b HUSUSIYAR SAKON MUSLUNCI
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

HUSUSIYAR SAKON MUSLUNCI

 

Sakon muslunci muhammadiya na mai asali ya fifitu da fifiko da hususiya bisa la'akari da Annabinsa madaukinsa zuwa ga mutane, mu `dan tsaya kadan kansa karkashin hasken ayoyin Kur'ani mai girma daga cikin mafi muhimmancin wanan fifiko da hususiya da yake da su:

 (يا أَيُّهَا الْمُزَّمِّلُ * قُمِ اللَّيْلَ إِلّا قَليلاً * نِصْفَهُ أَوِانْقُصْ مِنْهُ قَليلاً * أَوْزِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ الْقُرْآنَ تَرْتيلاً * إِنّا سَنُلْقي عَلَيْکَ قَوْلاً ثَقيلاً * إِنَّ ناشِئَةَ اللَّيْلِ هِيَ أَشَدُّ وَطْئاً وَأَقْوَمُ قيلاً * إِنَّ لَکَ فِي النَّهارِ سَبْحاً طَويلاً * وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّکَ وَتَبَتَّلْ إِلَيْهِ تَبْتيلاً * رَبُّ الْمَشْرِقِ وَالْمَغْرِبِ لا إِلهَ إِلّا هُوَ فَاتَّخِذْهُ وَكيلاً * وَاصْبِرْ عَلى ما يَقُولُونَ وَاهْجُرْهُمْ هَجْراً جَميلاً * وَذَرْني وَالْمُكَذِّبينَ أُولِي النَّعْمَةِ وَمَهِّلْهُمْ قَليلاً)[1] .

 Yakai wannan mau lullubi* ka tashi dare da sallah face kadan* rabinsa ko kuma ka rage kadan daga daren* ko ka kara kansa ka kyawunta karanta kur'ani kyawuntawa* lallai mu da sannu za jefo maka magana mai nauyi* lallai tashin dare shi ne mafi tsananin nutsuwa mafi daidaito ga magana* lallai cikin yini kana da tasbihi mai tsayi*ka ambaci sunan ubangijinka ka yanke kauna zuwa gare shi yankewa*shi ne ubangijin mahudar rana da mafadarta babu abin bautawa da gaskiya sais hi ka rike shi Wakili* ka yi hakuri kan abin da suke fada ka kaurace musu kauarcewa mai kyawu* ka barni da masu karyatawa ma'bota ni'ima ka dan jinkirta musu kadan.

Sai Allah yayi masa tanadi da yin ibada da tashin dare da karanta Kur'ani, da jefa masa magana mai nauyi, da dogon tasbihi da zikiri da yanke kauna, da tawakkali ga Allah da hakuri da kuma kyakkyawan kauracewa, wadannan suna daga jigon tanadi na ruhi zuciya da ruhi don daukar sakon muslunci mai girma wanda ya kasance sako ga baki dayan mutane har zuwa ranar lahira.

2-gamewa sakon sa zuwa ga mutane:

 (وَأَرْسَلْناکَ لِلنّاسِ رَسُولاً وَكَفى بِاللهِ شَهيداً)[2] .

 Hakika mun aiko Manzo ga mutane Allah shi ne ya isa zama shaida.

(يا أَيُّهَا النّاسُ قَدْ جاءَكُمُ الرَّسُولُ بِالْحَقِّ مِنْ رَبِّكُمْ )[3] .

 Yaku mutane hakika Manzo ya zo muku da gaskiya daga ubangijinku.

(إِنْ هُوَ إِلّا ذِكْرى لِلْعالَمينَ )[4] .

 Lallai tabbas shi Ambato ne ga Talikai.

(قُلْ يا أَيُّهَا النّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللهِ إِلَيْكُمْ جَميعاً)[5] .

 Ka ce yaku mutane lallai ni Manzon Allah ne zuwa gareku baki daya.

(الر كِتابٌ أَنْزَلْناهُ إِلَيْکَ لِتُخْرِجَ النّاسَ مِنَ الظُّلُماتِ إِلَى النُّورِ)[6] .

 Alif lamra littafi ne da muka saukar da shi gareka domin ka fitar da mutane daga duhu zuwa haske.

(هذا بَلاغٌ لِلنّاسِ وَلِيُنْذَرُوا بِهِ )[7] .

Wannan isar da sako ne zuwa ga mutane domin su gargadu da shi.

 

(وَما أَرْسَلْناکَ إِلّا كَافَّةً لِلنّاسِ بَشيراً وَنَذيراً)[8] .

Bamu aiko ba face ga dukkanin mutane kan Mai bushara da gargadi.

3-farawar wahayi da ilimi da karatu: 

 (اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّکَ الَّذي خَلَقَ * خَلَقَ الاْنْسانَ مِنْ عَلَقٍ * اقْرَأْ وَرَبُّکَ الاْكْرَمُ * الَّذüي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ * عَلَّمَ الانْسانَ ما لَمْ يَعْلَمْ

Ka karanta da sunan ubangijinka wanda ya yi halitta* ya halicci mutum daga gudan jini* ka karanta kuma ubangijinka shi ne mafi karamci*wanda ya sanar da mutum gameda Alkalami* ya sanar da mutum abin da bai sani ba.

4-hana shi motsa harshensa lokacin da ake saukar masa da wahayi:

 (وَلا تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِنْ قَبْلِ أَنْ يُقْضى إِلَيْکَ وَحْيُهُ وَقُلْ رَبِّ زِدْني عِلْماً)[10] .

 Kada kayi gaggawa da Kur'ani gabanin gama saukar wahayinsa gareka ka ce ya ubangiji ka kara mini ilimi.

(لا تُحَرِّکْ بِهِ لِسانَکَ لِتَعْجَلَ بِهِ * إِنَّ عَلَيْنا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ * فَإِذا قَرَأْناهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ * ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنا بَيانَهُ )[11] .

 Kada ka motsa harshenka don gaggawa da shi* lallai wajibi ne garemu tattarashi mu kuma tsara maka karatunsa.

5-bayyanar da da'awar muslunci da gargadin mutane:

 (يا أَيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ ما أُنْزِلَ إِلَيْکَ مِنْ رَبِّکَ وَإِنْ لَمْ تَفْعَلْ فَما بَلَّغْتَ رِسالَتَهُ وَاللهُ يَعْصِمُکَ مِنَ النّاسِ )[12] .

 Ya kai wannan Annabi ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka idan baka isar ba lallai baka isar da sakonsa ba Allah zai kareka daga mutane.

Wannan aya ta sauka ne kan wilaya Sarkin Muminai Ali (a.s) kan shugancinsa kan musulmai a ranar Gadir.

 (وَأَنْذِرْ بِهِ الَّذينَ يَخافُونَ أَنْ يُحْشَرُوا إِلى رَبِّهِمْ )[13] .

 Kayi gargadi da shi ga wadanda suke suke tsoran tsayawa gaban ubangijinsu

(كِتابٌ أُنْزِلَ إِلَيْکَ فَلا يَكُنْ في صَدْرِکَ حَرَجٌ مِنْهُ لِتُنْذِرَ بِهِ وَذِكْرى لِلْمُوْمِنينَ )[14] .

Shi littafi ne da aka saukar gareka kada wani kuntata ta kasance cikin kirjinka daga gare shi don gargadi da shi da tunatarwa ga Muminai 

(وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذيرُ الْمُبينُ )[15] .

Ka ce lallai ni mai gargadi ne mabayyani.

(وَأَنْذِرْ عَشرَتَکَ الاْقْرَبينَ )[16] .

 Ka gargadi danginka mafi kusanci da kai.

(فَاصْدَعْ بِما تُوْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكينَ * إِنّا كَفَيْناکَ الْمُسْتَهْزِئينَ )[17] .

 Kawai ka tunkari abin da aka umarceka da shi ka kau da kanka daga barin Mushrikai* lallai mun kareka daga masu maka izgilanci.

(يا أَيُّهَا الْمُدَّثِّرُ * قُمْ فَأَنْذِرْ * وَرَبَّکَ فَكَبِّرْ * وَثِيابَکَ فَطَهِّرْ * وَالرُّجْزَ فَاهْجُرْ * وَلا تَمْنُنْ تَسْتَكْثِرُ * وَلِرَبِّکَ فَاصْبِرْ)[18] .

Ya kai wanda ya lulluba da mayafi* tashi kayi gargadi* kuma ubangijinka ka girmama shi* ka tsarkake tufafinka* ka kauracewa gumaka*kada kayi kyauta kana mai neman kari, kayi hakuri domin ubangijinka.

6- ya kasance mai tsananin kwadayi kan shiryar da mutane: 

 (إِنْ تَحْرِصْ عَلى هُداهُمْ فَإِنَّ اللهَ لا يَهْدي مَنْ يُضِلُّ )[19] .

Idan kayi kwadayi kan shiriyarsu lallai Allah baya shiryar da wanda yake batarwa 

(فَلَعَلَّکَ باخِعٌ نَفْسَکَ عَلى آثارِهِمْ إِنْ لَمْ يُوْمِنُوا بِهذَا الْحَديثِ أَسَفاً)[20] .

Me yiwuwa kana halaka kanka kan kufaifayinsu idan basu imani da wannan zance sabida ban takaici. 

(لَعَلَّکَ باخِعٌ نَفْسَکَ أَلّا يَكُونُوا مُوْمِنينَ * إِنْ نَشَأْ نُنَزِّلْ عَلَيْهِمْ مِنَ السَّماءِ آيَةً فَظَلَّتْ أَعْناقُهُمْ لَها خاضِعينَ )[21] .

Me yiwuwa kana halaka kanka saboda sun ki zama Muminai*idan muka ga dama zama saukar musu da aya daga samaN wuyayen su zasu rankwafa mata 

(إِنَّکَ لا تَهْدي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلكِنَّ اللهَ يَهْدي مَنْ يَشاءُ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدينَ )[22] .

Lallai kai ba zaka shiryar da wanda kake so ba sai dai cewa Allah yana shiryar da wanda ya so shi ne masanin shiryayyu. 

(أَفَمَنْ زُيِّنَ لَهُ سُوءُ عَمَلِهِ فَرَآهُ حَسَناً فَإِنَّ اللهَ يُضِلُّ مَنْ يَشاءُ وَيَهْدي مَنْ يَشاءُ فَلا تَذْهَبْ نَفْسُکَ عَلَيْهِمْ حَسَراتٍ إِنَّ اللهَ عَليمٌ بِما يَصْنَعُونَ )[23] .

 Yanzu wanda aka kayata masa miyagun ayyukansa sai ya dauke kyawawa lallai Allah yana batar da wanda yaso yana kuma shiryar da wanda ya so kada ka halaka kanka don bakin ciki kansu lallai Allah masanin abin da suke aikatawa ne.

(وَما أَكْثَرُ النّاسِ وَلَوْ حَرَصْتَ بِمُوْمِنينَ )[24] .

 yawancin mutane ba Muminai ko da kuwa kana kwadayin su kasance Muminai

(اسْتَغْفِرْ لَهُمْ أَوْ لا تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ إِنْ تَسْتَغْفِرْ لَهُمْ سَبْعينَ مَرَّةً فَلَنْ يَغْفِرَ اللهُ لَهُمْ ذلِکَ بِأَنَّهُمْ كَفَرُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ وَاللهُ لا يَهْدِي الْقَوْمَ الْفاسِقينَ )[25]

Ka nema musu gafara ko baka nema musu ba ko da zaka nema musu gafara sau saba'in Allah ba zai taba gafarta musu ba sakamakon lallai su sun kafircewa Allah da Manzonsa Allah baya shiryar da mutanen da suke Fasikai.

7-ya kasance mai bushara da gargadi: 

(وَبَشِّرِ الَّذينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصّالِحاتِ )[26] .

 Kayi bushara ga wadanda sukai imani suka aikata ayyukan kwarai.

(إِنّا أَرْسَلْناکَ بِالْحَقِّ بَشيراً وَنَذيراً)[27] .

 Lallai mun aiko ka da gaskiya mai bushara da gargadi.

(أَكانَ لِلنّاسِ عَجَباً أَنْ أَوْ حَيْنا إِلى رَجُلٍ مِنْهُمْ أَنْ أَنْذِرِ النّاسَ وَبَشِّرِ الَّذينَ آمَنُوا أَنَّ لَهُمْ قَدَمَ صِدْقٍ عِنْدَ رَبِّهِمْ )[28] .

Shin mutane suna mamaki ne mun yi wahayi zuwa ga wani mutum daga cikin su ka gargadi mutane kayi bushara ga wadanda suka yi imani da cewa lallai fa suna da abin gabatarwar gaskiya a wurin ubangijinsu. 

(يا أَهْلَ الْكِتابِ قَدْ جاءَكُمْ رَسُولُنا يُبَيِّنُ لَكُمْ عَلى فَتْرَةٍ مِنَ الرُّسُلِ أَنْ تَقُولُوا ما جاءَنا مِنْ بَشيرٍ وَلا نَذيرٍ فَقَدْ جاءَكُمْ بَشيرٌ وَنَذيرٌ وَاللهُ عَلى كُلِّ شَيْءٍ قَديرٌ)[29] .

 Ya ma'abota littafi hakika Manzonmu ya zo muku yana bayyana muku kan lokaci fatara daga Manzanni domin kada kuce wani mai bushara da gargadi mu bai zo mana to hakika mai bushara da gargadi ya zo muku Allah mai iko ne kan komai.

(وَما أَرْسَلْناکَ إِلّا مُبَشِّراً وَنَذيراً)[30] .

 Bamu aiko k aba face don ka kasance mai bushara da gargadi.

(لِتُنْذِرَ أُمَّ الْقُرى وَمَنْ حَوْلَها)[31] .

 Domin ka gargadi mutanen Makka da wanda suke kewaye da Makka

(يا أَيُّهَا النَّبِيُّ إِنّا أَرْسَلْناکَ شاهِداً وَمُبَشِّراً وَنَذيراً * وَداعِياً إِلَى اللهِ بِإِذْنِهِ وَسِراجاً مُنيراً * وَبَشِّرِ الْمُوْمِنيüنَ بِأَنَّ لَهُمْ مِنَ اللهِ فَضْلاً كَبيراً)[32] .

 Yaki wannan Annabi hakika mun aikoka shaida mai bushara da gargadi* mai kira zuwa ga Allah da izininsa fitila mai haskakawa* kayi bushara ga Muminai da cewa wurin Allah suna da falala mai girma.

(فَإِنَّما يَسَّرْناهُ بِلِسانِکَ لِتُبَشِّرَ بِهِ الْمُتَّقينَ وَتُنْذِرَ بِهِ قَوْماً لُدًّا)[33] .

 Kadai mun saukake shi da harshenka domin ka yiwa masuTak'wa bushara da shim ka kuma gargadi mutane wasu tsananin jayayya.

راجع : البقره : 155، آل عمران : 21، النساء: 138، الانعام : 19 و 51 و92، الاعراف : 184 و188، التوبة : 3 و34 و112، هود: 2، الرعد: 12، الحجر: 89، الاسراء: 105، الكهف : 2 ـ 4، الحج : 49 ـ 51، الفرقان : 56، القصص : 46، سبأ: 28، فاطر: 24، يس : 11 و69 ـ 70، الزمر: 17، الشورى  : 27، الاحقاف : 9، الفتح : 8، الذاريات : 50 ـ 51، الملک : 26، المدثر: 1 ـ 2.


Tura tambaya