lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MENE NE MUSABBABIN MATSALOLIN IYALI?


da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Tsira da aminci su kara tabbata ga mafificin halittu baki daya Muhammad da iyalansa tsarkaka

Hakika sabubabban da suke kawo matsaloli da cikas cikin raywaur zamantakewar iyali da farko-farko sun kasance cikin sinfi biyu, sinfi na farko sune sabubban madiya sannan daya sinfin kuma ya bubbugo daga abubuwa da suke ratayuwa da abin da yake boye daga dabi’a.

 

Na farko: fafutikar Shaidan da rawar d ayake takawa cikin ganin ya lalata shekar d ama’aurata suke rayuwa cikinta, wannan shi ne dalili da sababi na tushe da asasi, Shaidan dai da muka sani wanda ya kasance halitta ta farko da ya fara aikata babban laifi da ya zama sanadiyar sauko da Adamu daga aljanna, lallai Shaidan yana da tarihi cikin halakar da `dan Adam, lokacin da ya je wajen babanmu Adamu ya fitar da shi daga cikin aljanna yana mai yi masa da matarsa Hauwa’u cewa shi lallai yana niyyar yi musu nasiha ne, wannan dai Shaidani da ya yi nasara cikin hari na farko da ya fara kaiwa a rayuwarsa, yunkurin farko na cuna da halakarwa ya kasance tare da Adamu (as).

Ya zo a cikin ba’arin nassoshi cewa Shaidan ya kasance mai yiwa Mala’iku huduba gabanin halakars hi da nuna girman kai da yay, sannan kuma ibadarsa ta kasance ibada da samun kwatankwacin ta ke da wuya a tsahon tarihin duniya, lallai ya kasance daga mafio girman masu ibada, ya kasance idan ya sunkuya sujjada ya kan yi dubban shekaru kafin ya dago, shi ya kasance daga masu bautar na farko-farko, cikin takunsa na farko na shaidanci da jahannamanci ya samu dama ya farauce abin farautarsa wato babanmu Adamu da matarsa, ya barsu nan suna kuka wanda ya zama daga kukan cikin tarihi, domin bayan fitiwarsu daga aljanna sun ta rusa kuka ba kakkautawa, lallai Shaidan yana taka rawa cikin rayuwarmu ta yau da gobe, lallai yana sadada da kwarara cikin kamar yanda jini yake gudana cikin jijiyoyi, musammam ma sa’ilin da ya ga iyali suna cikin farin ciki da kwanciyar hankali da samun tabbatuwa, shi miji wata shi wata samuwa ce mai matukar tasiri cikin rayuwar jama’a, shi samuwa mai bada gudummawa, ko kuma ma’abocin addini ko matashi mai riko da addini, ko malamin Jami’a, kowanne mutum yana da gudummawar da yake bayarwa cikin addini da isar da sako, haka ita ma mata tana da ta ta gudummawa da take bayarwa cikin gina addini cikin na ta bangaren a cikin Hauza ilimiya ne ko kuma a fagen wayar da kan jama’a, ko kuma cikin Mu’assasa Tablig da yada labarai ko aiki.

Irin wannan iyali Iblis yana daukar halaka su matsayin kololuwar burinsa.

Wannan mutumi ko kuma malamin addini wanda wayar da jama’a yake hannunsa, wannan uwa ko kuma wannan mata wacce za ta iya taka rawa mai tasiri cikin ceton adadi mai yawa daga `yan mata da mata cikin jama’a, Shaidan yana cewa: maimakon ian bata lokaci na cikin halaka wannan da wancan bara in halaka jagorori wadanda suke dauke da nauyin shiriyar da baki dayan al’umma.

Saboda hakane muke ganin duk sanda mutum ya karu cikin Imani da kutsawa cikin fagen sakafa da neman ma’arifa sai kaga hare-haren Shaidan sun girmama kansa, hakan na faruw ata hanyar wurgo masa wasiwasinsa, da samar da shamakai da shinge!

Shi Shaidan bai da iko kan gabbai sai dai cewa yana sadadawa ya shiga zukata, su zukata sune muhimmai, zuciya itace sarauniya kan dukkanin sasannnin jiki, idna Shaidan ya samu dama ya shiga wannan masarauta to lallai zai zama Kenan ya cimma burinsa.

 

Na biyu: rashin tsinkaye kan hikima da falsafar samuwa da ta rayuwa: wannan yana daga cikin abnd ayake kawo sabani ko kuma rashin nasara cikin rayuwar ma’aurata, wasu ba’arin mutane sun sani ko basu sani ba sun yi ikirari ko basu yi su a wurinsu jin dadi da morewa na daga abu mafi muhimmanci a rayuwa a wurinsu, zaka samu suna karar da rayuwarsu- cikin hali daga halayen abin da suke da’awar sa da jin dadi a rayuwance, suna rayuwa ne kawai su ci cikin wannan daura mai kisa, cikin lafazin riwayoyi ya zo cewa (shi mumini shi ne wanda yake tanadin guzuri bawai mai sakin jiki ya ji dadi kawai ba).

 

Mutanen da su babu abin da suka iya fahimta a rayuwa in banda son jin dadi, lallai a dabi’ance zaka samu dukkanin alakokin su tare da wasunsu da muhalli da dabi’a da dukkanin sinadarn rayuwa suna kokarin mai da al’amari zuwa ga jin dadi kawai.

Mata zaka samu tana kallon mijinta mai dukiya  matsayin wanda zai bata kudi domin cimma burinta a rayuwance, shi miji zai dinga kallon mace a matsayin kayan jin dadinsa kawai bata da wata kima da ta wuce wannan, sa’ilin shekaru suka ja bayan aurensu kyawun da ni’imar matar suka tafi sai ka ga miji yana fara tunanin zamansa da wannan matar fa ya kamata ya zo karshe ta gama amfani gare shi, sai ya dinga kallonta mara amfani lokacin da shekarunta suka kai 45, bai da wani kallo da zai m,ata face na matsayin mai rainon yara kamar sauran masu raino da ake dauko su kodago daga wajen gida, hakan ya faru ne sakamakon yana kallonta matsayin abokiyar jin dadi bawai abokiyar rayuwa ba.

Haka al’amarin yake wajen ita ma kanta mace idan ta ga mijinta ya karye dukiyarsa ta kare haske da kyalkyalinsa duk sun kauce sannan ga tsufa ya barbada masa gishiri, a dabi’ance zaka samu tana neman kauracewa misalin wannan miji, daidai lokacin da ita falsafar rayuwa ta sabawa haka, bari dai ya zo daga Kur’ani mai girma:

(وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً)

Daga cikin ayoyinsa ya sanya daga kawukanku ya halittar muku matayen aure domin ku samu nutsuwa garesu ya kuma sanya kauna da rahama tsakaninku.

 

Shin ka san cewa sa’ilin da maid aura igiyar aure yake cewa: na aura wance ga wane shi fa wannan kulli kufensa yana mikewa har Abadan abiding? Idan namiji ya shiga aljanna sakamakon kyawun aikinsa, lallai zai nemi matarsa ya ce: ya ubangiji ian mata ta wacce mu ka kasance tareda juna a gidan duniya wacce ta kasance abokar tarayyar fatana da burina wacce ta tarbiyantar da `ya`yana? Sai ace masa: matarka tana dubun la’arafi bene daga benayen wutar jahimu, wannan bawan Allah mumini wanda aka bashi mukamin ceto-kamar yanda kuka sani shi ceto mafi girma na Annabi da iyalansa, sannan karamin ceto an baiwa muminai za su yi ceto- saboda haka sai wannan mumini ya ceci matarsa, sai ka ga wannan iyali da suka rabu suka watse a filin lahira sun kara samun dama sun hade sun game da juna a karo na biyu,

Kur’ani mai girma yana cewa:

 (وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ)؛

Wadanda suka yi Imani zuriyarsu ta bisu da Imani zamu riskar da zuriyarsu da su.

 

Ma’ana mata da zuriya za a riskar da su da miji, Manzon Allah (s.a.w) ya ce:

(ما من أهل بيت يدخل واحد منهم الجنة، إلا دخلوا أجمعين الجنة، قيل: وكيف ذلك؟ قال: يشفع فيهم، فيشفع حتى يبقى الخادم فيقول: يا رب، خويدمتي قد كانت تقيني الحر والقر، فيشفع فيها أيضا)

Babu wani Ahlin gida da dayansu zai shiga aljanna face dukkaninsu sun shiga, sai aka ce masa kaka haka zai faru? Sai ya ce: za a bashi damar yin ceto cikinsu sai yayi ceto har sai ya zama hadima ta rage, sai ya ce: ya ubangiji `dan hadimata ta kasance tana kareni daga zafin rana da sanyi, sai a bashi damar cetonta.

 

Idan mutum ya kasance cikin rayuwa madawwamiya baya gafala daga hadimarsa to kaka kuma daga matarsa? Saboda haka wannan alaka alaka ce tsarkakka, da aka nufi rayuwa madawwamiya d aita, saboda haka mata da miji abokan tarayyar juna ne duk sanda dayan cikinsu ya daukaka da wata daraka cikin Imani to zaka samu tae rayuwa da daukaka cikin aljanna madawwamiya.

Kan wannan ne zai zama babu wani shinge da Katanga daga ma’aurata cikin daren auganci su ce: ya ubangiji ka sanya ka sanya product dinmu cikin kamfani guda, sannan raba lahira ka bamu masauki tareda juna cikin aljanna, mu kamfani ne gud adaya, sai miji ya nemi Allah ta’ala ya sanya ladan dukkanin abin da ya aikata cikin hidimtawa mutane cikin daga guminsa cikin taska, hak zalika ita za ta nemi ubangiji ya ajiye mata ladanta na kula da mijinta , dukkanin ladan nasu ya kasance jimillar darajoji da ba a iya riskarsu cikin aljanna, miji wanda yake daukar nauyin maraya ribarsa zai samu mata tagari.

 

Na uku: gajiya da kosawa daga maimaicin abu guda daya kullum a rayuwa: wannan yana daga abin da yake kawo sabani cikin rayuwar aure, domin mutuim zai wayi gari ya kuma yini da shakali daya da yake ta maimaituwa safiya da yammaci, matsala cikin kowanne irin dadi na duniya abubuwa biyu ne

Ta farko: karewa, kowanne abu yana karkarewa zuwa ga gushewa, kowanne abu yana halaka face fuskar Allah mai karamci, Allah ta’ala ya ce:

 (كُلُّ شَيْءٍ هَالِكٌ إِلاَّ وَجْهَهُ)

Kowanne abu zai halaka face fuskarsa.

 

Matsala ta biyu: duk wani sabon abu yana dau kar hankali, duk wani kyawu wata rana za a wayi gari an saba da shi, abin da kadai zai sanya mutum yaji bai kosawa shi ne tsallakawa zuwa abin da ya buya daga dabi’a, shin ka taba samun wani Arifi kaji yana cewa na gaji na kosa daga sallah! Idan ya kasance ma’auni shi ne fizgar mada (physical gravity) wacce fizga ce cikin hajji? Wanne abu ne yake sanya wasu shaukin zuwa hajji babu yankewa har tsawon shekaru arba’in ko hamsin, ka samu mutum yana tattare karbo bashi daga wurin wannan da wancan domin ya ga ya samu damar zuwa hajji? da zamu waiwaya zuwa ga zakin da dadin rayuwa daga wannan sashe, da ba a ma samu wnai abu wai shi gajiya da kosawa ba har abada, akwai wata Magana mai dadi da kaywu daga cikin litattafan Irfani da Aklak da cikinta ake cewa (babu maimaici cikin tajalli) kamar yanda ilimin ubangiji bai da karshe kudurarsa bata karshe haka zalika kyawunsa da yake tajalli cikin bayi shima bai da karshe, daga nan Annabi mafi karamci (s.a.w) ya kasance yana dadada daga wannan kyawu, yana cewa:   

 (إن لي مع الله حالات، لا يحتملها ملك مقرب ولا نبي مرسل)،

Inada shiga wani hali da yanayiyyika tare da Allah da babu wani Mala’ika makusanci ko Annabi aikakke da zai iya daukarsa.

 

Wanne abu ne ya kasance yana yana gigita Sayyada Zahara (as) sa’ilin da take tsayuwa a wurin ibadarta, wannan tsayuwa da yake canjuwa ya zuwa shakalin haskaka? Hakika an kirata da Zahara sakamakon haskenta ya kasance yana haskakuwa a cikin duniyar samuwa, ta kai ga Ali (as) ya kasance daga surorin dbe hasonsa da jin dadinsa a rayuwance.

Hakika mace tsararriya ce ta fito daga gidan babanta da babarta bata wata tawayar gata da tausasawa da kauna, ta kasance tana rayuwa matabbbaciya mai kyawu, to wanne abu ne ya sanya ta fita daga kyakkyawan muhallinta tama iya yiwu wa ta kasance cikin muhallin mai cike da ni’ima da wadata daga halaliya, wannan baiwar Allah ta zo gidan miji domin ta kasance a hannun mijinta tsararriya da zabinta, bawai tilashi ba, ita ta zabi ta daure kanta da igiyar aurensa, lokacin da miji ya dauki matarsa matsayin amanar Allah a hannunsa, lallai zai kalleta matsayin fure mai kamsasawa, kamar yanda ya zo a hadisi  

(المرأة ريحانة وليست بقهرمانة)

Mace fure ce ba a bawai abokiyar kokawa bace.

 Ita mace kamar misalin kwalaba ce ita ko kwalaba ana ajiye ta ne a wurin ado a zuba fure cikinta mutum ya dinga kaffa-kaffa da ita don gudun kada wani abu ya hambareta musammam idna kwalabar an kayata ta da kayayyakin ado masu tsada daga duwatsu masu daraja daga Yakutu da Zubarjad.

Tura tambaya