b Malamai magada Annabawa-tarihin mohd bn Ali bn Babawaihi Alqummi Shaik Saduk
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Malamai magada Annabawa-tarihin mohd bn Ali bn Babawaihi Alqummi Shaik Saduk

Shi ne Muhammad bn Aliyu bn Husaini Bn Musa bn Babawaihi Alqummi wanda aka sani da Shaikul Saduk, an haife shi a birnin Qum mai tsarki a shekara ta 306 hijra kamariya, ya taso karkashin kulawar mahaifinsa wanda ya kasance mafi ilimi da fahimta tsakanin tsaraikunsa a zamanin sa, ya yi karatu a hannun manyan shehunai, sannan ya taso cikin gidan ilimi, ya fa’idantu daga malaman birnin Qum tun yana karamin yaro, sannan ya bar birnin Qum a wani lokacin wanda tarihi bai bayyana shi ba, ya nufi garin Rayyu wanda shi ne garin da ya kasance babbar shelkwatar (capital) ta daular Buwaihiyyin a wannan zamani sai ya zauna a wannan gari, bayan wannan lokaci sai ya daura damarar barin garin a shekara ta 352 hijri ya nufi birnin Mashad a watan Rajab na wannan shekara.

A nan la’akari da SHaik Saduk matsayin babban jigo cikin malamai masana hadisi a shi’a imamiya rubuce-rubucen sa sun kai kusan littafi 200, daga cikin mafi muhimmancin su akwai littafin (Man la yahaduhuruhul Fakihu) wannan littafi yana daga cikin muhimman litattafan hadisai hudu da ake dogaro da su wurin shi’a, cikin wannan littafi ya zuba hadisai 5998, sannan yanada wasu litattafan daban kamar misalin littafin Amali da Ilalul shara’i da Ma’ani Akbaru da Tauhid  da Sawabul A’amal  da Kisal da Uyunu Akbarul Rida (as) da Kamaluld dini da dai sauran wasu litattafan, sannan yana wasu wallafe-wallafen da har yanzu ba a buga sub a suna nan a zaurukan nazari a Kasar Iran da wasu kasashen.

Daga cikin fitaccen fifikon da rubuce-rubucen sa suke da shi shi ne jingina ga hadisai cikin bayanin mafahim da tabbatar da kaziyoyin Ilimin tauhidi, shi a asasi fahimtar sa ta doru kan hadisi, ya kasance baya ganin halascin amfani da kiyasi, bari shi bai ganin halascin istinbadi da ciro hukunci, Shaik Saduk yayi tafiye-tafiye da yawan gaske cikin rayuwar sa domin neman ilimin hadisi, ya ji hadisi daga manya-manyan malamai masu tarin yawa, ya bar gurabe da kufaifayi masu tarin yawa cikin sa, lakabin da aki kiransa da shi ya kasance babbar aya kan gaskiyar sa da rikon amanar sa cikin nakalin riwaya da kiyaye ta, Ibn Idris Hulli shi ne mutum na farko da ya fara kiran sa da wannan lakabi, Shaik Dusi ya ambace shi da Imadun dini cikin isnadin littafin (Al’ibtibsar) bamu cikakken sani kan hakikar tarihin zamanin da aka haife shi da inda aka haife shi, iyakar abinda muka iya sani daga gareshi shi ne ya taso gidan ilimi a birnin Qum, sannan ya fa’idantu daga manyan malamai tun yana yaro sannan ya tafi Rayyu shelkwatar Buwaihawa a wannan lokaci ya kuma zauna cikinta, bayan haka ya daura damar barinta a shekara ta 352 hijri wacce tayi daidai da 967 miladiya ya nufi garin Mashad a watan Rajab na wannan shekara, Abu Abbas Najjashi cikin tarjamar sa ga mahaifin Saduk Aliyu bn Husain ibn Musa (rd) ya kawo cewa hakika shi ya zo ya tambaye shi masa’loli sannan ya bashi amsa ta hannun Aliyu bn Jafar, sannan ya hadu tare da Abu Kasim Husain ibn Ruhu Aswad ya tambaye shi da ya kai wasikar sa zuwa ga Sahibul Zaman (af) yana tambayar sa `da sai ya bashi amsa da cewa: lallai mun rokar maka Allah kan haka da sannu zaka azurtu da `ya`ya biyu mazaje masu alheri sai aka Haifa masa Abu Jafar da Abu Abdullah.

Shaik Dusi cikin littafin (Algaiba) ya rawaito daga Abu Abbas bn Nuhu daga Abu Abdullah Husaini bn Muhammad bn Suratu Alqummi yace: Aliyu bn Husain ibn Musa bn Babawaihi Alqummi ya zanatar da mu wata yar baffansa muhammad bn Musa bn Babawaihi ta kasance karkashin sa sai ya zama Allah bai azurta su da samun haihuwa basai ya rubuta wasika zuwa Shaik Abu Kasim Husain ibn Ruhu (rd) da ya roka masa sahibul Asri da Allah ya azurta shi da samun `ya`ya, sai amsa ta zo da cewa lallai ba zaka samu azurta da haihuwa daga gareta ba da sannu zaka mallaki wata baiwa daga Dailamiyya zaka azurtu daga gareta da `ya`ya biyu masana fikihu, Shaik Kudub dini Rwandi ya rawaito misalin haka cikin (Alkara’ij) hakama Dabarasi cikin (A’alamul wara) daga abin da ya gabata yana bayyana cewa Shaik Saduk an haife shi bayan wafatin Usmanul Amri ma’ana bayan shekara ta 305 hijri cikin farko-farkon jakadancin Husaini bn Ruhu ta yanda mahaifinsa ya je Irak a wannan lokaci ya hadu da Abu Kasim ya tambaye shi waus yan tambayoyi  sannan ya dawo Qum sannan ya kara aika masa da wasika ta hannun Aliyu bn Jafar bn Aswad kamar yanda ya zo cikin littafin Rijalul Najjashi, ka kuma ta hannun Abu Jafar Muhammad bn Ali Aswad kamar yanda aka rawaito daga babban malamin mu Saduk da kansa cikin littafin Kamalud dini , ya roke shi da ya kai masa wannan wasika zuwa ga Sahibul Zaman (Af) domin ya roka masa Allah da ya azurta shi da samun `da, kan wannan haihuwar sa zata kasance a shekara ta 306 hijri zamansa tare da mahaifin sa da kuma malamin sa Kulaini cikin gaiba sugra zai kasance shekaru ashirin da dan wani abu domin wafatin su ya kasance a shekara ta 329 wacce itace shekarar da Assamari ya bar duniya wanda shi ne jakada na karshe, ya kasance yana alfahari da haihuwar sa yana cewa an haife ni albarkacin addu’ar Sahibuz zaman (Af) haka yana cewa: Abu Jafar Muhammad ya kasance Shaik Saduk bn Aliyu Aswad (rd) sau da yawa ya na fadin idan ya ganni ina shige da fice zuwa ga majalisan babban malamin mu Muhammad bn Husain ibn Ahmad bn Walid (rd) kuma ina kwadayi cikin rubuta ilimi da haddace shi, sai yace babu mamaki ya kasance kana da wannan kwadayi cikin ilimi tunda dai kai an haifeka albarkacin addu’ar Imam zaman (Af).

Abu Abdullah bn Suratu ya kasance yana cewa: duk sa’ilin da Abu jafar da Abu Abdullah `ya`yan Aliyu bn Babawaihi suka rawaito wani abu sai kaga mutane suna ta mamaki daga haddar su suna ce musu: wannan sha’ani wata kususiya da ta kebance ku albarkacin addu’ar Imam yayi muku.

Shaik Saduk ya yi wafati a Rayyu a shekara ta 381 kabarin sa na nan kusa da kabarin Assayid Abdul Azim Hasani (rd) wurin ziyara ne da mutane ke zuwa suna neman tabarruki, sarki Fatahu Ali Shahi Kajari ya sabunta ginin sa a shekara ta 1238, Shaik Kuwansari ya kawo bayani filla-filla kan cikin Arraudat, haka babban malamin addini Abdullahil Mamakani ciki Attankihul Makal, da Alqummi cikin Alfawa’idul Ridawiyya.

 

Malaman sa:

1-mahaifin sa Aliyu bn Husaini bn Musa bn Babawaihi Alqumm ya bar duniya 329 hijri.

2-Shaik Muhammad bn Hassan bn Ahmad bn Walid.

3-Shaik Muhammad bn Musa bn Mutawakkil.

4-Shaik Ahmad bn Zayad bn Jafar Alhamdani.

5-Shaik Muhammad bn Ali Majilawaihi.

6-Shaik Muhammad bn Ibrahim bn Is’hak Addalikani.

7-Shaik Jafar bn Muhammad bn Masrur.

8-Shaik Husain ibn Ahmad bn Idris da sauran tarin malamai kusan 250 daga manyan marawaita daga garuruwa daban-daban.

 

Dalibansa:

Shaik Muhammad bn Muhammad bn Nu’umanu Al’ukbari Bagdadi Shaik Mufid wanda ya bar duniya a shekara 413

2- Alamul Huda Assayid Murtada wanda ya bar duniya a 436

3- mahaifin masanin Rijal Najjashi Aliyu bn Ahmad bn Abbas Alkufi.

4-`dan’uwan sa Abu Abdullah Husaini bn Ali bn Husaini bn Musa Babawaihi Alqummi.

5-muhammad bn Dalhatu Anna’ali Alkadib Bagdadi mawallafin tarihi.

6-Abu Ali Shaibani Qummi mawallafin tarihin Qum.  

 

 

Tura tambaya