sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » Malamai sune magada Annabawa
- » MALAMAI KAN TAFARKIN HUSAINI
- » DAGA ZANTUKAN IMAM MUHAMMAM BAKIR A.S
- » Ku tashi tsaye domin Allah
- » Kada ku riki wannan kur'ani abin kauracewa
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » falsafar humanism (mutumtaka) ka'ida ce ta mazhabar Almaniyanci
- Tarihi » Al'ummar Jahiliya gabanin aiko da Annabtar cikamaki
- Fikhu » KARIJUL FIKHU – BAHASI KAN DAGATAWA DA TSAYAWA KAN GABOBIN AYOYI
- » GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU
- » sakafa da sakafantacce a mahangar muslunci
- » IMAM HASSAN ASKARI DA TALAKAWA
- » Nasihar mahaifi ga dansa
- » ALLAH YANA GANI NA A KOWANNE WAJE
- Fikhu » BAHASUL KARIJUL FIKHU 19 RABIUS SANI 1441 H, JERANTAWA TSAKANIN FATIHA DA SURA DA TSAKANKANIN KALMOMINSU DA HARUFFANSU 47
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
bara in kara kan haka lallai ilimin Akhlak yana fuskantar da mutum zuwa ga hanyar da Allah ya tsara masa wacce ita ce halitta da ya halicce shi kai wato son kamala da fuskantar ubangijin iyayen giji.
Ina ne matsugunin Akhlak cikin sakon muslunci? Mene ne hanyoyin tsaftace zuciya wadanda da binsu mutum zai samu farin cikin gidaje biyu duniya da lahira, mane ne zai zama iliman Akhlak da zai fa'idantar da mutum a wannan fage, wadannan dukkaninsu maudu'ai da babban malaminmu ustaz sayyid Adil-Alawi (h) zai bamu darasinsu a hauza ckin wannan ganawar tamau tare da shi
Ku dabi'antu da dabi'un Allah
Tambaya: mun san cewa lallai shi Akhlak shi ne adaon mumini, wacce alaka ce tsakanin Akhlak da muslunci karkashin inuwar ayoyin kur'ani mai girma da madaukakan hadisai?
Amsa: Allah madaukakin sarki yana cewa:
(قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَا*وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَا)(الشمس: 9 ـ 10).
Tabbas ya rabauta wanda ya tsarkaketa* kuma hakika wanda ya taketa ya tabe.
Lallai Akhlak na daga taskokin muslunci sannan magana kan Akhlak kamar magana ce kan kur'ani da hadisi, wanda Allah matsarkaki ya saukar don shiriya ga mutane:
(إِنَّ هَذَا الْقُرْآنَ يَهْدِي لِلَّتِي هِيَ أَقْوَمُ وَيُبَشِّرُ الْمُؤْمِنِينَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ الصَّالِحَاتِ أَنَّ لَهُمْ أَجْراً كَبِيرا) (الإسراء: 9).
Lallai wannan kur'ani yana shiryarwa zuwa ga wacce take mafi daidaituwa yana kuma bushara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka nagargaru da cewa lallai suna lada mai girma.
وقد بُعث رسول الله ليتمّم مكارم الأخلاق «إنّما بُعثت لأتمّم مكارم الأخلاق ومحاسنها» (1).
Tabbas an aiko manzon Allah (s.a.w) domin cika kyawawan dabi'u* kadai dai an aiko ni don in cika kyawawan dabi'u.
Wannan na nuni da cewa manzon Allah (s.a.w) yana bayyana mana kur'ani mai girma wanda shi ne littafin Akhlak din rayuwa da farin ciki da muslunci cikin dukkanin hukunce-hukuncensa yana mai da hankali ne kan Akhlak, alal misali sallah wacce take amudi jigon addini wacce tana hani da aikata alfasha da munkari-wannan bai ishara zuwa ga komai illa Akhlak, sannan manzo mafi karamci Allah ya yabe shi cikin kur'ani da fadinsa:
(وَإِنَّكَ لَعَلى خُلُقٍ عَظِيمٍ) (القلم: 4).
Lallai kai kana kan dabi'a mai girma.
الإمام الصادق×: «تخلقوا بأخلاق الله» (3).
an karbo hadisi daga imam sadik (as) ya ce: ku dabi'antu da dabi'un Allah.
Duniya farin cikin mumini:
Tambaya: Cikin inuwar rayuwar zahiri ta mada cikin duniya shin akwai wata rawa da ma'anawiyt da al'amuran ruhi ke takawa cikin rayuwa mutum? Mece ce wannan rawa da suke takawa?
Amsa: hakika mu munyi imani cikin addinin muslunci da cewa duniya tana damfare da lahira hakama lahira tana damfare da duniya (gidan dabi'a) wanda cikinsa akwai madiyat sannan wadannan madiyat suna kishiyantar ma'anawiyat da al'amuran lahira, saboda shi lafazin sunan duniya a larabci tamatan (adna) ne wanda Allah ya sanya gona wurin shuka kasuwa ga waliyyai, lallai ita duniya share fage ce ga tsallakawa lahira, daga cikin mutane akwai wanda yake shuka ciki ya girbi abin da ya shuka ya tsallaka zuwa ga mukamin (kaba kausaini) ko kuma mai kusa daga gare shi daga wilaya da kusantar Allah ya wayi waliyin Allah.
Sannan shi kusantar Allah na nufin narkewa da yin fana'I cikin iradar Allah, sai mutum bai son komai face sai don Allah yana sonsa ya kuma nufe shi, da wannan `dan tsokaci ne muke imani da cewa lallai ita duniya wurin shuka ce don girba a lahira, sannan duniya mumini da mumina ita ce lahirarsu saboda ita ce guzurinsu a lahira.
(خَيْرَ الزَّادِ التَّقْوَى) (البقرة: 197).
Mafificin guzuri guzurin tsoran Allah.
Saboda haka ma'anawiyat suna yin tasiri cikin madiyat idan ta kasance da wannan mahangar, da ma'anar mu kalli mada a matsayin tsanin da zamu taka yakai ga abin da muke buri hadafin da muka nufa.
(وَأَنَّ إِلَى رَبِّكَ الْمُنْتَهَى) (النجم: 42) و(اِلَى اللهِ تَصِيرُ الأمُورُ)(الشورى: 53) و(إِنَّا للهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ) (البقرة: 156).
lallai makoma zuwa ga ubangijinka take. Suratu najamu. Lallai mu daga Allah muke gre shi kuma zamu koma.
Tambaya: yanzu Akaramallah kana nufin mada ita tsani ce ba ita ce hadafin dake son cimma ba?
Amsa: na'am a wannan lokaci ya kamata mada ta kasance tsani da za a taka akai zuwa ga Allah, sai dai cewa daga cikin sharrin mada shi ne tana sanya mantawa da lahira, musammam ma ace ansamu nafsul ammara bissu'i (nafsu mai umarni da mummuna) wacce bayanta akwai shaidan, sai dai cewa yayinda ma'anawiyyat sukai tasiri cikin madiyat wannan duniya ta wayi gari daga azurtar mumini, to dukkanin abin da yake cikinta sai ya wayi gari a wajen mumini tsani hadafi wurnsa shi ne Allah kadai, saboda ta zama cikin tafarkin Allah fisabilillah.
Amma idan mutum ya zamanto yana kallon duniya bai kallon lahira, baya yin tunani cikin ma'anawiyyat bai yin tunani cikin neman kusancin Allah to wannan duniya ta zama hatsari gare shi wacce take halaka mutum ta kai ga shiga jahannama makoma ta munana, Allah yana fushi da irin wannan uniya wacce take yanke mutum daga lahirarsa, amma idan iadan cikin akwai rinin Allah da ma'anawiyya, lallai mumini zai zama akiknsa cikinta ya shagaltu da sallah kowanne lokaci, ma'ana dai dukkanin abin da yake aikatawa hatta lokacin da yake karkasa awanninsa zuwa kashi hudu kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja lallai shi zai kasance cikin `da'a da ibada.
Takawa cikin gujewa bin son zuciya:
Tambaya: lallai wani lokacin mukan ganin takawa tare da wasu yanayi tana iya haifar da natija mai kyau ko akasin haka, mece ce takawa yaya kuma za a sameta?
Amsa: Kalmar takawa a harshen larabci daga wikaya (kare kai) ta samo asali sannan a ilimin Akhlak tana nufin yin taka tsantsan cikin hanya da take akwai kaya cikinta. Wannan kiyayewa da taka tsantsan shi ake kira da takawa, shi mumini yana yin taka tsantsan daga kayar zunubi da sabo daga abin da ya bayyana da wanda ya buya, duk wanda ya kasance haka to shi ne muttaki mai takawa, a wata Kalmar kuma anyi bayanin takawa cikin madaukakin hadisi da cewa ita ce:
«أن لا يراك الله حيث نهاك ولا يفقدك حيث أمرك» (5).
Kada Allah ganka wurin da ya haneka kada kuma ya rasa inda ya umarceka.
A wani hadisin kuma:
«اتّقوا الله في الخلوات فإنّ الشاهد هو الحاكم» (6).
Kuji tsoran Allah cikin kadaita da halwa domin mai ganinku shi ne ubangiji.
Sau da yawa loakcin da mutum ya kadaita da kansa musammam ma samari matasa sukan afkawa zunubi da sabo, da hujja cewa babu wanda yake ganinsu sai cikin sauri a afkawa zunubi, sai dai cewa idan ya san cewa Allah yana gani yana ji yana kuma ya san cewa Allah zai hukunta shi ranar kiyama to wannan lokaci zai ji tsoran Allah.
(وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى*فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى)(النازعات: 40).
Amma duk wanda ya ji tsoran tsayuwa gaban ubangijinsa ya hana ransa abin da take so* lallai aljanna ita ce masaukarsa.
Duk wanda ya kasance mai tsora Allah, sannan ya zama akwai dangantaka mai kafi tsakaninsu, malaman Akhlak suna cewa (lallai mutum na shiga aljanna da taku biyu takun farko shi ne ya ji tsoran Allah na biyu kuma ya hanawa zuciya abin da take so cikin sabawarta da magi giramn jahadi
Duk wanda ya kasance mai tsoran Allah da sannu zai rayu cikin kwanciyar hankali da nutsuwa
{أَلاَ بِذِكْرِ اللهِ تَطْمَئِنُّ الْقُلُوبُ} (الرعد: 28).
Ku saurara da ambaton Allah zukata ke samun nutsuwa.
Na'am ya zo cikin hadisi mai daraja daga imam sadik (as)
«التقوى ثلاث: تقوى العام وتقوى الخاص وتقوى خاص الخاص» (7).
Takawa guda uku ce: takawa gama gari, takawa kebantatta, takawa kebatanciyar kebantatta.
Takawa gama gari: shi ne ka sauke wajibai kabar aikata haram wannan ga mutane gama gari tun daga balagarsu, namiji yana balaga lokacin da yakai shekaru 15, mace na balaga a shekara 9, zai kasance mai takawa da wannan daraja, ma'ana zai aikata ayyukan wajibi zai bar ayyukan haram. Amma martaba ta biyu ta takawa kebantacciya- tokari kan aikin wajibai lallai shi yana rungumar ayyukan mustahabbi yana kuma bbarin zakkema shubuha Karin kan kauracewa ayyukan haramun, amma martaba ta uku wato takawa kebantacciyar kebantatta to cikin mutum hatta halal yakan bari, hakika ya zo daga imam Hassan (as) «الدنيا في حلالها حساب وفي حرامها عقاب وفي الشبهات عتاب» (8)
Ita duniya cikin halaliyar akwai hisabi cikin haramun dinta kuwa akwai ukuba sannan cikin shubauha akwai zargi.
Lallai shi yana barin halal don gudun hisabi sannan yana kauracewa shubuha don gudun zargi, yana kuma kauracewa haram gudun azaba da ukuba, ya zo cikin madaukakin hadisi cewa (mafifin aiki shi ne mafi wahalarsa) sannan lallai babu shakka cikin tasirn muhallin da mutum ke rayuwa cikin rayuwar mutum, hakika an rawaito cewa
«أن كلّ إنسان يولد على الفطرة،وأبواه إما يهوّدانه أو ينصّرانه أو يمجسانه»(10)،
Lallai kowanne mutum ana haifarsa kan halitta (tauhidi) sai dai iyayensa su maida bayahude ko banasare ko bamajuse.
Muhalli idan ya kasance muhallin mara kyau gurbatacce wanda ya wofinta daga kyawawan halaye, muhallin aikata zunubi da sabo sannan mutum ma'abocin takawa ya ta so cikin irin wannan muhalli gurbatacce ya yaki barna da imaninsa, to lallai shi ya fifici wancan ma'abocin takawa da ya taso cikin muhallin imani wanda ya taimaka masa cikin karuwar takawa, muhimmi shi ne mutum ya ji toran Allah da zuciyarsa sannan cikin kowanne lokaci ya dinga tuna cewa Allah yana ganinsa a kowanne yanayi, sai dai cewa ya zamu habbaka takawa cikin zuciya? Lallai ana cewa muslunci da Akhlak kamar misali carbi ne lokacin da ka riki guda daga cikinsa sai ka tsallaka ta kusa da ita har sai ka kai ga karshen carbin, saboda haka su hukunce-hukuncen muslunci kamar `yayan carbi ne ba zai yiwu mutum ya dauki daya bay a kyale ragowar dole ne ya rike su baki daya, ance wani mutum ya je wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya ce masa ya manzon Allah ka koya mini wani hukunci guda daya a cikin muslunci da za aiki da shi ba sai nayi ragowar ayyuka, sai manzon Allah (s.a.w) ya ce masa: kada kayi karya, a wannan lokacin wannan mutumin ya tafi sailokacin sallah yayi sai ya ce idan banyi ba sannan manzon Allah (s.a.w) ya tambayeni gameda ita da me zan bashi amsa? Shin zance ne bani sallah ba? Lallai fadin hakan nada wahala gare ni, ko kuma zance nayi sallah? Sai in zama makaryaci, a wannan lokaci sai ya tashi yayi sallah, sannan bayan haka sai azumi ya gangaro sannan gulma sannan fushi… haka dai da Kalmar kada kai karya sai yayi aiki da dukkanin hukunce-hukuncen muslunci, saboda dole ne ya kasance mai gaskiya cikin rayuwarsa.
Waliyyan Allah:
Tambaya: akaramakallahu mene ne hanyar tsaftace zuciya da kauracewa afkawa cikin aikata haramun?
Amsa: mafificiyar hanya zuwa ga Allah shi ne ka so shi shi ne ka nufi Allah, wannan ita ce hanya takaitaciya mafi kusancin hanyoyi, ita ce siradi mikakke wanda yake janyo wusuli cikin gaggawa, ya zo cikin madaukakin hadisi kudisi:
لو علمت من قلب عبدي المؤمن أنّه يريدني لفتحت عليه أبواب السماوات والأرض.
Da cikin zuciyar bawana mumini zan gano cewa ya nufe ni da lallai zan bude masa kofofin sammai da kasa.
Ance wannan ita ce mafi kusancin hanyoyi saduwa da Allah matsarkaki madaukaki kamar yadda yake cikin ilimin Akhlak da irfani.
Idan bawa ya so Allah lallai Allah zai so shi anan ne dangantakar soyayya zata kasantu, dangantakar mai nufi da abin nufi
(اللهُ وَلِيُّ الَّذِينَ آمَنُوا)(البقرة: 257) (والّذين آمنوا أولياء لله).
Allah ne masoyin wadanda sukai imani. Bakara 257. Kuma Wadanda sukai imani sune masoyan Allah.
Tambaya: mene ne ma'aunin rashin karkata zuwa ga duniya dangane da malami?
amsa: ma'aunin shi ne kada ya sake ya manta lahira kada kuma ya zakkewa aikata sabo saboda duniya, misali lokacin da wani mutum mai askakken gemu domin ya bada hakkokin shari'a ga wani malami sai wannan malami yaki umarni da kyakkyawa da hani da munkari don gudun kada ya fasa bashi wadannan kudaden hakkokin shari'a da gudun kada ya kaiwa wani daban to wannan malami shaidanin malami ne,
Tambaya: shin hawa ga malami ko mallaka gida yana iya zama karkata zuwa ga duniya gameda shi?
Amsa: bai daga zuhudu kin mallakar wani abu, sai dai cewa zuhudu shi ne kada abun duniya ya mallake ka, cikin wasu ba'arin lokuta ana iya ganin daukakar muslunci, kamar yadda muhakkik naraki mawallafin littafin (jami'ul sa'adat) ya nakalto lokacin da wani sufi daga cikin wadanda suke da'awar irfani, shi arifi yana yakar zuciyar mai umarni da mummuna daga cikinta sannan yana yakar makiya muslunci daga waje, muhakkik naraki lokacin da ya wallafa littafin jami'ul sa'adat daya daga muridansa ya karanta littafin sai ya burge shi ya yanke shawarar ziyartarsa lokacin da ya je wajensa ya kasance yana rayuwa a garin kashan cikin kasar iran sai ya ga gidan muhakkik naraki kataon gida cike da ni'ima ga hadimai ga mutum na shiga wasu na fita wasu na fita, sai wannan sufi yayi mamakin ganin haka ya dauki hakan cewa duniya ta rudar da mahakkik naraki sai ya je ya zauna wajen muhakkik naraki har sai da ya bari mutane suka fita, sannan ya bayyana takaicinsa daga abin da ya gani a gidansa musammam bayan ya karanta littafinsa na tsaftace zuciya mai suna jami'ul sa'adat, ya ce masa lallai kai baka aiki da abin da da iliminka abin da yafi dacewa shi ne ka fita daga garin kashan ka tafi sahara kayi watsi da duniya, sai naraki ya ce masa to tashi mu tafi tare, sanannen al'amari shi ne sufaye sunada wata `yar kwarya da basu barinta duk inda suka je, yayinda suka tafi suka fita sahara sai sufin nan ya waiwaya ya ce ya kamata mu koma, sai naraki ya tambaye shi me ya sanya hakan? Sai ya ce na manta `yar kwaryata a gidanka.
Sai naraki ya ce subhanallah ni na bar iyalina Ahalina da kuma bar gida da duk abin da na mallaka na fito tare da kai domin myi bautar Allah cikin sahara, amma kai yanzu baka iya barin `yar kwaryarka ga kowa, to idan ya zama haka to wane ne mai zuhudu wane ne kuma mai son duniya?
Ma'ana wannan kissa shi ne zuhudu ba shi ne kada ka mallaki abin duniya ba, kadai zuhudu shi ne kada abun duniya ya mallake ka.
Ka shiriya da shiriyarsu:
tambaya: Allah madaukakin sarki na cewa:
(لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللهَ وَالْيَوْمَ الآَخِرَ وَذَكَرَ اللهَ كَثِيراً) (الأحزاب: 21).
Hakika abin koyi kyakkyawa ya kasance gareku cikin manzon Allah ga wanda yake fatan Allah da ranar lahira ya kuma ambaci Allah da yawa.
akaramakallahu shin ta kaka abin koyi nagari zai yi tasiri cikin mutum sannan ta kaka za a zabe shi?
Amsa: al'amarin yana komawa ga tsarin halitta lafiyayya
(فِطْرَةَ اللهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا)(الروم: 30).
Halittar Allah da ya halicci mutane kai.
Mu cikin muslunci munyi imani da cewa kowa ana haifarsa tsarkakakke, Allah madaukaki ya sanya jijiyar halitta cikin nau'uka guda uku daga soyayya, son alheri, son kyawu, son kamala, sannan duk wani da aka haifa zaka samu yana son alheri ba sharri ba, sai muhallin rayuwa ya sanya shi ya aikata laifi ya karkace daga hanyar gaskiya, shi mutum da halittarsa yana son kamala da kyawu da alheri, shi yana son ya kammalu ya kasance maf alheri saboda haka nema ka sameshi yana neman wanda zai shiriya da shi, idan ya zama daga masu shiriya to zai nemi abin koyinsa daga makarantar annabawa da litattafan sama ta yadda madaukaki yake cewa (ku shiriya da shiriyarsu) da shiriyar annabawa da rayuwarsu da tsarin yadda suka rayu da dabi'unsu (abin koyi mai kyawu ya kasance gare ku daga manzon Allah) idan ka nufi koyi to abin koyinka ya kasance manzon Allah (s.a.w) mutum mafi girma mafi kamala idan kaso koyi to abi koyinka ya zama sarkin muminai (as) idan ka so koyi ka kuma ka zama mai hakuri to yi koyi da Hassan (as) idan ka so koyi cikin danne fushi to yi koyi da Musa Alkazim (as) hakaza imamanmu salihai magada annabawa sune ababen koyi, hakama idan ka samu malami tsarkakakke to ya kamaceka kayi koyi da shi.
Amma idan ya zama ya nesanta daga wannan fage da yanayi, to lallai shi zai nemi kamala daga nan da can wajen `yan was an kwallo wajen fasikai gafalallu, idan mutum ya san hakika ya san cewa wadannan gafalallu ba zasu kais hi ga abin da yake buri ba to wannan lokaci zai bincika wanda zaikusanta shi da Allah wanda shi ne abin koyi nagari a wannan lokaci zai sanya gaskiya da hakika (ka san gaskiya zaka san ma'abotanta)
ka tsarkake niyyarka zaka samu komai:
Tambaya: ibada wani tsani ne mai tasiri cikin tasftace zuciya, sai dai cewa wanne nau'in na ibada?
Amsa: ibada a luggance daga shi ne wanda ya wahala kan hanya ibadoji wahalar hanya don kaiwa ga kusantar Allah madaukaki, wadannan ibadu halastattu masu kai mu ga Allah sune ibada ta hakika bisa la'akari da cewa lallai shaidan ya cewa Allah matsarkaki:
(فَبِعِزَّتِكَ لأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ*إِلاَ عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ)(ص: 82).
Na ranste da buwayarka sai na halakar da su baki dayansu*face bayinka tsarkakakku daga cikinsu.
Da iklasi ake samun kubuta daga shaidan da zuciya mai umarni da mummuna da rudun duniya mayaudariya mai janyo kaucewa daga hanyar gaskiya, hakika hadisi ya zo daga sarkin muminai (as) cewa kalmomi biyu cikinsu akwai dukkanin ibada sune (kayi iklasi zaka samu) idan ka nufi samun dukkanin mukamai madaukaka to ka lazimci iklasi misalin Kalmar (ya Allah) idan ta ksance da tsarkin zuciya to zata kaika zuwa ga Allah matsakaki madaukaki, in kuma babu to koda ya tsaya dukkanin dare ya azumci dukkanin zamani amma sai ya zama bai tsarkake niyya ba to ibadarsa zata kasance hijabi kai ita ce mafi girman hijabi, idan ya zama haka to dole ne ibadar da da zata kaika zuwa ga Allah ta siffantu da tsarkin niyya.
(اِنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِنَ الْمُتَّقِينَ) (المائدة: 27).
Kadai dai Allah yana karba daga masu takawa.
Ibada tare da iklasi `dan kadan tafi alheri daga ibada mai tarin ba tare da iklasi ba, sabubba masu tasiri cikin takawa wani lokaci kan kasantuwa daga cikin gida kamar son Allah da tsoran azaba, wani lokacin kuma daga waje kamar samuwar iyaye nagargaru da abokai salihai daga ahalin sallah da jihadi, idan mutum ya nufi ya rayu cikin halin ma'anawiyya, to ya zama dole yayi abota ma'abocin halin ma'anawiyya lallai hakan zai yi tasiri a badininsa.
Hakika an rawaito daga imam sadik (as)
«قطيعة الجاهل تعدل صلة العاقل» (13).
Yanke alaka da jahili tana daidai da sada zumunci da mai hankali.
Imam yana cewa yanke alaka da jahili idan ka yanke masa to kai kamar kana tafiya da ma'abocin hankali ne.
An tambayi annabi isa (as) shin dawa za muyi mu'amala? Sai yace: da wanda ganinsa ke sanya ku tunawa da Allah, furucinsa ke kara muku ilimi, iliminsa yana kwadaitar daku cikin lahira
Tambaya: mecece nasiha wacce kuke ganin jarinta na amfanarwa ga masu suluki cikin hanyar tsarkake zuciya?
Amsa:
(قُلْ إِنَّمَا أَعِظُكُمْ بِوَاحِدَةٍ أَنْ تَقُومُوا للهِ مَثْنَى وَفُرَادَى) (سبأ: 46)، فكل حركاتنا وسكناتنا ينبغي أن تكون لله تعالى (الَّذِينَ قَالُوا رَبُّنَا اللهُ ثُمَّ اسْتَقَامُوا تَتَنَزَّلُ عَلَيْهِمُ الْمَلاَئِكَةُ أَلاَ تَخَافُوا وَلاَ تَحْزَنُوا) (فصّلت: 30).
Kace kadai ina muku wa'azi da kalma guda daya ku tashi don Allah bibiyu da daidaiku. Suratu saba'I aya 46
Dukkanin motsinmu da shirinmu ya kamata su kasance don Allah.
Wadanda suka ce Allah ne ubangijinmu sannan suka daidaita mala'iku suna sauka kansu kada ku tsorata kada kuyi bakin ciki.
Saboda haka ita nasiha da wa'azin kur'ani na Allah da annabi shi ne cewa suna kiranmu da lallai baki dayan ayyukanmu su kasance don Allah, kamar yadda sakin muminai (as) yace: ( tsarkake niyya zaka samu)
Daga karshe muna rokon Allah matsarakaki madaukaki da ya sanyamu tare da makaranta masu daraja daga cikin masu azurtuwa kuma mu kasance cikin kulawar sahibuz zamam daga cikin kebantattu tsarkakakkun sahabbnsa da mataimakansa masu shahada a gabansa amin amin.
*****
الهوامش:
(1) بحار الأنوار، العلّامة المجلسي، ج 58، ص 129.
(2) وسائل الشيعة، الحرّ العاملي، ج 4، ص 27.
(3) بحار الأنوار، م. س، ج 58، ص 129.
(4) محاسبة النفس، الشيخ إبراهيم الكفعمي، ص 181.
(5) نور البراهين، السيّد نعمة الله الجزائري، ج 1، ص 204.
(6) نهج البلاغة، خطب الإمام علي×، الشريف الرضي، ج 4، ص 77.
(7) جامع السعادات، مهدي النراقي، ج 2، ص 138.
(8) أعيان الشيعة، السيّد محسن الأمين، ج 1، ص 77.
(9) بحار الأنوار، م. س، ج 79، ص 229.
(10) كنز العمال، المتقي الهندي، ج 1، ص 261.
(11) بحار الأنوار، م. س، ج 40، ص 126.
(12) ميزان الحكمة، محمّد الريشهري، ج 1، ص 760.
(13) خصائص الأئمّة، الشريف الرضي، ص 137.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- kunya a musulinci
- Sai nayi na so abu kaza, sai muka so abu kaza niyya, sai ubangiji ya nufi abu kaza
- Kashe-kashen ma'arifa
- Malamai magada Annabawa-tarihin mohd bn Ali bn Babawaihi Alqummi Shaik Saduk
- TUFA barbeloli masu yawan gaske sun sauka kan wata qatuwar bishiya, sannan iskar ta kasance iskar kak
- Karanta, yi tunani, ka yi aiki, ka san makiyinka Shaidan
- Haqiqanin Ruhi
- YAYA ZAN RUBUTAWA YARA KISSA
- FIKHU 13 GA WATAN SAFAR 1441 WAJIBI MAZAJE SU BAYYANA KARATU CIKIN SALLARA ASUBAHI
- KARIJUL FIKHU 7 GA RABIU AWWAL SHEKARA 1441, KAN MUSTAHABBANCIN BAYYANARWA CIKIN AZUHUR DA LA’ASAR