم علی المعصیة لکونها معصیة، والعزم علی ترک المعاودة في المستقبل، لأن ترک العزم یکشف عن نفي النّدم

Allama cikin sharhin littafin Attajrid yana cewa: (tuba shine nadama kan sabo sakamakon kasantuwarsa sabo, da yin azama kan barin komawa aikata shi a nan gaba, saboda barin azama na bayyana koruwar nadama da rashinta. 

Tura tambaya