lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Taskar Adduoi 1

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki uban gijin talikai, tsira da amincin Allah sutabbata ga manzon tsira (saww) da kuma iyalan gidan sa tsarkaka musamman imamin wannan zamanin wato imam Mahdi (Allah ya gaggauta bayyanar sa)

Ga dukkan yan uwa da ke bibiyan mu a shafuffukan mu na yanan gizo, ga wani hadiya na addua me matukan faida, wanda wannan addua ya taimaka min sosai a cikin rayuwana, na sami wannan addu'ar ne agun malamaina kuma wanna adduar yazo cikin wani littafi mai suna Zubdatul Asrar fil ulumi Alghariba, Ko dayake baa sami daman buga wanna littafin ba sabida yan wasu dalilai.

 littafin ya qunshi adduoi da ke da tasiri kan abubuwa da ban daban kamar su biyan bukatu da magance matsololi: irin su Karin Arziki, kara kaifin kwakwalwa, tsari daga abokan gaba da duk wani abu na sharri da kuma tsari daga waswasan shaidan.

Wannan Addua da na kawo way an uwa shine

 Duk wanda yake da wani bukatu zai iya yin nafila raka abiyu da niyyar neman biyan bukatu, acikin ko wacce  raka’a za akaranta bismillah sau 19 (بسم الله الرحمن الرحيم) bayan haka sai akarata suratul fatiha sau 19 sannan sai akaranta Qul’ huwa kafa daya, bayan an idar da sallar sai a yi salitin Annabi kafa 10, sannan sai a karanta Bismiallah (بسم الله الرحمن الرحيم) kafa 786 sai asake salatin annabi kafa 130 bayan haka sai akaranta wannan addua kamar haka.

بسم الله الرحمن الرحيم اللهم إني أسئلك بأسمك الرحمن الرحيم الذي لا إله إلّا هو الحي القيوم لا تأخذه سنة ولا نوم الذي ملأت عظمته السموات والأرض، وأسئلك بإسمك بسم الله الرحمن الرحيم الذي لا إله إلّا هو خشعت له الأبصار ووجلت له القلوب من خشيته أن تصلّي على محمد وآله أن تعطيني حاجتي

Bayan angama wannan adduar sai a roki biyan bukatu, da ikon Allah zaa sami nasara.

Muna baran Adduar ku Yan uwa 

Tura tambaya