lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

rayuwa bayan mutuwa

 

Rayuwa bayan mutuwa

Hakika mas'alar lahira da rayuwa bayan mutuwa tana daga cikin mas'aloli masu wahalar gaske ta yanda ya kai ga hankula da ma'abo zuzzurfan tunani sun dimauta cikin sha'aninta fiye da dimautarsu cikin mas'alar mafarar duniya, hakika ra'ayin inkari da kore samuwar karshen duniya bai takaitu kadai cikin mulhidai ba da masu inkarin mafarar duniya, bari dai hakika wani sashe daga masu imani kansantuwar duniya tana da farko da kuma masu imani da mahaliccin halittu ya kasance suna da shakku dangane da batun lahira da rayuwa bayan mutuwa basu karbi wannan tunani ba, wannan inkari kari kan abinda yake sabbabawa daga rashin warwarar mas'alar makoma kiyama, akwai wata nukuda daban shine cewa bai kasantu ba tare da wani dalili ba, saboda haka imani da samuwar lahira da ranar sakamakoyana wajabtawa mutum daukar masl'uliya da taklifi ta yanda hakan zai hana shi wasa da wargi da aikata zalunci ya kuma sanya shi karkashin dokoki, saboda haka sai suka fake da inkarin ranar sakamako domin samun damar yin zalunci da wasa da wargi.

Gabanin tsunduma cikin bahasi kan ranar asalin sakamako da rawar da take takawa mai matukar tasiri cikin tarbiyantar da mutum da tsarkake ruhinsa ya zama tilas mu nemi sanin sirrin kafewar annabawa dangane larurar imani da samuwar ranar lahira cikin kishiyantar inkarin masu inkarinta.

Yayin da kur'ani mai girma yake nakalto ishkalolin masu inkarin ranar lahira yake kuma warware su yana cewa ba shubuhar ilimi ta hana su imani da lahira ba, bari dai abinda yafi shahara kin son dabaibantuwa da kuma son aikata fajirci ne ya sanya su. 

أيحسب الإنسان ألن نجمع عظامه، بلى قادرين على أن نسوّي بنانه، بل يريد الإنسان ليفجر أمامه.‏ القيامة (3- 5).

Mutum yana tsammanin ba zmau iya tattara kasusuwansa ba, bari dai muna da ikon daidaita yatsunsa, bari mutum dai kawain yana son yin fajirci ne.

Banbanci tsakanin shubuhar ilimi da sha'awa ta aiki da sannu zamu yi bayaninsa a fasali na biyu a ciki zamu kawo shubuhohin masu zurfafa tunani kan ranar lahira

إن الذين يضلون عن سبيل الله لهم عذاب شديد بما نسوا يوم الحساب‏. ص (39).

Hakika wadanda suke kaucewa daga barin tafarkin Allah suna da azaba mai tsanani sakamakon abinda suka manta dangane da ranar hisabi.

Idan ya zamanto babu samuwar ranar hisabi babu ranar sakayya daga lada da ukuba kan kowanne irin aiki to zai zamanto babu abinda ya rage sai karkacewa daga barin hanyar Allah a kuma fada cikin wahala da tsiyata.

«إن الجنة حفّت بالمكاره، وإن النار حفّت بالشهوات» نهج البلاغة، خطبة 175.

Hakika aljanna ta kewaya da abubuwa marasa dadi, ita kuma wuta kewaye da sha'awe-sha'awe.

Sannan shi imani da ranar lahira yana lamincewa mutum falaloli, kur'ani na ganin tunawa da lahira da halarto ta cikin kwakwalwa yana zama tsanin daukaka ga ruhi da tsarkakuwar imani, dangane da masu tsarkakar niyya yana cewa:

إنَّا أخلصناهم بخالصة ذكرى الدار. (ص 46)

Lallai mun kebance su da watan tsarkakakka shine tunawa da lahira.

Kan asasin wannan himmatuwa cikin mai kishiyantuwa cikin falaloli da kishiyarsu muna samun manzon Allah (s.a.w) yana ranstuwa kan cewa lallai lahira gaskiya ce, kari kan yankakkun dalilai, haka kuma masu inkarin ranar kiyama wadanda suke imani da farantuwar halittu sai dai cewa tareda haka basu imani da ubangiji, gabanin rarraunar shubuha suna rantsuwa cewa lahira tsagwaronta karya ce kawai

وقال الذين كفروا لا تأتينا الساعة، قل بلى وربي‏. سبأ (3).

Wadanda suka kafirce suna fadin babu wata kiyama da zata zo mana, kace na'am ina rantsuwa da ubangijina

Haka cikin suratu Yunus an ambaci ma'anar wannan ayar a aya ta 53 haka cikin suratu tagabun aya 7

وأقسموا بالله جهد أيمانهم لا يبعث الله من يموت ....

Sun rantse da Allah bakin iya rantsuwarsu Allah ba zai tashi wanda ya mutu ba.

Wannan matsaya mai kishiyantar juna tana bayyana saboda imani da lahira yana tilasta kiyaye dokoki da takawa daidai lokacin da inkarinsa yana haifar da fasadi da fajirci.

Nukudar da bai kamata ace mun gafala daga gareta ba shine cewa ranstuwar annabi (s.a.w) ba daidai take da sauran rantsuwar mutane ba, saboda tana kasancewa a galibi mayin dalili da hujja, mai da'awa ya kanyi rantsuwa idan ya zama babu wani dalili gareshi, amma shi annabi (s.a.w) yayin da yake bayyana larurar imani da lahira bai takaituwa da kafa yankakkiyar shaida kan hakan bari dai yana karawa da rantsuwa kan wancan yankakken dalili, saboda ita rantsuwa da ubangiji na nufin rantsuwa mafarar duniya dalilin shiryuwar duniya, saboda lokacin da duniya take zama mai kammaluwa da kaiwa zuwa ga hadafi lallai idan ta zamanto ba tareda hadafi za ta kasance fanko kuma tauyayya, saboda abinda ubangijintaka take hukuntawa shine sadar da duniya zuwa ga kamala da kebantacciyar tarbiyya  

الله لا إله إلَّا هو ليجمعنّكم إلى يوم القيامة لا ريب فيه .... النساء (87).

Allah babu abin bautawa da gaskiya sai shi tabbas zai tattaroku zuwa ranar kiyama babu kokwanto cikinta.

Ma'ana ubangijintaka tana hukunta imani da lahira saboda lahira a hakika tana komawa zuwa ga mafara, saboda a hakika mafara itace makoma,

A takaice shine cewa imani da lahira yana taka rawa mai matukar tasiri cikin samar da nauyi da mas'uliya da takawa, saboda haka zamu tsallaka zuwa ga asalin bahasinmu ma'ana tabbatar da rayuwa bayan mutuwa.

Ya zo cikin kur'ani mai girma cikin madaukakiyar aya:

ونزلنا إليك الكتاب تبياناً لكل شي‏ء.

Mun saukar maka da littafi faiface bayani ga kowanne abu.

Hakika ya bayyana dukkanin ilimummukan mutum da dukkanin abinda zai bada gudummawa cikin lamintar da farin cikinsa, sai dai cewa sakamakon bayanin kan zuwa a dunkule lokacin ake bijiro da shi da dalili

يا أيها الناس قد جاءكم برهان من ربكم ...

Ya ku mutane hakika hujja daga ubangijinku ta zo muku…

Saboda haka zaka samu kur'ani yana bijiro da mas'alar ranar lahira makoma wacce babu wata kaya ko matsala da ke bijiro mata cikin bayanin yankakken dalili kanta, haka yana bayyana larurar samuwar lahira cikin inuwar sanin mutum, ma'ana yana bayanin duniyar da yake iya gani hakama duniyar dabi'a kamar yanda suke, to mutum haka kamar yanda aka halicce shi har ya wayin gari sananne abu ne laurar samuwar lahira da tabbatuwar ranar kiyama.

Duk da kasantuwar bahasi kan makomar duniya yana tattarowa da makomar sabowa su mutane yanki ne na wannan duniyar da ake gani sai dai cewa siffofinsu kebantattu tana wajabta bijiro da bahasi kan makomar mutum da bayani filla-filla.

Abinda ake bijiro yanzu shi asali ne na faruwar makoma bawai yanda take ba.

 

 


Tura tambaya